Labarai

Turmutsutsun Anambra: Mutum 22 sun rasa rayukansu

Turmutsutsun Anambra: Mutum 22 sun rasa rayukansu

Hukumar ƴan sanda yankin Anambra ta bayyana cewa yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon turmutsutsun jama’a a jihar ya kai 22, a cewar rahoton da aka bayar a ranar Lahadi. Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya ce an fara bincike kan lamarin. Ikenga, wanda shi ne babban sufeton ‘yan sanda, ya ce waɗanda suka ji raunuka suna karɓar magani a asibiti. “Kwamishinan ‘yan sanda, Nnaghe Obono Itam, ya ziyarci asibitin da ake kula da waɗanda lamarin ya shafa, wanda ya faru a ranar 21/12/2024 a Okija, ƙaramar hukumar Ihiala, kuma ya bayyana cewa mutane 22 sun…
Read More
Tinubu ya umarci sojoji su kawo ƙarshen ta’addanci a 2025, inji Ministan tsaro

Tinubu ya umarci sojoji su kawo ƙarshen ta’addanci a 2025, inji Ministan tsaro

Daga USMAN KAROFI Shugaba Bola Tinubu ya umurci sojojin Nijeriya da su tabbatar da kawo ƙarshen ayyukan ƴan ta'adda kafin shekarar 2025, kamar yadda ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle, ya bayyana. Matawalle ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin da yake jawabi ga ƴan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a gidansa da ke Gusau, inda ya yi alƙawarin cewa sojoji za su yi duk abin da ya dace don bin umarnin Shugaban Ƙasa. Tsohon gwamnan Jihar Zamfara ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta kammala shirye-shiryen tura ƙarin sojoji da kayan aikin soji zuwa yankunan da matsalar tsaro ta fi…
Read More

Tinubu ya fasa halartar wasannin Legas kan iftila’in Anambara da Abuja

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya soke tafiya jiharsa ta Legas inda a nan ne ya saba yin hutu yayin bikin Kirismas, domin karrama waɗanda suka mutu a sakamakon turmutsutsin da ya janyo hasarar rayuka a Abuja da Jihar Anambra. Mutane 10 ne suka mutu ciki har da ƙananan yara, inda da dama suka samu raunuku a wani turmutsutsu da ya faru a cocin Catholic dake Maitama a Abuja. A wata sanarwa da rundunar ƴan sanda ta fitar a Abuja, ta ce cikin waɗanda suka mutu akwau ƙananan yara huɗu, yayin da mutum takwas suka samu munanan…
Read More

Nijeriya ta musanta zargin tana da hannu a harin bututun man Nijar

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta musanta ikirarin da wasu hukumomin ƙasar suka yi na cewa tana da hannu a harin 13 ga watan Disamba da aka kai wa bututun mai na Nijar-Benin dake Gaya, yankin Dosso da Jamhuriyar Nijar. Kakakin Ma'aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce Gwamnatin Nijeriya ta musanta kowane irin alaƙa da ƙungiyar ta'addanci ta Lakurawa ko zargin jami'anta suna da hannu a lamarin. Ƙasar ta jajenta wa Nijar game da harin tare da jaddada ƙoƙarinta wajen daƙile ta'addanci da ƙaurace wa kusanci da ire-iren waɗannan…
Read More

Matatar Ɗangote ta haɗa kai da MRS don sayar da fetur a N935

Daga BELLO A. BABAJI Matatar Ɗangote ta ce ta haɗe kan ne da Kamfanin MRS don fara sayar da litar fetur a N935 a baki ɗaya gidajen mansu na Nijeriya a ƙoƙarinsu na sauƙaƙa wa al'umma. Hakan na zuwa ne bayan Kamfanin Man fetur na Ƙasa (NNPCL) ya sanar da rage farashin lita zuwa ƙasa da N1,000. A wani rubutu da aka wallafa a shafin X, Shugaban rukunin Kamfanin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa ƙoƙarinsa na amfani da naira a yayin gudanar da kasuwancin ɗanyen mai wanda hakan ya yi sanadiyyar rage farashin fetur…
Read More

