Labarai

Za a ƙarfafa gyare-gyaren tsarin tattalin arziki da Tinubu ke yi a 2025, inji Ministan Yaɗa Labarai

Za a ƙarfafa gyare-gyaren tsarin tattalin arziki da Tinubu ke yi a 2025, inji Ministan Yaɗa Labarai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya tabbatar da cewa shekarar 2025 za ta zama shekarar da za a ƙarfafa gyare-gyaren da ake aiwatarwa ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, waɗanda tuni suke haifar da sakamako mai kyau a fannonin tsarin tattalin arziki. Idris ya bayyana haka ne a ranar Talata a Abuja a wurin taron atisayen shugabanci da gudanarwa wanda gidan rediyon Muryar Nijeriya (ɓON) ya shirya wa ma’aikatan sa. A jawabin sa, Idris ya jaddada rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen bayyana nasarorin gwamnatin. Ya…
Read More
An gurfanar da mutum biyu a gaban kotu kan zargin wulaƙanta gawa

An gurfanar da mutum biyu a gaban kotu kan zargin wulaƙanta gawa

An gurfanar da wasu mutum biyu a gaban wata Kotun Majistare mai zamanta a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, kan zargin wulaƙanta wata gawa. Kamfanin Dillancincin Labarai na Nijeriya (NAN), ya rawaito ana tuhumar mutum biyun ne da aka gurfanar ranar Juma’a da haɗin baki wajen wulaƙanta gawar ta hanyar jefar da ita a wani shago. Sai dai babu wani cikakken bayani kan yadda aka yi aka kai gawar shagon, da kuma ko sun aikata mata wani rashin ɗa’a. Lauyar mai tuhuma, ASP Foluke Adedosu, ta shaida wa kotun cewa, an aiktata laifin ne ran 12 ga Satumba, laifin da…
Read More
Ya yi wa ’yar cikinsa fyaɗe

Ya yi wa ’yar cikinsa fyaɗe

An kama wani magidanci mai shekaru 40, Kenneth Nwangwu da laifin lalata ’yarsa mai shekaru 9 a ƙauyen Akama, Igbo-ukwu, ƙaramar hukumar Aguata ta jihar Anambra. Rundunar ’yan sandan ta kama wanda ake zargin ne biyo bayan samun bayanan sirri da aka samu. Wanda ake zargin, a halin yanzu yana hannun ’yan sanda a sashin binciken manyan laifuka da bincike na jihar (CID), Awka, duk da ya musanta zargin da ake masa. “Wannan aikin maƙiyana ne domin suna kishina. Ina ciyar da ɗiyata ne kawai, ba wani abu ba,” inji shi. A halin yanzu, binciken likita da aka yi wa…
Read More
William Tubman: Wanda ya zamanartar da Laberiya

William Tubman: Wanda ya zamanartar da Laberiya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Laberiya kasa ce ta 'yantattun bayi, wadda aka gina da musguna wa 'yan ƙasar lokacin da aka zaɓi William Tubman a matsayin shugaban ƙasa. Bayan haɗa kan mutane, ya shirya ƙasar bisa tsarin ci-gaba wanda bai samu ba. An haifi William ɓacanarat Shadrach Tubman ranar 29 ga watan Nuwamba 1895. Ya fito daga yankin kudu maso gabashin Laberiya, daga garin da ake kira Harper na gundumar Maryland. Sunan wuraren ya yi kama da na Amurka, saboda Jamhuriyar Laberiya ta ayyana samun 'yanci daga Amirka a shekarar 1947 da 'yantattun bayi suka yi, waɗanda suka dawo daga…
Read More

Bayan shekara biyar, Gwamnatin Tarayya ta cire takunkumin haƙar ma’adanai a Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI Ministan Ci-gaban Ma'adinai, Dele Alake ya faɗi hakan yayin hira da manema labarai a ranar Lahadi, kamar yadda Kakakin Ma'aikatar, Segun Tomori ya bayyana. Ministan ya ce gwamnati ta yanke soke takunkumin haƙar ma'adanan ne la'akari da yadda ake samun ci-gaba game da halin tsaro a jihar. Alake ya bayyana cewa akwai riba sosai ga Nijeriya a irin ma'adanan da Zamfara take da su waɗanda suka haɗa da Gwala-gwalai, 'Lithium' da 'Copper belts'. Ya kuma ce an dakatar da ayyukan haƙar ne sakamakon samun waɗanda suke bi ta haramtattun hanyoyi acikin masu haƙar wanda hakan ke…
Read More

