Labarai

Da Ɗumi-Ɗumi: Vinicius Junior ya lashe kyautar ɗan wasan shekara na FIFA

Da Ɗumi-Ɗumi: Vinicius Junior ya lashe kyautar ɗan wasan shekara na FIFA

Ɗan wasan gaba na Real Madrid da Brazil, Vinicius Jr, ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon maza na duniya a gasar FIFA Best Awards. Vinicius, mai shekaru 24, ya karɓi wannan lambar yabo ne a wani biki da aka gudanar a birnin Doha, Qatar. Tun da farko, Vinicius da kulob ɗinsa sun ƙaurace wa bikin Ballon d'Or na baya-bayan nan bayan da ya sha ƙasa ga ɗan wasan Manchester City, Rodri. Sai dai wannan lambar yabo ta FIFA Best ta zo masa a matsayin gagarumar nasara, bayan rawar gani da ya taka a kakar wasa ta 2023-24, inda ya zura…
Read More
Hukumar NSCDC ta Zamfara ta kama wani ɗan Kano bisa laifin sata

Hukumar NSCDC ta Zamfara ta kama wani ɗan Kano bisa laifin sata

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Rundunar ‘yan sandan farin kaya ta Nijeriya, sibil difens, reshen Jihar Zamfara, ta cafke wani mutum mai suna Muhammad Dauda Ismail daga ƙaramar hukumar Dala ta jihar Kano, da ake zargi da laifin sata da zamba cikin aminci. Kwamandan rundunar a jihar, Muhammad Sani Mustapha ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai a Gusau yau Talata. “ Alkasim Muhammad Kabir ɗan shekara 33 dan asalin Kano, wanda aka yi masa sata, a ranar Alhamis, 12 ga Disamba, 2024 ya kawo rahoton ɓacewar wata mota ƙirar Mercedes-Benz…
Read More
HOTUNA: Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Ghana mai jiran gado ya ziyarci Tinubu a Abuja

HOTUNA: Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Ghana mai jiran gado ya ziyarci Tinubu a Abuja

Shugaban Ghana mai jiran gado, John Dramani Mahama, ya kai ziyara ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa. Wannan ziyara ta samu tabbaci ne ta hannun mataimakin shugaba Tinubu na musamman kan kafofin sada zumunta, Dada Olusegun, wanda ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata. A cewarsa, "Shugaban Ghana mai jiran gado, H.E John Dramani Mahama, ya kai ziyara ta girmamawa ga Shugaba Tinubu a fadarsa, Villa ta Ƙasa, jiya." Wannan ziyara ta biyo bayan saƙon taya murna da Shugaba Tinubu ya aike wa Mahama bayan nasarar da ya samu a zaɓen Ghana da aka…
Read More
Majalisar Wakilai ta yi sammacin shugabannin sojoji bisa zargin aiki ba bisa ƙa’ida ba a Nasarawa

Majalisar Wakilai ta yi sammacin shugabannin sojoji bisa zargin aiki ba bisa ƙa’ida ba a Nasarawa

Majalisar Wakilai ta Nijeriya ta yanke shawarar gayyatar babban hafsan tsaron Ƙasar, Shugaban Sojojin Ƙasa da kuma kwamandan bataliya ta 177, saboda zargin kamawa da tsare wani shugaban al'umma ba bisa ƙa’ida ba a Jihar Nasarawa. Ɗan majalisa Mansur Soro ne ya gabatar da ƙudirin a zaman majalisa na ranar Talata, inda ya bayyana cewa a ranar 9 ga Disamba, 2024, sojojin bataliya ta 177 sun kama Bello Badejo a garin Maliya na jihar Nasarawa ba tare da an yi masa wata takardar gayyata ko umarnin kotu ba. Ya ƙara da cewa, har zuwa mako guda bayan kamun, har yanzu…
Read More
Turji na barazanar kashe mutanen da ya yi garkuwa da su bayan sojoji sun kama na hannun damansa

Turji na barazanar kashe mutanen da ya yi garkuwa da su bayan sojoji sun kama na hannun damansa

Daga UMAR GARBA a Katsina Ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Turji ya sha alwashin kashe mutanen da yake garkuwa da su a halin yanzu, matuƙar gwamnatin Najeriya bata saki abokin ta'addancinsa ba wato Baƙo Wurgi. Blueprint Manhaja ta rawaito cewa rundunar sojin Najeriya ta ɗaya ta cafke ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Baƙo Wurgi a Jihar Zamfara. Ana zargin Wurgi da hannu a kisan Sarkin Gobir na Sabon Birni a Jihar Sakkwato, Alhaji Isa Mohammed Bawa. Rahotanni sun bayyana cewa ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji, tuni ya fara tuntuɓar dagatai da ke Shinkafi a Jihar Zamfara, inda ya yi barazanar kai…
Read More

