Labarai

Jamhuriyar Nijar ta kori ‘yan Nijeriya 310

Jamhuriyar Nijar ta kori ‘yan Nijeriya 310

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Nijeriya da haɗin gwiwar Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Gijira ta Nijeriya sun karɓi ’yan Nijeriya guda 310 da da aka koro su daga Jamhuriyar Nijar ranar Litinin. An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka yaɗa a shafin Tiwita ranar Laraba. Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa reshen jihar Kano, ta halarci bikin karɓar ‘yan gudun hijira ɗari uku da goma (310) tare da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta ƙasa da ƙasa da hukumar kula da ‘yan gudun…
Read More
Majalisar Dokokin Kano za ta ƙarfafa dangantaka da gidan talibijin na NTA

Majalisar Dokokin Kano za ta ƙarfafa dangantaka da gidan talibijin na NTA

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore ya bayyana aniyarsa na inganta haɗin gwiwar da ake yi da hukumar gidan talabijin ta Nijeriya (NTA) domin ƙara danƙon zumunci. A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Kamaluddeen Sani Shawai ya fitar a ranar Laraba ya yabawa NTA bisa rawar da take takawa wajen samar da sahihan bayanai akan lokaci da suka yaɗu a faɗin Nijeriya. An amince da NTA saboda gagarumin tasirin da take da shi wajen tsara tunanin 'yan Nijeriya da kuma bayyana kyawawan al'amuran al'umma ga masu sauraron duniya.…
Read More

Ƙaramar Hukumar Kaugama ta Jigawa za ta kewaye maƙabartu

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Ƙaramar hukumar Kaugama dake Jihar Jigawa, ta shirya tsaf domin inganta harkar Noma a jihar. Shugaban ƙaramar hukumar, Alh Usman Masaki D Sule ya tabbatar wa manema labarai a Dutse ce inda ya ce ƙaramar hukumar ta ware N5,700,000,000 domin yi wa al'ummar yankin ayyukan raya ƙasa. Ya ce ƙaramar hukumar za ta kashe kuɗaɗen ne wadda hakan yana cikin kasafin kuɗinta shekarar 2025. Masaki ya ce za su bada fifiko ne wajen harkar kiwon lafiya, noma da inganta harkar ilimi. Ya ƙara da cewa ƙaramar hukumar za ta tallafa wa Marasa lafiya Mata…
Read More
Majalisar Dokokin Kano ta tantance mutum bakwai domin naɗa su a matsayin kwamishinoni

Majalisar Dokokin Kano ta tantance mutum bakwai domin naɗa su a matsayin kwamishinoni

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ce ta amince da sunayen mutum bakwai da gwamnan Kano Injiya Abba Kabir Yusuf ya aike domin tantancewa ya naɗa su a matsayin kwamishinoni, Kuma 'yan majalisar zartarwar Jihar Kano. Shugaban masu rinjaye na Majalisar Lawan Hussaini cibiyar 'Yan Gurasa ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala tantance mutanen bakwai. In da ya ce mutanen da aka zabo nagartattu ne ƙwararru. "Ƙwararru ne kuma matasa masu ƙwari kuma matasa masu niyyar yin aiki, kun ga yadda akai masu tambayoyi Kuma suka amsa yadda ya kamata. Musamman akan wutar lantarki…
Read More
Kamfanin Shell zai zuba jarin Dala biliyan biyar a haƙar man teku a Nijeriya – Tinubu

Kamfanin Shell zai zuba jarin Dala biliyan biyar a haƙar man teku a Nijeriya – Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa kan yadda kamfanin haƙar mai na Shell da abokan hulɗarsa suka amince da zuba jarin Dala biliyan biyar kan aikin haƙo ɗanyen mai a cikin teku. A rahoton da Blueprint Manhaja ta samu, aikin shi ne babban aikin haƙo mai daga teku karo na farko tsawon shekaru masu yawa a Najeriya, sannan zai taimaka wa tsare-tsare da manufofin shugaban ƙasa na jawo hankalin masu zuba jari a fannin mai da iskar gas. Aikin mai suna ‘Bonga North Oilfield’ zai laƙume Dala biliyan biyar, ana kuma sa ran zai riƙa samar da…
Read More
Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanya hannu a kasafin kuɗi na 2025

Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanya hannu a kasafin kuɗi na 2025

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya sanya hannu a kasafin kuɗi na Naira biliyan 692. Tun farko gwamnan ya miƙa wa Majalisar kasafin kuɗi na Naira biliyan 682 amma bayan da majalisar ta yi nazari da gyare-gyare ta ƙara Naira biliyan 10. A bayanin sa gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa kashi 77% na kasafin kuɗin zai tafi ne wajan mayan ayyuka inda fanin ilimi yafi samun kaso mai tsoka. Ya cigaba da cewa kasafin kudin mai suna "gina makomar alumma" zai maida hankali wajen harkar ilimi,noma da kiwon lafiya. Malam Dikko Raɗɗa sai…
Read More
Al’ummar Bichi na buƙatar a gina masu jami’a

Al’ummar Bichi na buƙatar a gina masu jami’a

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ƙungiyar Cigaban Matasan Bichi wato Bichi youth development Forum ƙarƙashin gamayyar ƙungiyoyin matasa da cigaban ƙaramar hukumar Bichi, sun buƙaci gwamnatin Kano da ta samar masu da jami'a domin cigaban ilimi a wannan yanki, Ƙungiyar ta yi wannan Kiran ne yayin taron jin ra’ayin jama'a da aka gudanar a majalisar dokokin jihar Kano akan kasafin kuɗi na 2024/2025, wanda gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya miƙa wa majalisa. Gazali Abubakar Isah Bichi (Gaza) wanda shi ne ya wakilci al'ummar ta Bichi ya bayyana yankin a matsayin matattara ta ilimi, inda ya ce "Babban giɓin da…
Read More

Kamfanin Ɗangote ya rage farashin fetur zuwa N899

Daga BELLO A. BABAJI Matatar Man fetur ta kamfanin Ɗangote, ta sanar da rage farashin litar fetur zuwa N899.5. Jami'in Labaran kamfanin, Anthony Chiejina ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar ranar Alhamis. Ya ce hakan na zuwa ne a lokacin da al'ummar Nijeriya ke shirin gudanar da bukukuwan ƙarshen shekara don sauƙaƙe musu tsardar rayuwa da ake fama da ita a ƙasar. A watan Nuwamba ne kamfanin ya rage farashin zuwa N970 inda a yanzu kuma dawo da shi N899.50. Ya kuma sanar da cewa kamfanin ya bada dama ta musamman ga kwastomominsa na…
Read More

Antoni Janar zai gana da Majalisar Dattawa kan ƙudirin gyaran haraji

Daga BELLO A. BABAJI A yau ne Antoni-Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi zai tattauna da Majalisar Dattawa kan batun kuɗirin gyaran haraji da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar wa majalisa. Bayan cecekuce da aka samu ne game da ƙudirin kan wasu saɗarori da al'umma ke ganin ka iya haifar da matsaloli ga harkokisu na yau da kullum, sai Shugaba Tinubu ya umarci Antonin da ya gana da majalisa don samun maslaha game da batun. A gefe guda kuma, Majalisar ta shirya wani kwamiti dazai gana da ministan shari'ar. Shugaban kwamitin, Sanata Abba Moro ya bayyana wa manema…
Read More

Jami’an DSS sun kama shugaban NBS, an rufe shafin hukumar

Daga BELLO A. BABAJI Jami'an tsaron ƴan sandan farin kaya (DSS), sun yi ram da shugaban Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), Semiu Adeyemi Adeniran a ofishinsa na hukumar. Jaridar News Point Nigeria ta ruwaito cewa, an kama shugaban hukumar ne kan alaƙa da batun sata da wani rahoton tsaro da hukumar ta fitar a ranar Talata. A baya ne NBS ta fitar da rahoton cewa ƴan Nijeriya sun biya kuɗin fansa da adadinsa ya kai Naira tiriliyan 2.23 daga watan Mayun 2023 zuwa Afrilun 2024. Rahoton ya bayyana cewa waɗannan kuɗaɗe ne da magidanta suka biya sakamakon ayyukan garkuwa da…
Read More