Labarai

Yahaya Bello ya shaƙi iskar ƴanci bayan cike ƙa’idodin beli

Daga BELLO A. BABAJI An sako tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello daga gidan gyaran hali na Kuje dake Abuja bayan cike ƙa'idodin beli da Babbar Kotun Tarayya ta gindaya masa. Kakakin Hukumar Gyaran hali (NCoS) na Abuja, Adamu Duza ya bayyana hakan inda ya ce an sako tsohon gwamnan ne a yammacin Juma'a. A baya ne Alƙalin Maryanne Anenih ta yi hukuncin belin Yahaya Bello akan Naira miliyan 500 da kuma mutum uku da za su tsaya masa dake da kadarori a Maitama ko Guzape ko kuma Asokoro duk a Abuja. Kotun ta kuma umarci Bello da ya bayar…
Read More

Kotu ta haramta zaɓukan mazaɓu na APC a Jihar Ribas

Daga BELLO A. BABAJI Babbar Kotun Jihar Ribas dake Fatakwal ta haramta zaɓukan ƙananan hukumomi da na jiha da jam'iyyar APC ƙarƙashin jagorancin Tony Okacha ta shirya. APC reshen jihar ta gudanar da zaɓukan duk da hukuncin kotun na haramta yin hakan ƙarƙashin Okocha. A ranar 14 ga watan Disamba ne Shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya rantsar da sabbin jagorancin jam'iyyar reshen jihar. Wasu mambobin jam'iyyar sun shigar da ƙara, a inda suka yi zargin cewa an ware su cikin harkokin jam'iyyar.
Read More

Gwamnatin Katsina ta bada tallafin N38m ga iyalan waɗanda ta’addanci ya rutsa da su a Musawa da Sabuwa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A ƙoƙarinsa na yaƙi da da ta'addanci, fashi da makami, satar dabbobi, da kuma garkuwa da mutane tare da nuna alhininsa ga waɗanda lamarin ya shafa, gwamna Dikko Umar Raɗɗa na Jihar Katsina ya bada tallafin kuɗi Naira miliyan 38 ga iyalan mutanen da harin ƴan bindiga ya shafa a ƙananan hukumomin Musawa da Sabuwa. Waɗanda da suka amfana da tallafin kuɗaɗen sun haɗa da mutanen da ƴan bindigar suka kashe, da mutanen da suka jikkata, da mutanen da ɓatagarin suka yi garkuwa da su, da kuma waɗanda suka yi asarar dukiyoyinsu a sakamakon harin…
Read More

Nasarorin da aka samu a yaƙi da cin zarafin ƴaƴa mata a Filato

Daga SARATU IBRAHIM MACHU Da farko, Allah ya halicci mace ne don ta zama mataimakiya ga namiji wanda hakan ke nuna tana da rauni kuma ta na buƙatar kariya da tsaro ta kowacce hanya. Cin zarafin ƴaƴa mata ya yi ƙamari a ƴan shekarun nan wanda ya kai ga har wasu matan sun rasa rayukansu a gidajen aure. Idan rikici ya faru a garuruwa, mafi yawanci mata da yara ne suka fi jikkata. Domin dakile cin zarafin mata a duniya baki ɗaya, Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) ta keɓe kwanaki 16 domin gudanar da shirye-shirye daban-daban na wayar da kan jama'a…
Read More

Har yanzu farashin fetur N1,025 ne duk da Kamfanin Ɗangote ya rage

Daga BELLO A. BABAJI Kawo yanzu jama'a ba su gani a ƙasa ba game da ragin farashin litar fetur da Kamfanin Ɗangote ya sanar da cewa ya yi a ƴan kwanakin nan zuwa N899.5 daga N970. Mafi yawancin gidajen mai a Kano, Abuja, Fatakwal da Legas suna sayar da man ne akan N1,025 wanda shi ne mafi ƙarancin farashin kamfanin NNPCL sai kuma na manyan ƴan kasuwa da ke sayarwa a N1,070 da kuma N1,100 na ƴan kasuwa masu zaman kansu. Kamfanin Ɗangote ya ce ya yi ragin ne don sauƙaƙe wa al'umma halin matsin da ake ciki a yayin…
Read More
Duk wasu matakai na gyara harkar ilimi a jihar Kano Gwamna Abba na ɗauka – Bashir Baffa

