23
Dec
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Tsohon gwamnan Jihar Zamfara kuma ƙaramin ministan tsaro, Bello Muhammad Matawalle ya yabawa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan matakin da ta ɗauka na dakatar da dokar hana haƙar ma'adinai a ƙasar nan cikin gaggawa. Matawalle ya yi wannan yabon ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a gidansa da ke Gusau a jiya. A cewar sa, matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na ɗage haramcin haƙar ma’adanai, abu ne mai kyau, a cewar shi matakin zai bunƙasa tattalin arzikin jihohin da Allah ya albarkace su da albarkatun ma’adinai a yankin…
