Labarai

‘Yan sandan INTERPOL sun yi shelar neman ‘yan Nijeriya 14 ruwa a jallo

‘Yan sandan INTERPOL sun yi shelar neman ‘yan Nijeriya 14 ruwa a jallo

Daga USMAN KAROFI Ƙungiyar ‘Yan Sandan Ƙasa da Ƙasa (Interpol) ta ayyana wasu ‘yan Nijeriya 14 a matsayin waɗanda ake nema bisa zargin aikata laifuka daban-daban kamar fataucin mutane da miyagun ƙwayoyi, fashi da makami, yaudara, da jabun takardu. A wata sanarwa da ta fito daga Interpol, sun ce waɗannan mutane suna fuskantar tuhuma a ƙasashe daban-daban kan rawar da suka taka a wasu ayyukan laifi. Sunayen waɗanda ake nema sun haɗa da Felix Omoregie, wanda ake zargin shugabantar wata ƙungiyar laifi a Belgium, wadda ke amfani da ƙananan yara wajen karuwanci da Jessica Edosomwan, wadda ake zargin fataucin mutane…
Read More
Gwamna Abba ya halarci jana’izar mahaifiyar gwamnan Jigawa

Gwamna Abba ya halarci jana’izar mahaifiyar gwamnan Jigawa

Daga RABIU SANUSI a Jigawa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya halarci Sallar jana'izar mahaifiyyar gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar Namadi(Dan Moɗi) Gwamnan Kanon wanda ya samu rakiyar wasu daga cikin masu ruwa da tsaki zuwa ƙaramar hukumar Kafin Hausa dake Jihar Jigawa yayin rufe marigayiyar Hajiya Maryam Namadi Umar. Yayin halartar sallar jana'idar gwamnan yayi addu'ar samun rahama da kwanciyar kabari cikin lumana ga mahaifiyar gwamnan na Jigawa. 'Wannan babban rashin ba na gwamna Umar Namadi bane kaɗai, kafatanin al'ummar arewa ne da ƙasa baki ɗaya. Wakilin mu ya ruwaito cewa Hajiya Maryam Namadi ta rasu ne…
Read More

Badaƙalar Dala 35m: Kotu ta tusa ƙeyar daraktan matata zuwa Kurkukun Kuje

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Litinin ne Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta'annati, EFCC ta gurfanar da Darakta-Manaja na matatar Kamfanin 'International Refinery and Petrochemical Limited', Akindele Akintoye bisa zargin sa da hannu a badaƙalar Dala miliyan 35. A ranar 31 ga watan Oktoba, 2024 ne EFCC ta kama Mista Akintoye inda ta tsare a ofishinta dake Abuja. Mai Shari'a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ne yake hukunci game da shari'ar. Wani saƙo da EFCC ta wallafa a shafin X, ya ce ana zargin Akintoye ne da karɓar kuɗaɗen daga Hukumar Ci-gaban Ayyuka da…
Read More
Yan sanda a Katsina sun ceto mutane 10 a hannun ‘yan bindiga.

Yan sanda a Katsina sun ceto mutane 10 a hannun ‘yan bindiga.

' Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 'Yan sanda a Katsina sun sami nasarar ceto fasinjoji 10 da 'yan bindiga sukai ƙoƙarin sacewa a ƙaramar hukumar Jibiya. Jami'in yaɗa labarai na rundunar 'yan sanda a jihar ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanar da haka a wata hira da manema labarai. Ya ce, lamarin ya faru ne a Magama Jibiya inda 'yan bindiga ɗauke da manyan bindiga ƙirar AK 47 suka kaiwa wata motar haya ɗauke da fasinjoji 10 farmaki. Da samun labarin lamarin 'yan sanda suka garzaya wajan inda akai ta bata kashi da 'yan ta'addan. ASP Sadiq ya bayyana cewa…
Read More

Saƙon Kirsimeti: Gwamnatin Tarayya ta rage farashin sufuri a hanyoyi 144 – Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce Gwamnatin Tarayya ta samar da tallafi ga harkar sufuri a yunƙurita na rage raɗaɗin talauci a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara. A yayin saƙonsa na Kirsimeti, Tinubu ya ce gwamnati ta samar da sufurin jiragen ƙasa kyauta da kuma ragi ga sufurin motoci a yayin tafiye-tafiye ga ƴan Nijeriya a lokacin bukukuwan. Tinubu ya kuma tabbatar wa al'umma cewa hanyoyi za su kasance cikin tsaro, ya na mai cewa sun samar da sauƙin tsadar ababen hawa a titina 144 a sassa daban-daban na faɗin Nijeriya. Ya yi kira ga kiristoci da…
Read More

