Labarai

Ƙaryata labarin garkuwa da mutane a Zamfara bai mana daɗi ba – Kwamared Halilu

Ƙaryata labarin garkuwa da mutane a Zamfara bai mana daɗi ba – Kwamared Halilu

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wani jigo a ƙaramar hukumar Maradun ta Jihar Zamfara, Kwamared Haliru Attahiru ya koka kan kalaman da gwamna Dauda Lawal na jihar yayi kan sace mutane 50 da aka yi kwanan nan, inda gwamnan ya fito tana mai cewar hakan bai faru ba. A baya dai gwamnan ya ƙaryata rahotannin garkuwa da mutanen Ƙauyen Kakindawa da wasu ‘yan bindiga suka yi a Ƙauyen da ke ƙarƙashin gundumar Gidan Goga a ƙaramar hukumar Maradun da wasu kafafen yaɗa labarai su ka yi. Attahiru a wata hira da manema labarai ya bayyana cewa kamata ya yi gwamna…
Read More

Ganduje na yunƙurin kama kakakin gwamnan Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Babban Daraktan yaɗa labarai da sadarwa na Gwamna Abba Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana yadda ya nemi mafaka a gidan gwamnatin Jihar Kano domin gudun kada jami’an ƴan sanda su kama shi. Da ya ke magana a ranar Asabar yayin taron ƙungiyar sadarwar matasa ta 'PR Nigeria' a Kano, Bature Dawakin Tofa ya yi ikirarin cewa kimanin jami’ai 40 daga tawagar Sufeto Janar na ƴan sanda (IGP) aka tura Kano kwanaki shida da suka gabata da nufin cafke shi. "Kwanaki biyar da suka gabata, ina gidan gwamnati kuma na kasa fitowa", inji shi.…
Read More

NNPCL ya rage farashin fetur a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI Kamfanin Man fetur na Ƙasa, NNPCL ya rage farashin litar fetur a gidajen mai dake birnin tarayya Abuja. Masu ababen hawa sun ce gidajen man sun rage farashin ne daga N1,060 zuwa 1,040 wanda hakan ya nuna an samu ragin Naira 20 a kowacce lita. Hakan na zuwa ne makonni uku dawo wa aiki da matatar Fatakwal ta yi bayan tsawon lokaci da rufe ta.
Read More
CCLM ta ƙaddamar da rabon kayan abinci da na karatu ga marayu a Sakkwato 

CCLM ta ƙaddamar da rabon kayan abinci da na karatu ga marayu a Sakkwato 

Daga MUKHTAR A. HALLIRU TAMBUWAL a Sokoto    Wata ƙungiya mai taimakawa mabuƙata da ake kira da Concerned Citizens of Likes Minds (CCLM) a turance, ta ƙaddamar da rabon tallafin kayan abinci da kayan karatu ga marayu da ɗalibai, 'yan gudun hijira da sauran mabuaata, a Jihar Sakkwato.  Ita dai CCLM ƙungiya ce mai rassan a dukkan faɗin Nijeriya har da Jihar Sakkwato, wacce jama'a da dama ke amfana da ita, sakamakon tallafin da take bayarwa. A cikin ayyukan jinƙai da ƙungiyar ta gudanar a Sakkwato har da rabon kayan abinci a gidan marayu da sansanin 'yan gudun hijira, tare da…
Read More
Jarman Sakkwato ya ɗauki nauyin kai marayu Umra

Jarman Sakkwato ya ɗauki nauyin kai marayu Umra

Daga MUKHTAR A. HALLIRU TAMBUWAL a Sakkwato  Rukuni na 4 daga cikin Rukunai 50 na marayun nan su 174 da aka ɗauko lokacin tsananin rikicin Boko Haram a jihohin Borno da Yobe, waɗanda fitaccen ɗan kasuwar nan mai taimakawa marayu wanda ake yi wa laƙabi da Uban Marayu Dr. Ummarun Kwabo yake ɗaukar nauyin kula da su ƙarƙashin kulawar Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Sakkwato, sun samu nasarar komawa gida, bayan da suka kammala aikin Umra da aka kai su.  Shugabar makarantar da ke kula da ilimantar da waɗannan yara marayu maza da mata Malama Adama Muhammad ta bayyana…
Read More
Fitar da Zakka zai kawo maganin talauci a Nijeriya, cewar AZAWON 

