16
Dec
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya rantsar da Hon Abdulkadir Mamman Nasir a matsayin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar da masu ba gwamnan shawara guda uku . Hon Abdulkadir Nasir tsohon ɗan majalisar wakilai a tsakanin 2007 zuwa 2011 kuma ya riƙe shugabancin jam'iyyar APC na jihar Katsina. Kafin wannan muƙami shine babban daraktan na hukumar kula da noman rani a jihar,haka kuma ya riƙe muƙamin shugaban ƙaramar hukumar Malumfashi. Hon Nasir da aka fi sani da suna (Andaje) ya taɓa rike muƙamin mai ba gwamna shawara kan tallafawa masu ƙanana da matsaikaitan sana'o'i.…
