Labarai

Wike ya aika da sabon gargaɗi ga masu filaye na musamman a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bai wa masu filaye 762 a Maitama da Cadestral Zone da A10 da su biya kuɗin takardar shaidar mallaka ta CofO daga nan zuwa sati biyu ko kuma a ƙwace su. Wike ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Kakakinsa, Lere Olayinka ya fitar a ranar Juma'a inda ya ce ba burinsu ba ne ƙwace filayen, saidai sun yi haka ne don tabbatar da biyan kuɗaɗen ƙa'ida ga gwamnati. A watan Oktoba, 2024 ne aka bai wa masu filaye 3,273 wa'adin sati biyu su biya kuɗaɗen CofO da ake…
Read More
Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta Jihar Kano ta fitar da zakarun gasar gajerun labarai

Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta Jihar Kano ta fitar da zakarun gasar gajerun labarai

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar tace fina-finai da ɗab'i ta Jihar Kano ta bayyana sunayen mutum uku wanda suka lashe gasar gajerun labarai ta 2024. Waɗanda suka lashe gasar sun haɗa da Danladi Haruna (Zakariyya ) da labarinsa Gadon gida sai da Horo, da Hauwa Shehu da labarinta Bahaushe mai arziki ne da kuma Zubairu Musa Ballannaji da labarinsa mai suna Bahaushiyar Al'ada. Hukumar ta bayyana ranar 31/12/2024 a matsayin ranar da za ta karrama waɗanda su ka yi nasara a babban ɗakin taro da ke Mumbayya a unguwar Gwammaja, Kano.
Read More
Da Ɗumi-Ɗumi: A karon farko Matawalle ya iso Gusau ziyarar aiki

Da Ɗumi-Ɗumi: A karon farko Matawalle ya iso Gusau ziyarar aiki

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau A karon farko tun bayan zamansa Ƙaramin Ministan tsaro, tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Hon. Bello Muhammad Matawalle ya shigo Gusau babban birnin Jihar Zamfara a yau Juma'a domin ziyarar aiki. Blueprint Manhaja ta tattaro cewa Ministan zai gana da masu ruwa da tsaki da ‘ya’yan jam’iyyar APC a lokacin ziyarar. Ana kuma sa ran Ministan zai ziyarci mahaifar sa Maradun hedikwatar ƙaramar hukumar Maradun a yayin ziyarar. Wakilinmu ya ruwaito cewa ɗaruruwan magoya bayan jam’iyyar APC ne suka yi dandazo a gidan Ministan domin nuna goyon baya kan ziyarar tasa. Cikakken rahoto na tafe…
Read More

Majalisa za ta yi karatu na biyu ga kasafin 2025 sa’o’i 24 bayan Tinubu ya gabatar da shi

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun ɗage zama game da karatun ne zuwa ranar Talata, 14 ga watan Janairu, 2025 ga kasafin tiriliyan N49.7 da Shugaba Tinubu ya gabatar musuva ranar Laraba. Kasafin ya tsallake karatu na farko ne Majalisar Dattawa bayan muhawara da aka gudanar ƙarƙashin jagoran sanatoci, Sanata Michael Opeyemi Bamidele da gudunmawar wasu guda 42. Daga cikin abin da rabon kasafin ya ƙunsa akwai tiriliyan N4.4 ga harkokin gwamnati, sai N16.3tn na harkokin bashi, da na kashe-kashe tiriliyan N14.1; sai na gyare-gyaren kadarorin gwamnati 14.8 da sauran su. An dai tsara kasafin ne…
Read More

Wajibi ne a kula da damuwar mutane kan ƙudirin gyaran haraji – Shekarau

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma shugaban ƙungiyar ƴan demokraɗiyya ta Arewa (LND), Sanata Ibrahim Shekarau ya nuna muhimmancin kulawa da damuwar al'umma kan ƙudirin dokar gyaran haraji da Shugaba Tinubu ya gabatar wa majalisa. Shekarau ya bayyana hakan ne cikin rahoton kwamitin ƙungiyar game da ƙudirin wanda a yanzu ya ke hali na tantance wa a majalisa. Lamarin ƙudirin harajin ya haifar da cecekuce acikin al'umma musamman gwamnoni da wasu manyan Arewa waɗanda ke neman a sake nazari game da shi. Makonni biyu da suka gabata ne LND ta samar da kwamiti da zai yi nazari…
Read More