Fitar da Zakka zai kawo maganin talauci a Nijeriya, cewar AZAWON 

Daga MUKHTAR A. HALLIRU TAMBUWALa Haɗejia  Kungiyar Zakka da Waƙlaafi ta ƙasa (AZAWON) ta buƙaci gwamnatoci a matakin tarayya da jihohi da su yi amfani da tsarin Zakka da Waƙafi, domin magance matsalolin ƙuncin rayuwa da matsin tattalin arziki da ke addabar ƙasar nan. Shugaban ƙungiyar Malam Muhammad Lawal Maidoki, Sadaukin Sakkwato, shi ya yi wannan kiran a yayin wani taron manema labarai da ƙungiyar ta kira a garin Haɗejia na Jihar Jigawa, a wani ɓangare na Babban Taron ƙasa da ƙungiyar ke gudanarwa karo na 4. Shugaban ƙungiyar ya bayyana cewa, ƙididdigar da aka gudanar a shekarar 2015 ta…
Read More
Me Tinubu ya yi da za a sake zaben shi —Atiku

Me Tinubu ya yi da za a sake zaben shi —Atiku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya mayar da martani kan furucin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, wanda ya ce ’yan Arewa su hakura da neman kujerar shugaban ƙasa a 2027, sai 2031 idan Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu. Manhaja ta ruwaito George Akume na cewa ’yan Arewa ’yan Jam’iyyar APC mai mulki da ke son neman shugabancin ƙasa su haƙura zuwa 2031, saboda a cewarsa, yanzu lokacin mulkin ’yan yankin Kudu ne, don haka su jira sai Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu. Ya kuma buƙaci Atiku, babban abokin hamayyan Tinubu…
Read More

Nan ba da jimawa ba Nijeriya za ta fara fitar da gangar mai 30,000 a kowacce rana – Shettima

Daga BELLO A. BABAJI A wata gagarumar nasara ƙarƙashin gyare-gyaren da Shugaba Bola Tinubu ke yi wa ɓangaren mai a Nijeriya, kamfanin gas na 'Oriental Energy Resources Limited' ya fitar da Dala 316 don bunƙasa samar da man fetur a ƙasar bisa tsarin maɗaukan FPSO. Aƙalla ganga miliyan ɗaya FPSO zai ke fitarwa wanda hakan ya ƙera adadin ganga 17,000 da ake iya samarwa zuwa ganga 30,000 a kullum. A rabin farko na shekarar 2025 ne ake sa ran tsarin zai fara aiki a Nijeriya. Mataimakin shugaban ƙasa, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu a yayin bikin buɗe sabon tsarin na…
Read More

Dujiman Katsina ya musanta zargin ƙaurace wa mazaɓarsa

Hon. Aliyu Abdullahi Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban kwamitin harkokin cikin gida na Majalisar Wakilai, Hon. Aliyu Abdullahi, kuma Dujiman Katsina, ya musanta zargin da Abdullahi Musawa ya yi masa na ƙaurace wa mazabarsa. Abdullahi Musawa ya yi zargin ne a wata kafar sadarwa ta yanar gizo inda ya soki ɗan majalisar da ƙaurace wa mazaɓarsa duk da matsalar tsaro da yankunan ke fama da shi. Saidai mataimaki na musamman kan yaɗa labarai, Mr Francis Sardauna a wata takarda da ya fitar, ya musanta batun zargin da Abdullahi Musawa ya yi wanda ya yi hakan ne don neman ɓata…
Read More
Gwagwarmayar dimukraɗiyya: Bello El-Rufai ya yaba wa Uba Sani da Shehu Sani 

Gwagwarmayar dimukraɗiyya: Bello El-Rufai ya yaba wa Uba Sani da Shehu Sani 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Dan Majalisar Wakilai, Hon. Mohammed Bello-El-Rufai (APC-Kaduna), ya yaba wa Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ta 8, da kuma Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna bisa gagarumar rawar da suka taka a fafutukar tabbatar da dimukraɗiyya a Nijeriya. Hon. El-Rufai mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta Arewa, wanda ɗan tsohon Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ne, inda ya kuma yaba wa Marigayi Gani Fawehinmi, Femi Falana da sauran masu kishin ƙasa, ya bayyana hakan ne a wajen wani taron da ƙungiyar ’yan majalisar dokoki ta ƙasa (NASSLAF)…
Read More