Labarai

Yadda gobara ta laƙume asibitin Jega

Yadda gobara ta laƙume asibitin Jega

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi  Rahotanni daga ƙaramar Hukumar mulki ta Jega da ke Jihar Kebbi sun bayyana tashin wata mummunar gobara da ta yi sanadiyyar ƙonewar wata asibiti safiyar Talatar da ta gabata. Gobarar da har yanzu ba a gano musabbabin tashin ta ba, ta ƙone sashen aikin gaggawa da hatsari tare da dukkanin kayan aikin da ke ciki. Ta ƙone babban ɗakin shan magani na asibitin ƙurmus, inda kayan duk da ke cikin ɗakunan da suka haɗa da kayan gwaje-gwaje da na ayyukan gaggawa da sauran magunguna suka ƙone. Wani ma'aikaci a asibitin da bai so a bayyana…
Read More
Hukumar Kwastom ta sanar da cire harajin VAT a iskar gas ɗin dafa abinci da CNG

Hukumar Kwastom ta sanar da cire harajin VAT a iskar gas ɗin dafa abinci da CNG

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Kwastom ta Nijeriya (NCS) a ranar Laraba ta sanar da cire ƙarin harajin ɓAT a kan iskar gas ɗin dafa abinci wato Liƙuefied Petroleum Gas (LPG), da kuma iskar iskar gas na CNG. Har ila yau, ta sanar da harajin sifili cikin ɗari na shigo da kayayyakin. Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abdullahi Maiwada ne ya bayyana hakan a wata sanarwa. Sanarwar ta ce: “A bisa la’akari da ƙudirin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na inganta yanayin zuba jari a Nijeriya da kuma ƙara yawan amfani da iskar gas a cikin gida,…
Read More
Farashin man fetur ya sauka zuwa N970 kan kowacce lita, inji ‘yan kasuwa

Farashin man fetur ya sauka zuwa N970 kan kowacce lita, inji ‘yan kasuwa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A wani mataki na samun daidaito a ɓangaren man fetur, ƙungiyar Manyan Dillalan Man Fetur na Nijeriya, MEMAN ta bayyana cewa farashin man fetur ya sauka zuwa N970 a watan Disamba 2024, daga N971 kowace lita. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da farashin ɗanyen mai ya yi ƙasa da dala 73.77 a ranar Laraba, daga dala 74 a makon jiya. Sai dai a cikin sanarwar ta rahoton makamashin yau da kullum da Blueprint Manhaja ta samu, ta bayyana cewa sabon farashin ya dogara ne akan Naira 1,533.57/$ da dala 73.91 kan…
Read More
Babu gaskiya a kasafin kuɗin Tinubu na 2025 – PDP

Babu gaskiya a kasafin kuɗin Tinubu na 2025 – PDP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam'iyyar PDP ta soki kasafin kuɗin da Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya gabatar wa majalisar dokokin ƙasar, wanda ta bayyana a matsayin wani abu da ''ba zai yiwu ba'' kuma wanda ''babu gaskiya a ciki''. Sakataren yaɗa labaran PDP Debo Ologunagba, a cikin wata sanarwa a kan kasafin kuɗin, ya ce kasafin kuɗin ya shafi abubuwan da za su ƙara jefa jama'a cikin ƙangin talauci da kuma matsalar tsaro. Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin na 2025, na naira tiriliyan 49.7 ga majalisar dokokin Nijeriya, inda ya sha alwashin bayar da fifiko ga ɓangaren…
Read More
Kasafin 2024 zai kai watan Yunin 2025 – Akpabio

Kasafin 2024 zai kai watan Yunin 2025 – Akpabio

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa wa’adin kasafin kuɗin shekarar 2024 kai har zuwa ranar 25 ga watan Yuni, 2025. Ya bayyana haka ne a ranar Laraba, yayin da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 a zauren Majalisar Dokokin ƙasa. Akpabio, ya bayyana cewa kasafin 2024 ya samu nasarar kashi 50 na ayyukan manyan gine-gine da kuma kashi 48 na kuɗin tafiyar da gwamnati. Shugaba Tinubu, ya gabatar da kasafin kuɗi na Naira tiriliyan 47.9 na shekarar 2025 domin tantancewa da yin nazari.
Read More
Gwamnatin Tarayya za ta samar da bankin matasa