Gwamnan Zamfara ya ƙaddamar da aikin titi a Ribas da yaba wa Gwamna Fubara

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jinjina wa Gwamna Siminalayi Fubara kan ƙoƙarinsa na samar da ayyukan ci-gaba a Jihar Ribas. Kasancewar sa babban baƙo a yayin buɗe ayyukan titin Opobo da gadoji a ƙaramar hukumar Opobo/Nkoro a ranar Litinin, Gwamna Lawal ya yaba da hoɓɓasa da gwamnan na Ribas ke yi wa al'ummar jihar. Ya kuma yaba da ayyukan inganta harkokin tattalin arziƙi don amfanar da al'ummar jihar. Cikin wata takarda da Kakakin Gwamna Lawal, Sulaiman Bala Idris ya fitar, gwamnan ya ce samar da titina za su taimaka wa harkokin kasuwanci da faɗaɗa damammaki…
Read More

Lukman Ademola ya zama gwarzon ɗan wasan Afrika na 2024

Daga BELLO A. BABAJI Ɗan wasan Super Eagles, Ademola Lukman ya lashe kyautar CAF ta shekarar 2024. An gudanar da taron bada lambobin yabon ne a ranar Litinin, a birnin Marrakech na ƙasar Morocco. Lukman ya nuna bajinta matuƙa wa ƙungiyarsa ta Atalanta dake ƙasar Italiya a kakar Bara inda ya taimaka mata ta lashe kofin gasar Europa. A wasan ƙarshe ne ya zura ƙwallaye uku a raga. Ya kuma taka rawar gani wa Super Eagles a gasar kofin ƙasashen Afirka, wato AFCON ta 2024.
Read More

An sauya sunan Jami’ar Abuja zuwa Jami’ar Yakubu Gowon

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta sanar da sauya sunan Jami'ar Abuja (UniAbuja) zuwa Jami'ar Yakubu Gowon (Yakubu Gowon University). Ministan Labarai, Mohammed Idris ya bayyana hakan ga manema labarai na Fadar shugaban ƙasa bayan zaman Majalisar Zartarwa (FEC) da aka gudanar ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, a ranar Litinin. An ƙaddamar da hakan ne don karrama tsohon shugaban mulkin soji na Nijeriya, Janar Yakubu Gowon mai ritaya, wanda a kwanan nan ne ya yi bikin cika shekaru 90 a duniya. Ministan ya ce za su miƙa buƙatar sauya sunan ga Majalisa domin tabbatarwa. Da farko, Blueprint ta ruwaito…
Read More
MAKAMASHI: Waiwaye adon tafiya

MAKAMASHI: Waiwaye adon tafiya

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI  Masu hikima na cewa, “waiwaye adon tafiya”, hakan ya biyo bayan rashin wutar Lantarki na tsawon kwanki kusan goma sha daya a dukkan arewacin Nigeria. Zantuka ta ko ina kamar ruwan dare daga bakuna daban-daban, wasu masu ma’an, wasu ban haushi, wasu kuma masu ban dariya, kuma shifcin gizo tattare da wawta da jahilci. Wannan ya sa muka yanke shawara da mu yi waiwaye duk da cewa, a wannan fili mun taɓa  ambatawa,  mene ne makamashi? Yaya tarihin makamashi ya ke a wannan ƙasa ta Nijeriya? Tarihin ya nuna cewa, ƙasar Kano ce, ƙasar farko…
Read More
Sojoji sun kama ƙasurgumin ɗan bindigar da ya kashe Sarkin Gobir

Sojoji sun kama ƙasurgumin ɗan bindigar da ya kashe Sarkin Gobir

Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar sojin Nijeriya ta ɗaya ta cafke ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Baƙo Wurgi wanda aka fi sani da Baka Na Garba a jihar Zamfara. Ana zargin Wurgi da hannu a kisan Sarkin Gobir na Sabon Birni a Jihar Sakkwato, Alhaji Isa Mohammed Bawa. Rundunar ta samu nasarar kama shugaban 'yan bindingar bayan wani farmaki da ta kai masa a ranar 14 ga watan Disamba da misalin ƙarfe 10 na dare a garin Shinkafi da ke jihar Zamfara, biyo bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa Wurgi na samun kulawa a wani asibiti da…
Read More