Labarai

Ɓarayi sun datse adireshin yanar gizo na Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa ta sanar da cewa ɓarayi a intanet sun datse adireshinta na yanar gizo. A ranar Laraba ne hukumar ta wallafa hakan a shafinta na X. Ta yi kira ga al'umma da ƙaurace wa duk wani bayani da za a yaɗa a ƙafar daga yanzu har zuwa lokacin da za a kammala aikin gyaran adireshin. A halin yanzu jami'an gudanarwa suna ƙoƙari wajen ganin shafin ya koma aiki yadda aka saba kamar yadda suka tabbatar a sanarwar.
Read More
Su waye abokan ‘ya’yanmu

Su waye abokan ‘ya’yanmu

Daga AISHA ASAS  Abu Musa Al’ash’ari ya rawaito hadisi daga manzon rahman (S.A.W), cewa, Annabin Allah (SAW) ya ce, "Misalin aboki na gari da abokin banza, kamar misalin mai siyar da (ko daukar) turare ne, da mai hura zuga-zugi (kira), mai daukar turare ko dai ya shafa maka ko ka sayi turare a wurinsa ko kuma ka ji ƙamshi mai daɗi a wurinsa, mai hura zuga- zugi kuma ko ya ƙona maka kaya ko ka ji wari a wurinsa." Wannan hadisi ne da Bukhari ya ruwaito.  Kamar yadda bahaushe ke cewa, zama da maɗaukin kanwa, shi ke kawo farin kai.…
Read More
Kirsimeti: ‘Yan sanda sun tsaurara tsaro ga Kiristoci a Zamfara

Kirsimeti: ‘Yan sanda sun tsaurara tsaro ga Kiristoci a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta ce ta tanadi isassun jami’an tsaro a faɗin ƙananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara, domin su tabbatar da gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin lumana a tsakanin mabiya addinin Kirista. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ASP Yazid Abubakar, ya bayyana haka a wata hira da ya yi da Blueprint ta wayar tarho a yau Laraba. A cewar sa tuni rundunar ta kammala dukkan shirye-shirye na tabbatar da cewa dukkan majami’u sun samu cikakken tsaro don baiwa Kiristoci damar gudanar da bukukuwansu na Kirsimeti cikin lumana. "Mun shirya…
Read More

Tsaro, manyan ayyuka da Ilimi ke kan gaba a kasafin 2025 da Tinubu ya gabatar wa majalisa

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Laraba ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 na Naira tiriliyan 47.9 ga ƴan majalisu a matakin tarayya. Shugaba Tinubu ya lissafo ɓangarori daban-daban inda aka ware wa Tsaro tiriliyan N4.91, sai na Manyan ayyuka da ya samu N4.06tn, sannan ɓangaren Lafiya wanda ya samu N2.4tn, sai kuma N3.5tn ga Ilimi. Ya ce batun abinci kuwa, ɓangare ne da bai buƙatar tattaunawa, ya na mai tabbatar da cewa gwamnatinsa ta na ɗaukar matakan da suka dace wajen ganin kowane ɗan Nijeriya bai kwana da yunwa. Shugaban ƙasar ya ce…
Read More

Majalisar Ɗinkin Duniya ta wayar da kan masu buƙata ta musamman kan cin moriyar kwangilolinta

Daga BELLO A. BABAJI Shirin samar da abinci na duniya ƙarƙashin Majalissar Ɗinkin Duniya (MƊD) ya ƙaddamar da shirin bunƙasa damammaki ga sana'o'in nakasassu da bada kwangilolinta gare su. Shugaban shirin, Daniel Kuhe ya sanar da hakan yayin wani taron gabatar da shirin wayar da kai ga tawagar masu buƙata ta musamman da aka yi a Abuja. Kuhe ya bayyana buƙatar haɗin-gwiwa tsakanin hukumomin MƊD wajen samar da damammaki da daidaito acikin al'umma. Ya ce yunƙurin zai taimaka wajen faɗaɗa hanyoyin damawa da ɓangarori daban-daban yayin ayyukan kwangilolin MƊD, ya na mai cewa nakasa ba hujja ba ce ta nuna…
Read More
Gwamnan Kaduna ya mayar wa iyalin Abacha filaye da gwamnati El-Rufai ta ƙwace