Gwamnatin Tarayya za ta samar da bankin matasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kafa bankin matasa don bayar da lamuni, tallafi da sauran kayayyakin kuɗi don tallafa wa matasa masu sana’o’in dogaro da kai wajen bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire da samar da ayyukan yi. Ministan ci gaban matasa Mista Ayodele Olawande ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Talata a Abuja. A cewar ministan, ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an samar da tsarin samar da ayyukan yi ga matasan Nijeriya domin magance matsalar rashin aikin yi a ƙasar. “Kafa bankin matasa yana da fa’ida da dama ga matasa…
Read More
Ana fargabar mutuwar yara da dama a turmutsitsi a Ibadan

Ana fargabar mutuwar yara da dama a turmutsitsi a Ibadan

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ana fargabar cewa yara da yawa ne suka mutu sakamakon turmutsitsin da  aka yi a wani dandalin wajen wasan yara mai zaman kansa a makarantar Basorun Islamic High School da ke Ibadan a jihar Oyo. Manhaja ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Laraba. Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Prince Dotun Oyelade, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya tabbatar wa jama’a cewa gwamnatin jihar ta ɗauki matakin gaggawa da tura jami’an agaji domin taimakawa waɗanda abin ya shafa. Ya kuma tabbatar da cewa an kai yaran da…
Read More
Manufofina sun fara farfaɗo da tattalin arziƙin Nijeriya — Tinubu

Manufofina sun fara farfaɗo da tattalin arziƙin Nijeriya — Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce tattalin arziƙin Nijeriya na samun farfaɗowa sakamakon manufofin gwamnatinsa. Tinubu, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 a zauren majalisar dokoki ta ƙasa. Ya ce gwamnatinsa tana ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arziƙi ta hanyar kashe kuɗaɗe a wuraren da suka dace ba tare da haifar da hauhawar farashi ba. “’Yan Nijeriya za su shaida an samu ci gaba a tattalin arziƙi kuma nan ba da jimawa ba abubuwa za su sake daidaita,” inji Tinubu. Hakazalika, ya jaddada cewa akwai alamu…
Read More
An samu cimma kashi 80 na yaƙi da garkuwa da mutane – Ribaɗu

An samu cimma kashi 80 na yaƙi da garkuwa da mutane – Ribaɗu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A ranar Alhamis ne mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Mallam Nuhu ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu sama nasara da kashi 80 cikin 100 a yaƙi da masu garkuwa da mutane. Ya ce, an samu nasarar ne sakamakon sadaukarwar da jami’an tsaro suka yi da kuma aiki mai inganci da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ke yi. Ribadu ya bayyana haka ne a wajen ƙaddamar da cibiyar yaƙi da ta’addanci ta ƙasa (NCTC) da 'Multi-Agency Kidnap Fusion Cell' (MAAKFC). Hukumar ta NSA ta ce,…
Read More
Majalisar Dattawa ta buƙaci a haramta amfani da kuɗaɗen waje a mu’amalar cikin gida

Majalisar Dattawa ta buƙaci a haramta amfani da kuɗaɗen waje a mu’amalar cikin gida

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Majalisar Dattawa, a ranar Talata, ta amince da wani ƙudirin doka na haramta amfani da kuɗaɗen waje wajen hada-hadar kasuwanci a Nijeriya. Dokar da aka gabatar, da nufin tabbatar da cewa ana gudanar da duk wasu mu'amalar kuɗaɗe da suka haɗa da albashi a cikin naira don neman kawar da ayyukan nuna wariya da kuma ƙarfafa kwarin gwiwa kan kuɗaɗen cikin gida. Wannan ya haɗa da sanya wajabta fitar da kaya zuwa ƙasashen waje da za a biya a naira. ƙudirin ya yi wa laƙabi da “ƙudirin Dokar Kuɗi Na Babban Bankin Nijeriya, 2007, Lamba 7,…
Read More