Daga ranar Litinin za a riƙa sayar da fetur a Naira 935 – IPMAN

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar ƴan kasuwar man fetur (IPMAN) ta ce farashin kowacce lita za ta koma N935 daga ranar Litinin la'akari da sabon tsarin da Kamfanin Ɗangote ya yi. IPMAN ta ce tunda kamfanin Ɗangote ya rage farashi hakan ya sa take ganin dacewar a samu tsari na bai-ɗaya daga gidajen man ƴan kasuwar a faɗin Nijeriya. Shugaban ƙungiyar, Alhaji Maigandi Garima ya bayyana hakan a ranar Lahadi, yayin hira da kamfanin dillancin labarai (NAN) inda ya jinjina wa ci-gaban da aka samu daga Ɗangote. A ƴan kwanakin nan ne Kamfanin Ɗangote ya sanar da rage farashin da…
Read More
Sufeto Janar ya gargaɗi masu raba tallafi ga talakawa bisa rashin tsari

Sufeto Janar ya gargaɗi masu raba tallafi ga talakawa bisa rashin tsari

Daga BELLO A. BABAJI Sufeto Janar na ƴan sanda, Kayode Egbetokun ya yi gargaɗi game da hargitsi da rashin tsaro da ake samu wajen raba kayayyakin tallafi ga mutane a yayin bikin Kirismas. Sufeton ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Kakakinsa, Muyiwa Adejobi ya fitar, inda ya ce duk wanda aka samu da sakaci a ɓangarensa yayin irin aikin, za a kama shi da aikata babban laifi. Egbetokun ya koka kan rashin tsari dake tattare da irin aikin wanda ya haddasa asarar rayuka da dama a Nijeriya musamman a irin wannan lokaci na bukukuwan ƙarshen shekara. A ranar…
Read More
Kasafin 2025: Gyaran makwancin Tinubu da Shettima zai lashe Naira biliyan 6.36

Kasafin 2025: Gyaran makwancin Tinubu da Shettima zai lashe Naira biliyan 6.36

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta ware zunzurutun kuɗaɗe da adadinsu ya kai N6,364,181,224 don gyaran gidajen zaman Shugaba Bola Tinubu da na Mataimakinsa, Kashim Shettima da kuma na wasu manyan muƙarrabansu a kasafin kuɗin shekarar 2025. Haka kuma rahotanni sun bayyana cewa kuɗin gyaran Fadar shugaban ƙasa dake Abuja, za ta riƙa lashe Naira biliyan 5.49 kamar yadda yake a ƙudirin gyare-gyare na 2025 da aka gabatar wa majalisa. Daga cikin kasafin, za a yi amfani da miliyan N765 wajen gyaran gidan da mataimakin shugaban ƙasar yake zama da kuma masauƙinsa. Gyaran sashin da Shugaba Tinubu yake zama…
Read More
NDLEA ta kama ɗan kasuwa da hodar iblis a tashar jirgin sama na  Malam Aminu Kano

NDLEA ta kama ɗan kasuwa da hodar iblis a tashar jirgin sama na Malam Aminu Kano

Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) sun kama wani ɗan kasuwa, Olisaka Chibuzo Calistus, a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano da ke Jihar Kano. Ana zargin wanda aka kama, wanda ya ce yana aikin shigo da kaya da fitar da su, da ɗauke da ƙwayoyi 256 na hodar iblis masu nauyin kilogiram shida a ranar Lahadi, 15 ga Disamba. Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi. “Wannan kamen, wanda shi ne mafi girma tun da aka kafa ofishin hukumar NDLEA a filin jirgin sama na Kano a…
Read More
Tsohon Allƙalin Kotun Ƙoli ya rasu

Tsohon Allƙalin Kotun Ƙoli ya rasu

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi Allah ya yi wa tsohon Allƙalin Kotun Ƙolin Nijeriya, Mai Shari'a Usman Muhammed Argungu rasuwa a safiyar yau Lahadi. Marigayi Mai Shari'a Argungu ya rasu ne a gidansa dake garin Argungu a Jihar Kebbi bayan fama da wata jinya. Ya rasu yana da shekaru 90 inda ya bar mataɗaya da ƴaƴa 12 waɗanda daga cikin su akwai alƙalan manyan kotuna da suka haɗa da; Alƙali Hassan Usman Muhammed da Alƙali Raliya Usman Muhammed da kuma jikoki sama da talatin. Kafin rasuwarsa, ya yi aiki a matsayin Allƙalin Alƙalan ƙasar Gambia, babban Joji a jihohin Sokoto,…
Read More