Labarai

Ana binciken Azman kan zargin sayar wa kamfanin Iran jiragen sama

Ana binciken Azman kan zargin sayar wa kamfanin Iran jiragen sama

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kamfanin jiragen sama na Azman Air, ɗaya daga cikin manyan kamfanonin jiragen sama na cikin gida a Nijeriya, na iya fuskantar takunkumi kan zargin safarar jiragen Nijeriya biyu masu rijista zuwa Mahran Air na Iran. Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA) ta ce za ta rubutawa takwararta ta Iran, Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Iran (CAA.IRI) game da matsayin jiragen biyu. Jirgin - Airbus A340-600 tare da lambar rajista: 5N-AAM da Boeing 737-300 tare da lambar rajista: 5N-YSM - an sayar da su ba tare da sanin NCAA ba. An sayar…
Read More
Sojoji sun lakaɗa wa ma’aikatan Wike duka yayin da suka je rushe katafaren gida a Abuja

Sojoji sun lakaɗa wa ma’aikatan Wike duka yayin da suka je rushe katafaren gida a Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rahotanni sun bayyana cewa, wasu sojoji da ke aiki da umarnin wani Janar na soji a ranar Larabar da ta gabata sun kai hari kan jami’an kiyaye zaman lafiya da ke Sabon Lugbe, Abuja, domin rushe wasu haramtattun gine-gine a yankin. Jami’an sun je wurin ne domin rushe katangar wani gini da ke kan Lamba 416 da aka ce na wani Manjo Janar ne. Wani jami’in ma’aikatar ya bayyana irin halin da suke ciki kamar haka; “A wannan farmakin, an samu wani lamari da ya faru a Lamba 416 Sabon Lugbe mallakar Manjo Janar.…
Read More
’Yar hidimar ƙasa ta yanke jiki ta faɗi ta mutu a Kebbi 

’Yar hidimar ƙasa ta yanke jiki ta faɗi ta mutu a Kebbi 

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi  Wata matashiya 'yar hidimar ƙasa ta yanke jiki ta faɗi a sansanin yi wa ƙasa hidima da ya ke garin ɗakingari a ƙaramar Hukumar mulki ta Suru da ke jihar Kebbi. Matashiyar mai suna Tayachibiyacha Ebal dai ta yanke jiki ta faɗi ranar Larabar da ta gabata inda aka ɗauke ta zuwa ɗakin shan magani na sansanin horar da matasan don agajin gaggawa kafin daga bisani aka garzaya da ita zuwa asibitin tarayya (FMC) da ke Birnin Kebbi inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta bayan ƙoƙarin da suka yi na ceto rayuwarta ya ci tura.…
Read More
An kashe ’yan Nijeriya 614,937, an sace miliyan 2.2 a shekara ɗaya – NBS

An kashe ’yan Nijeriya 614,937, an sace miliyan 2.2 a shekara ɗaya – NBS

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS), ta bayyana cewa ’yan Nijeriya 614,937 aka kashe, yayin da aka sace mutum miliyan 2.2 daga watan Mayun 2023 zuwa Afrilun 2024. Wannan na ƙunshe ne cikin rahotonta mai taken Binciken Laifuka da Tsaron Jama’a na 2024. Rahoton, ya nuna cewa masu garkuwa da mutane sun karɓi jimillar kuɗi Naira tiriliyan 2.2 a matsayin kuɗin fansa, inda kowane lamari ke wakiltar kai aƙalla Naira miliyan 2.7. Yawancin mutanen da aka yi garkuwa da su (miliyan 1.6) sun fito ne daga ƙauyuka, yayin da Yankin Arewa Maso Yamma ya fi…
Read More
Mun karɓo bashin dala biliyan ɗaya don taimaka wa Matatar Ɗangote — NNPCL

Mun karɓo bashin dala biliyan ɗaya don taimaka wa Matatar Ɗangote — NNPCL

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), ya tabbatar da karɓo bashin dala biliyan ɗaya, don tallafawa aikin Matatar Ɗangote lokacin da ta fuskanci matsalar kuɗi. Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na NNPC, Olufemi Soneye ne, ya bayyana hakan yayin wani taro na masu ruwa da tsaki kan makamashi a Abuja. “Mun yi dabarar karɓo bashin dala biliyan ɗaya wanda aka tallafawa aikin Matatar ɗangote ta shawo kan matsalolin kuɗi da ta fuskanta,” inji Soneye. “Wannan tallafi ya bayar da damar buɗe ƙofa ga matatar mai ta farko mallakar ‘yan kasuwa a Nijeriya, wanda ke…
Read More
Za mu yi mai yiwuwa don ganin gwamnatin Kano ta cika alƙawarin da ta ɗauka – Kwamishinan Ruwa

