21
Dec
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Jigawa, ta gano ma’aikatan bogi 6,348, yayin tantance ma’aikatan jihar, wanda hakan ya taimaka wajen hana zurarewar kuɗi sama da Naira miliyan 314 a wata da kuma Naira biliyan 3.7 a shekara. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Sagir Musa, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Dutse. Ya ce an gano ma’aikatan bogi bayan tantancewa da gwamnatin ta gudanar ta hanyar ɗaukar yatsunsu, wanda aka shirya domin tsaftace tsarin biyan albashi a jihar. “A yayin gudanar da wannan bincike, an gano ma’aikata…