Gwamnan Kaduna ya mayar wa iyalin Abacha filaye da gwamnati El-Rufai ta ƙwace

Daga USMAN KAROFI Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya mayar da filaye guda biyu da ke cikin birnin Kaduna ga iyalin tsohon Shugaban ƙasa, Janar Sani Abacha, shekaru biyu bayan da tsohon gwamna Nasir El-Rufa’i ya ƙwace su. Filayen da aka mayar sun haɗa da ɗaya da ke No. 9 Abakpa GRA, Kaduna, mai girman mita 2,284, wanda ke ɗauke da takardar mallakar gwamnatin Jihar Kaduna mai lamba 30575, da kuma wani filin da ke No. 1 Degel Road, Ungwan Rimi GRA, Kaduna, mai girman murabba'in mita 3,705, da ke ɗauke da takardar mallakar gwamnati mai lamba 11458. Lauyan iyalin…
Read More

NIMET ta yi hasashen samuwar ƙura da hazo na kwana uku daga Laraba

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar kula da Yanayi, NIMET ta yi hasashen samun ƙura da hazo daga ranar Laraba zuwa Juma'a a Nijeriya. Hasashen da hukumar ta yi a ranar Talata ya nuna cewa za a samu matsakaicin hazo da ƙura a ranar Laraba na tsawon hangen kilomita 2 zuwa 5 a arewacin Nijeriya. Haka ma a yankin Arewa ta Tsakiya da kudanci, inda ta ce za a samu hazo sakamakon matakin yanayin sanyi musamman a yankuna masu koguna. NIMET ta yi kira ga al'umma da su ɗauki matakan kariya daga ƙurar wadda ka iya haddasa yaɗuwar cutuka musamman masu…
Read More
Buhari shugaba ne mai tausayin talakawa – Garba Shehu

Buhari shugaba ne mai tausayin talakawa – Garba Shehu

Daga UMAR GARBA a Katsina Albarkacin zagayowar ranar haihuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Mallam Garba Shehu wato kakakin tsohon shugaban ƙasar, ya bayyana Buhari a matsayin shugaba mai gaskiya da riƙon amana gami da tausayin talakawa. Garba Shehu, ya bayyana hakan a shafinsa na X, a ranar da tsohon shugaban yake murnar cika shekara 82 a duniya. "Buhari shugaba ne daban, wanda yake damuwa da damuwar talakawa da masu rauni, sannan yake dagewa wajen inganta rayuwar talakawa da fitar da su daga cikin ƙunci." Inji kakakin. Garba Shehu ya ƙara da cewa siyasa da cin hanci da rashawa suna…
Read More

Gwamnatinmu ta yi ƙoƙarin toshe hanyoyin zurarewar kuɗi a Kano – Gwamna Abba

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya ce gwamnatinsa ta yi ƙoƙari wajen ganin ta toshe hanyoyin zurarewar kuɗi mai yawa dan inganta hanyoyin kuɗin shiga a jihar. Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen taron tunawa da ranar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Duniya da Hukumar karɓar Ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da Cin hanci da Rashawa ta jihar ta shirya. Gwamnan ya ce dole ne ya yi alfahari da hukumar ƙarƙashin jagorancin Barista Muhuyi Magaji Rimin-Gado bisa ƙoƙarinsa na aiki tuƙuru wajen aiki da masu cin hanci da rashawa a Kano. ''A…
Read More

Majalisar Dokokin Katsina ta amince da kasafin kuɗin 2025 da Gwamna Raɗɗa ya gabatar mata

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Majalisar ta amince da kasafin kudin ne a zaman majalisar, ƙarƙashin Jagorancin Kakakinta, Hon. Nasir Yahaya wanda adadinsa Naira biliyan 692 da Gwamnan Jihar, Dikko Raɗɗaya gabatar. Amincewa da kasafin kuɗin na 2025 ya biyo bayan karanta rahoton kare shi ne da shugaban kwamitin, Hon. Lawal H. Yaro Away ya gabatar ya kuma karanta. Yayin tattauna batun, majalisar ta yaba wa gwamnan inda ta ce a tarihi ba a taɓa kasafin kudi irin wannan ba, wanda aka bai wa manyan ayyuka kaso mai tsoka da za su taɓa rayukan talakawa kai tsaye. Ƙudirin farko shi…
Read More