Za mu yi mai yiwuwa don ganin gwamnatin Kano ta cika alƙawarin da ta ɗauka – Kwamishinan Ruwa

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Sabon Kwamishinan Ma'aikatar Ruwa na Jihar Kano Hon. Umar Haruna Doguwa ya ce a za su yi duk abinda ya kamata don ganin gwamnatin Kano ta sauke alƙawarin da ta ɗauka akan kyautata cigaban al'ummar Kano. Ya bayyana haka ne a lokacin da tawagar al'ummar masu ruwa da tsaki daga ƙaramar hukumar Doguwa suka yi masa rakiya ya karɓi aiki daga tsohon kwamishinan ma'aikatar ruwa da aka mayar ma'aikatar ilimi Gwani Ali Haruna Makoɗa a ma'aikatar ruwa ranar Talata. Ya ce daga abinda yake alfahari da shi a matsayin da ya yi na kwamishinan ilimi…
Read More
Mun yi bankwana da ECOWAS babu batun dawowa – Nijar, Mali da Burkina Faso

Mun yi bankwana da ECOWAS babu batun dawowa – Nijar, Mali da Burkina Faso

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso, waɗanda suka ƙulla sabon ƙawance, sun sake tabbatar da matsayarsu na ficewa daga ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS). Kasashen sun bayyana wannan matsaya ne yayin wani taro da ministocin harkokin wajen ƙasashen suka gudanar a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, a ranar Juma’a. Taron ya mayar da hankali kan samar da hanyoyin da za su bai wa jama’arsu damar yin zirga-zirga tare da samun damar gudanar da kasuwanci cikin sauƙi a faɗin yankin. Haka kuma, ministocin sun bayyana aniyarsu na kafa kwamitin ƙwararru da…
Read More
EFCC ta kama mutum 792 a Legas kan zargin damfara ta intanet

EFCC ta kama mutum 792 a Legas kan zargin damfara ta intanet

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Nijeriya, EFCC,Ola Olukoyede, ya bayyana cewa hukumar ta kama mutum 792 da ake zargi da aikata laifin damfara ta Intanet da suka gada da damfara ta hanyar soyayya. An gabatar da wadanda ake zargin ne a ranar Talata, 10 ga watan Disamba, 2024, yayin wani samame da jami'an hukumar suka kai a maɓoyar wadanda ake zargin, a cikin wani katafaren gini dake lamba bakwai, Oyin Jolayemi Street, ɓictoria Island, Lagos, bayan hukumar ta samu bayanan sirri. Da yake jawabi ga manema labarai, Olukoyede, a ranar…
Read More
An ƙaddamar da asibitin bayar da kulawa kyauta a Katsina

An ƙaddamar da asibitin bayar da kulawa kyauta a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya ƙaddamar da asibitin kulawa da marasa lafiya kyauta, musamman mata masu juna biyu da ƙananan yara a babban birnin jihar. Asibitin wanda wata gidauniyar taimaka wa al'umma ta Maiwada Global ta gina, an samar da shi ne a cikin birnin na Katsina. Wanda ya gina asibitin, Haruna Maiwada ya ce an samar da asibitin ne "Domin tallafa wa a'ummar yankin da magani da kulawa kyauta". Gwamnan jihar, Dikko Radda ya bayyana cewa, gina asibitin zai taimaka wa ƙoƙarin gwamnati na inganta lafiyar al'umma da rage wahalhalun da jama'a ke…
Read More
Ya kamata a riƙa tantance masu wa’azi a ƙasar nan, inji Sarki Sanusi

Ya kamata a riƙa tantance masu wa’azi a ƙasar nan, inji Sarki Sanusi

Daga HABU DAN SARKI a Jos Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu ya yi kira ga hukumomi a Nijeriya da su tabbatar da ganin an samar da wani tsari da zai riƙa tantance malamai da fastoci masu wa'azi, har da masu kafa ƙungiyoyin addini, domin magance matsalar yaɗa koyarwar da ba ta dace da addini, kundin tsarin mulkin ƙasa, da zaman lafiya ba. Babban basaraken na magana ne a wajen taron tunawa da cika shekaru 50 da ziyarar da babban malamin addinin Musuluncin nan Shaihu Ibrahim Inyass ya kai Jos, babban birnin Jihar Filato, bisa gayyatar tsohon shugaban…
Read More