Za mu tara harajin Naira bilyan 80 a 2025 – Gwamna Abba

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya bayyana ƙudirinsa na hukunta duk waɗanda suka ƙi biyan haraji a shekarar 2025, inda ya bayyana shirin gwamnatinsa na yunkurin samar da kuɗin shigar da bai gaza Naira bilyan 80 a sabuwar shekarar ba. Ya kuma buƙaci kwamishinoninsa da manyan sakatarorin gwamnati da sauran masu-ruwa-da-tsaki da su ƙara ƙaimi wajen gudanar da ayyukan da za su kawo ma ci-gaba a jihar. Gwamnan ya bayyana hakane a yayin da yake rufe taron Majalisar Zartarwa da manyan sakatarorin gwamnatin Kano na kwanaki uku da aka gudanar a ɗakin taro…
Read More
A bikin mu na wannan shekarar za mu haska fim din ‘Nanjala’- Kabiru Jammaje

A bikin mu na wannan shekarar za mu haska fim din ‘Nanjala’- Kabiru Jammaje

DAGA MUKHTAR YAKUBU Kamar yadda a duk ƙarshen shekara, makarantar Jammaje Academy wadda take koyar da ilimin Turanci tare da ɗaukar nauyi shirya finafinai take gudanar da taru a duk ƙarshen shekara, wanda a wajen taron ake haska fim ɗin da Shugaban Makarantar Malam Kabiru Musa Jammaje yake shiryawa ta ƙarƙashin kamfanin sa mai su Jammaje Production, a bana ma za a yi gagarumin taro a ranar 26 ga Disamba a babban ɗakin taro na Jami'ar Bayero da ke Kano inda za a gabatar da jawabai tare da nishaɗantar da mahalarta taron. Kamar dai yadda Malam Kabiru Musa Jammaje ya…
Read More
Gwamnatin Kano za ta fara gurfanar da masu ƙin biyan haraji a 2025

Gwamnatin Kano za ta fara gurfanar da masu ƙin biyan haraji a 2025

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, za ta fara gurfanar da duk masu ƙin biyan ƙuɗaɗen haraji a shekarar 2025, a wani ɓangare na sauye-sauyen da ta ke yi a harkokin haraji. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Blueprint Manhaja daga Jihar Kaduna a ranar Asabar. A cewar sanarwar, Shugaban hukumar tattara kuɗaɗen haraji ta Jihar Kano (KIRS), Dr. Zaid Abubakar, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da jawabi ga Gwamnan Jihar…
Read More

‘Yan kasuwa sun rage farashin fetur

Daga BELLO A. BABAJI Ƴan kasuwar man fetur daga matatar Ɗangote sun rage farashin lita daga N1,060 zuwa N939.50. Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa gidajen mai ciki har da MRS sun rage farashin litarsu a ranar Juma'a. Gidan man MRS dake Ojota a Legas su na sayar da lita a N939.5. Hakan na zuwa ne jim-kaɗan da Kamfanin Ɗangote ya sanar da rage farashin lita daga N970 zuwa 899.5 don sauka ga al'umma yayin da ake shirye-shiryen bukukuwan ƙarshen shekara. Kamfanin ya kuma sahale wa kowane kwastoma sayan mai a bashi na adadin da ya saya kuɗi a hannu ta…
Read More

Amurka ta kashe jagoran IS a Siriya yayin wani hari

Daga BELLO A. BABAJI Amurka ta ce kashe jagoran ƙungiyar IS, Abu Yusif a ƙasar Siriya. Dakarun Amurka na (Centcom) sun ce sun kai farmaki ne ta sama inda suka nufi Abu Yusif a yankin gabashin ƙasar. Jami'an Amurka sun ce sun kuma kashe wani wani mamban IS. An kai harin ne a wani yankin dake ƙarƙashin mulkin Siriya da jami'an Rasha. Kwamandan Centcom, Janar Michael Erik Kurilla ya ce Amurka da ƙawayenta dake aiki a yankin ba za su bar ISIS su yi amfani da damar halin da ƙasar take ciki. IS ta na yunƙurin fasa wajen da aka…
Read More