Duk wasu matakai na gyara harkar ilimi a jihar Kano Gwamna Abba na ɗauka – Bashir Baffa

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana cewa duk wani mataki da ya kamata a ɗauka na gyara ilimi, Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf zuwansa gwamnati ya na ɗauka sakamakon ya zo ya samu fannin a ragargaje da sai an yi da gaske. Allah ya kawo shi ya sa harkar cigaban ilimi a gaba fiye da komai ba don haka ba da ba a san yadda za a samu kai ba. Babban Sakataren ma'aikatar ilimi na jihar Kano, Alhaji Bashir Baffa Muhammad ne ya shaida hakan ga manema labarai, ya ƙara da cewa yanzu a matsayinsu na ma'aikata…
Read More
Shugaban majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya goyi bayan ƙudurin dokar haraji 

Shugaban majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya goyi bayan ƙudurin dokar haraji 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce ƙarancin harajin da Nijeriya ke samu ya kasance wani babban cikas ga ci gaban ƙasar. Abbas ya bayyana haka ne a wajen gabatar da ƙudurin kasafin kuɗin 2025 ga wani zama na haɗin gwiwa na majalisun tarayya da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi a Abuja ranar Laraba. A cewarsa, rabon harajin Nijeriya zuwa kayan da ake samarwa a ƙasa, GDP, a halin yanzu ya yi ƙaranci da kusan kashi 10.9 cikin 100 a 2024, inda ya ce yana cikin mafi ƙaranci a Afirka, wanda ya yi…
Read More
’Yan sanda sun kama tsohuwar matar Ooni bisa mace-macen turmutsutsu a Ibadan

’Yan sanda sun kama tsohuwar matar Ooni bisa mace-macen turmutsutsu a Ibadan

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta tabbatar da cafke Naomi Silekunola, tsohuwar matar Ooni na Ile-Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi. Hakan ya biyo bayan wani mummunan turmutsitsin da ya faru ne a wajen bikin yara da ta shirya wanda ya faru a ranar Laraba, 18 ga watan Disamba, 2024, a babbar makarantar Islamiyya, Bashorun, Ibadan, kuma ya yi sanadiyyar mutuwar ƙananan yara da dama, tare da jikkata wasu. A wata sanarwa a ranar Alhamis, Osifeso Adewale, kakakin rundunar ‘yan sandan Oyo, ya ce yara 35 ne suka mutu yayin da wasu 6 suka samu…
Read More
Sakin Nnamdi Kanu ba zai kawo ƙarshen rashin tsaro a Kudu Maso Gabas ba – Gwamnan Anambra

Sakin Nnamdi Kanu ba zai kawo ƙarshen rashin tsaro a Kudu Maso Gabas ba – Gwamnan Anambra

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, a ranar Talata, ya ce tabbas sakin jagoran ’yan awaren Biyafara, Nnamdi Kanu, da ake tsare da shi ba zai kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ta addabi yankin Kudu maso Gabas ba. Soludo ya bayyana cewa, masu aikata laifuka suna saka rigar masu fafutukar kafa ƙasar Biyafara kuma a yanzu suna amfani da fafutukar ƙafa ƙasar Biyafara da sunan Kanu wajen aikata miyagun laifuffuka da rura wutar rashin tsaro a yankin Kudu maso Gabas. Soludo ya bayyana cewa, suna fakewa da biyafara, waɗannan mutane sun koma ga “ta'addanci,” suna…
Read More
UNESCO ta sanya hawan Kano cikin manyan tarukan al’ada na duniya

UNESCO ta sanya hawan Kano cikin manyan tarukan al’ada na duniya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Ilimi da Kimiya da Al'adu ta Majalisar ɗinkin Duniya (UNESCO), ta gabatar da takardar shaidar sanya hawa a Kano a cikin jerin sunayen manyan tarukan al'adu a Nijeriya. Ambasada Hajo Sani, Wakiliyar Dindindin ta Nijeriya a UNESCO, ta miƙa takardar shaidar jinjina ga ministar fasaha, al'adu, yawon buɗe ido da kuma tattalin arzikin ƙasa Hannatu Musawa ranar Talata a Abuja. Hajo Sani ta ce, an yi la’akari da takardar da ke jinjina wa hawan Kano a hukumance kuma an amince da shi a zaman taro na 19 na kwamitin kula da al’adun gargajiya…
Read More