24
Dec
24
Dec
Daga BELLO A. BABAJI Allƙalin wata kotun Shari'a dake Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, ya umarci a tsare waɗansu mutane uku da aka alaƙanta su da hannu a iftila'in da ya auku a makarantar Bashorun Islamic High School. Mutanen sune Frinsifal ɗin makarantar, Mista Abdullah Fasasi da mai gidan rediyon Agidigbo Alhaji Oriyomi Hamzat da kuma Naomi Silekunola, wadda ita ce tsohuwar matar Ooni na Ile Ife, Adeyeye Ogunwusi. Alƙali Olabisi Ogunkami wanda ya yi hukunci game da lamarin ya umarci a tsare mutane ukun a gidan yarin Agodi. Ana zargin mutanen ne bisa aikata laifuka huɗu da suka ci…
24
Dec
Daga RABIU SANUSI a Kano Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Aikin Asibiti ta Jihar Kano, DMCSA ta nemi haɗin kan Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa, NDLEA reshen Kano don yaƙar mummunar ta'adar nan ta ta'ammali da miyagun ƙwayoyi musamman a tsakanin ma'aikatan gwamnati. Shugaban DMCSA, Famasist Gali Sule ne ya bayyana haka yayin da ya kai ziyarar aiki zuwa ofishin NDLEA dake nan Kano a safiyar ranar Litinin. Ya nuna damuwarsa sakamakon yadda shan miyagun kwayoyi ya zama ruwan-dare musamman a tsakanin matasa, a faɗin jihar. Shugaban ya ce za su yi wa dukkanin ma'aikatan…
24
Dec
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya buɗe makarantar marayu da yara marasa galihu a jihar. Cibiyar Magnet Academy AL- HUDA da ke ƙasar Amurka ta assasa ginin makarantar. A jawabin sa gwamna Raɗɗa ya bayyana mahimmancin tallafawa marayu da yace lada ne ba iyaka . Sai yayi kira ga al'ummar musulmi da su tashi tsaye wajan taimaka wa marayu ta inganta rayuwar su da sa su cikin farin ciki. Malam Dikko Raɗɗa ya kuma nuna jin daɗin sa ga yadda yaga tsarin ginin da kayayyakin da makarantar ta tanada na fara gudanar da karatun.…
24
Dec
Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Adamawa, Umaru Fintiri ya sanar da ƙirƙiro sabbin sarakuna da masarautu guda shida a jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a gidan gwamnatin jihar dake Yola wanda wani ɓangare na ayyukan ƙarshen shekara. Masarautun sune; Hoba, wato Hong mai daraja ta biyu; Madagali (Gulak mai daraja ta biyu); Michika (Michika, daraja ta biyu); Fufore (Fufore daraja ta biyu); Gombi (Gombi, daraja ta uku); Maiha (Maiha, daraja ta uku); Yungur (Dumne, daraja ta uku),” kamar yadda gwamnan ya wallafa a shafin X ranar Litinin. Ya ce gyare-gyaren za su taimaka wajen inganta harkokin gwamnati da ƙarfafa…
24
Dec
Daga RABIU SANUSI a Kano A ƙoƙarin kare rayukan ƙananan yara da aka haifa a jihar Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dawo da ayyukan rigakafi na yau da kullum, waɗanda aka yi watsi da su na tsawon watanni 18 a ƙarƙashin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba tare da wata hujja ba. Kakakin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa da ya fitar da sanarwar ga manema Labarai. Rahotanni sun bayyana cewa daga farkon wa'adinsa a 2023, Gwamna Yusuf ya bada fifiko ga lafiyar mata da yara tare da nuna matuƙar damuwa kan dakatar da shirye-shiryen rigakafin…
23
Dec
Daga USMAN KAROFI Ankama mutane huɗu da ake zargi da kasancewa masu alaƙa da fitaccen shugaban ƴan ta'adda, Bello Turji, a gidan yarin Kuje bisa umarnin Mai Shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja. Waɗanda ake zargin sun haɗa da Musa Muhammad Kamarawa, Abubakar Hashimu (wanda aka fi sani da “Doctor”), Samuel Chinedu, da Lucky Chukwuma. Sun musanta zargin da ake musu bayan an karanta musu tuhume-tuhume 11 da ake yi musu a kotu. Mai Shari'a Nwite ya ɗage shari'ar zuwa ranar 10 ga Fabrairu don ci gaba da sauraren shari'ar. A cikin tuhume-tuhumen, ana zargin waɗanda…
23
Dec
Daga BELLO A. BABAJI Rundunar ƴan sandan jihar Kano sun gargaɗi ƴan wasan barƙwanci game da ɗaukar bidiyo akan titina wanda hakan ke haifar da cinkoson ababen hawa. Rundunar ta lura cewa cinkoson ababen hawa a musamman manyan titina saboda ire-iren ayyukan wanɗanda saɓa wa dokar ƙasa ne ka iya haifar da hatsari. Don haka ne take gargaɗin al'umma da su ƙaurace wa aikata hakan, ta na mai kira ga iyaye da su ja wa ƴaƴansu kunnuwa kan shiga irin ayyukan. Ta kuma ce tana cigaba da tabbatar da zaman lafiya acikin al'umma ta hanyar ɗaukar matakan da suka dace…
23
Dec
Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar ƴan kasuwar fetur ta Ƙasa, IPMAN ta yi kira ga al'umma da kada su karaya wajen sayan man fetur inda ta ce tana da isasshen man fetur a gare su yayin da ƙarshen shekara ke ƙara ƙaratowa. Sakataren Labaran ƙungiyar, Mista Ukadike Chinedu ya bayyana a ranar Lahadi, a Abuja, kamar yadda NAN ya ruwaito. Chinedu ya yaba wa matatar Ɗangote bisa rage farashin lita zuwa Naira 899.5 wanda hakan zai rage tsadar farashin sufuri a lokacin tafiye-tafiye na bukukuwan ƙarshen shekara. Ya ce hakan shi ne amfanin kula da farashin daga manyan ƴan kasuwa,…
23
Dec
Daga RABIU SANUSI a Kano An bayyana cewa dukkan wanda zai kawo tashin hankali a Jihar Kano ko Ƙasar nan ba masoyin da za'ayi alfahari da shi bane a cikin Al'umma. Babban darakta na ayyuka na musamman a fannin tsaro AVM Ibrahim Umar(Rtd) ne ya bayyana haka yayin wani sulhu da ya jagoranta a cigaba da faɗan daba dake wanzuwa a anguwannin Zage,Ƙofar Mata,Yakasai da Zango da sauran wasu yankuna dake cikin birnin Kano. AVM ya ce a wannan gwamnati ta Gwamna Abba Kabir Yusuf kowa yasan irin ƙoƙarin da ta ke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma don…