Cin zarafi a kafar sadarwa babban laifi ne – Kakakin ƴan sanda

Daga BELLO A. BABAJI Olumuyiwa Adejobi, Kakakin rundunar ƴan sanda ya ce cin zarafi da ake yi wa waɗansu a kafar sadarwa babban laifi ne a ƙarƙashin dokar ƙasa. A cikin wani rubutu da ya wallafa a shafin X, Adejobi ya bayyana irin aikin a matsayin cin zarafi ta yanar gizo wanda ba za a amince da shi a matsayin bayyana ra'ayi ba. Ya ce cin zarafi a kafar sadarwa bai cikin ƴancin Ɗan-adam da dokar ƙasa ta sahale wa al'umma, saidai abu ne da ke zama aibu ga wanda aka yi wa. Don haka ne ya yi kira ga…
Read More

Tinubu ya umarci a binciki iftila’in da ya sabbaba rasa rayuka a filin shaƙatawa na Ibadan

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Tinubu ya bayyana alhini game da mummunan al'amarin da ya faru a wajen shaƙatawa na yara a Ibadan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da raunata wasu masu yawa. Tinubu ya umarci hukumomin dake da alhakin binciken da su binciki musabbabin faruwar lamarin, kamar yadda Kakakinsa, Bayo Onanuga ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis. Shugaban ƙasar ya ce yana da muhimmanci a gano sakaci ne ya haifar da hakan ko kuma ganganci, ya na mai nuna muhimmancin tabbatar da adalci. Ya kuma nemi Gwamnatin Jihar Oyo…
Read More

Filin da aka ƙwace a Abuja ba na Buhari ba ne – Garba Shehu

Daga BELLO A. BABAJI Garba Shehu, Kakakin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi tsokaci game da ƙwace fili da aka yi a Abuja wanda aka ce na tsohon shugaban ƙasar ne. Rahotonni sun bayyana yadda Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ƙwace takardun wasu filaye da adadinsu ya kai guda 762 a yankin Maitama dake babban birnin bisa rashin cike ƙa'idodi. Waɗanda lamarin ƙwace takardun na 'CofO' ya shafa sun haɗa da na Gidauniyar tsohon shugaban ƙasa Buhari; tsohon Alƙalin Alƙalai, Walter Onnoghen; Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas; Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da matarsa Regina; Gwamnan Kaduna, Uba Sani…
Read More
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane sama da 40 a Maru ta Jihar Zamfara cikin makonni biyu

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane sama da 40 a Maru ta Jihar Zamfara cikin makonni biyu

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau  Wasu gungun ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da mutane aƙalla 40 a garin Maru hedikwatar ƙaramar hukumar Maru a hare-hare daban-daban na tsawon makonni biyu da suka gabata ga al’ummar Maru.  Mazaunin yankin Malam Ibrahim Sama'ila ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho a ranar Laraba da ta gabata.  A cewarsa, ‘yan bindigar sun shiga garin sau biyu cikin makonni biyu a yayin farmakin.  "A makon da ya gabata ne 'yan bindigar suka dira garinmu suka fara bi gida-gida suna bincike  tare da yin garkuwa da mutane bakwai, kawo ya zuwa yanzu mutanen mu arba'in…
Read More
Har yanzu Lakurawa na cigaba da zama a Kebbi  

Har yanzu Lakurawa na cigaba da zama a Kebbi  

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi  Tun lokacin da Lakurawa suka yi wa waɗansu mutane goma sha bakwai kisan gilla a garin Mera da ke ƙaramar Hukumar mulki ta Augie watanni biyu da suka wuce ne, al'ummar yankin suka sha alwashin bai wa garuruwansu tsaro ta hanyar amfani da 'yan banga da mafarauta da sauran matasa masu jini a jika. Ganin haka ne ya sa Lakurawan suka tattara nasu ya nasu suka bar sansanoni uku da suka kafa a ƙaramar hukumar mulki ta Augie da ke iyaka da jihar Sakkwato suka koma yankin Sakkwato, sai dai ba su bar kawo samame…
Read More