Mahaifiyar gwamnan Jigawa ta rasu

Daga BELLO A. BABAJI A safiyar ranar Laraba ne Mahaifiyar Gwamnan Jihar Jigawa (Umar Namadi), Hajiya Maryam Namadi ta rasu. Sakataren Labaran gwamnan, Hamisu Mohammed Gumel ya faɗi hakan a wata sanarwa da ya fitar. Ya ce za a gudanar jana'izarta ne a yammacin ranar kamar yadda addinin musulunci ya tanadar a garin Kafin Hausa. Gwamnan da iyalansa sun buƙaci al'umma da su sanya ta a cikin addu'o'insu don samun rahamar Allah SWT.
Read More

Kirsimeti: Tinubu ya yi kira da a yi wa ƙasa addu’ar samun nasarori

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ƴan Nijeriya da su kasance masu kyautata zato da tsammanin cimma nasarori yayin da ake gudanar da bukukuwan ƙarshen shekara. A cikin wani saƙo na musamman ga al'umma da ke ɗauke da sanya hannunsa, Shugaba Tinubu ya taya mabiya addinin Kirista murnar Kirsimeti da fatan alheri a sabuwar shekara ta 2025 dake cigaba da ƙaratowa. Ya ce Kirsimeti lokacin ne na nuna godiya ga Ubangiji da kuma yaɗa soyayya, zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al'umma. Yace duk da cewa ƙasar tana fama da matsaloli a sassanta,…
Read More
An yi zanga-zanga a Ibadan dalilin tsare tsohuwar matar Ooni

An yi zanga-zanga a Ibadan dalilin tsare tsohuwar matar Ooni

Wasu mazauna Ibadan sun gudanar da zanga-zanga a kan hukuncin kotu na tsare tsohuwar matar Ooni, Naomi Ogunwusi, fitaccen mai gabatar da shirye-shirye Oriyomi Hamzat da shugaban makarantar Islamic High School bisa zargin su da hannu a turmutsutsun da ya yi sanadin mutuwar yara sama da 36. Wannan al’amari ya faru ne yayin wani taron bikin Kirsimeti na yara da aka gudanar a makarantar. Kotun Majistare a Ibadan, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Olabisi Ogunkanmi, ta bada umarnin tsare su a gidan yari na Agodi har zuwa 13 ga Janairu, lokacin da za a sake sauraron shari’ar. ‘Yan sanda sun tuhumi…
Read More
Kirsimeti: Atiku ya yi kira a zauna lafiya da nuna ƙaunar juna

Kirsimeti: Atiku ya yi kira a zauna lafiya da nuna ƙaunar juna

Daga USMAN KAROFI Tsohon mataimakin shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su rungumi soyayya da haɗin kai, yana mai cewa lokaci na Kirsimeti ya kamata ya zama abin koyi wajen zaman lafiya da fahimtar juna. Atiku ya bayyana haka ne cikin wani saƙo na musamman da ya fitar a Abuja, inda ya ja hankalin ‘yan ƙasa kan muhimmancin nuna tausayi da sadaukarwa domin cigaban al’umma. A cikin saƙonsa, Atiku ya ce lokaci na Kirsimeti ya dace muyi tunani mai zurfi game da muhimmancin haɗin kai da zaman tare. Ya kuma yi kira ga shugabannin siyasa…
Read More
Jam’iyyar NNPP ba ta rabe ba – Asiwaju Shittu

Jam’iyyar NNPP ba ta rabe ba – Asiwaju Shittu

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Tsohon shugaban jam’iyyar Alliance National Party (ANP), Asiwaju Moshood Shittu, ya musanta raɗe-raɗin da ake yi cewa an samu rikici a cikin jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP). Da yake magana yayin wani taron manema labarai a Abuja jiya, Shittu ya jaddada cewa, jam’iyyar NNPP ƙarƙashin jagorancin mai girma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na nan dunƙulalliya, mai ƙarfi, kuma ita ce kaɗai jam’iyyar adawa mafi ƙarfi da za ta iya lashe kujerar shugaban Ƙasa a 2027. Ya ƙara da cewa, jam’iyyar Alliance National Party (ANP) na daga cikin jam’iyyun da suka yi haɗaka da…
Read More