Labarai

Za mu kai hakimin Bichi fadarsa cikin lumana – Sarki Sanusi

Za mu kai hakimin Bichi fadarsa cikin lumana – Sarki Sanusi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya tabbatar wa mazauna yankin ƙaramar Hukumar Bichi da ke jihar Kano cewa, Masarautar za ta tabbatar da an kai musu Hakimin su, Munir Sanusi Bayero, domin ya ci gaba da gudanar da aikinsa cikin lumana a Bichi. An bayyana cewa jami’an ‘yan sanda da jami’an DSS sun tare hanyar shiga fadar Gidan Rumfa, inda suka hana zirga-zirgar shiga da fita. Ko da yake ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro ba su bayyana dalilin ɗaukar matakin ba, amma majiyoyi sun ce ci gaban ya na da nasaba…
Read More
Tinubu zai gabatar da kasafin kuɗin 2025 ranar Talata

Tinubu zai gabatar da kasafin kuɗin 2025 ranar Talata

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai gabatar da ƙudirin kasafin kuɗin shekarar 2025 ga Majalisar Dokoki ta ƙasa ranar Talata. Akpabio ya bayyana hakan ne a majalisar ranar Alhamis a cikin zauren Majalisar Dattawa. Ya ce, “Shugaban ƙasa ya bayyana aniyarsa ga majalisar dokokin ƙasar na gabatar da kasafin kuɗin 2025 a zaman haɗin gwiwa na Majalisar a ranar 17 ga Disamba, 2024. Akpabio ya bayyana cewa za a gabatar da kasafin kuɗin ne a Zauren Majalisar Wakilai. Tunda farko Tinubu ya gabatar da takardun daftarin tsarin…
Read More
Zaɓen 2027: INEC na son katin zaɓe ya zama hanyar tantancewa

Zaɓen 2027: INEC na son katin zaɓe ya zama hanyar tantancewa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta gabatar da shawarar sake duba katinan zaɓe na dindindin (PVCs) a matsayin hanyar tabbatar da waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri’a a zaɓen 2027. INEC ta kuma nemi yin garambawul don inganta tsarin zaɓen ƙasar, bayan darussan da aka koya daga babban zaɓen shekarar 2023 da kuma zaɓukan da ba a yi ba. Da yake jawabi yayin wani taro da kwamishinonin zaɓe na mazauni a Abuja, shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, taswirar kwamfuta da aka yi wa mai…
Read More
Ƙarancin takardun kuɗi ya haddasa dogayen layika a na’urar ATM 

Ƙarancin takardun kuɗi ya haddasa dogayen layika a na’urar ATM 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu mazauna birnin Kalaba sun nuna fargaba kan rashin samun kuɗaɗe daga bankuna da kuma na’urar ATM a cikin birnin. Mazauna yankin da suka zanta da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya a Kalaba a ranar Laraba, sun ce samun kuɗi ya yi matuƙar wahala a cikin mako guda da ya wuce. NAN ta ruwaito cewa an samu dogayen layukan ATM a kewayen birnin yayin da mazauna garin ke kokawa wajen samun kuɗi. NAN ta kuma ƙara da cewa lamarin na yin ta’adi a kan ƙananan ‘yan kasuwa da ba su da na'urar POS da…
Read More
NCDC ta buƙaci  cibiyoyin lafiya su ƙara azamar gwaji cutar Korona

NCDC ta buƙaci cibiyoyin lafiya su ƙara azamar gwaji cutar Korona

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Hana Yaɗuwar Cututtuka ta Nijeriya, NCDC, ta bayyana fargaba a game da ɓullar sabuwar cutar korona a ƙasar Australia da ma wasu ƙasashe 42. Yayin da ta ke bayani a kan sabuwar cutar ga jami'anta, ta buƙaci dukkan asbitoci na gwamnati da ma masu zaman kansu da su ƙara yin gwajin da suke a kan dukkan marassa lafiyar suke zargin sun kamu da sabuwar cutar Korona. Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, NCDC, ta ce duk wani samfurin da aka samu yana ɗauke da cutar to a kai shi ɗakin gwaje gwajenta…
Read More
An yi walimar taya sakataren dindindin na ma’aikatar ilimin Jihar Kano, Bashir Baffa murna

An yi walimar taya sakataren dindindin na ma’aikatar ilimin Jihar Kano, Bashir Baffa murna

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf da cewa babu wani abu da ya fiifita a gabansa da ya wuce harkar bunƙasa ci gaban ilimi, ta bijiro da tsare-tsare na cigaban ilimi  amma sai an yi haƙuri abubuwa za su tafi yadda ake so sakamakon irin matsalolin da suka zo suka samu a harkar ilimi. Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano Hon. Haruna Doguwa ne ya bayyana hakan a yayin taron walima da ƙungiyar shugabannin makarantun sakandire suka shiryawa sabon sakataren dindindin na ma'aikatar ilimi na jihar Kano Kwamared Bashir Baffa Muhammad. Ya ce…
Read More
Dalilan da ya sa mahaifina ya auri mata 30 da ‘ya’ya 108 – Gwamnan Ebonyi

Dalilan da ya sa mahaifina ya auri mata 30 da ‘ya’ya 108 – Gwamnan Ebonyi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya bayyana dalilan da suka sa mahaifinsa, Ezekiel Nwifuru, ya auri mata har 30 da kuma haihuwar ‘ya’ya 108. Nwifuru ya bayyana hakan ne a ƙarshen mako a lokacin bikin naɗa mahaifinsa Sarkin Oferekpe Agbaja kamar yadda jaridar Sun ta rawaito. Ezekiel da fari ya auri mata 30 ne, sai dai izuwa yanzu adadinsu ya dawo 29 saboda goge sunan wasu daga jerin matansa sakamakon gaza haihuwa da suka yi. Sannan matan nasa 19 su ne suka haifa masa ‘ya’ya 108 amma bayan naɗa shi wannan sarauta, a yanzu…
Read More
Wasu jihohi ba za su iya biyan albashin N70,000 ba idan aka tabbatar da ƙudurorin haraji – Gwamna Lawal

Wasu jihohi ba za su iya biyan albashin N70,000 ba idan aka tabbatar da ƙudurorin haraji – Gwamna Lawal

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya ce wasu jihohin da ba su da ƙarfin tattalin arziki za su shiga tasku idan aka amince da ƙudurorin haraji da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aika majalisa. "Don haka dole a nazarci ƙudurorin cikin tsanaki saboda kar mu cuci kanmu," in ji shi a tattaunawarsa da tashar Channels a ranar Talata. Ya ƙara da cewa, "a cikin ƙudurorin akwai abubuwa masu kyau, akwai kuma marasa kyau, wannan ya sa muke ƙara nazartar abubuwan da ke ciki domin ba mutanenmu shawara kan abin da ya kamata." Lawal ya…
Read More
Ya kamata a riƙa ɗaure shugabanni da suka ci rashawa – Obi

Ya kamata a riƙa ɗaure shugabanni da suka ci rashawa – Obi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Dan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi ya ce kamata ya yi duk shugabanni da aka samu da cin hanci a Nijeriya su riƙa fuskantar tsassaurar hukunci. Obi ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata domin bikin ranar yaƙi da cin hanci ta duniya. A cewarsa, cin hanci ya dabaibaye dukkan matakan gwamnati a Nijeriya a tsawon shekaru. Ya ce ƙasar na fuskantar tarin bashi da ya yi mata katutu, wanda ya faru sakamakon ciyo bashi da gwamnatoci ke ci gaba da yi.…
Read More
Shugabannin da shaiɗan ya yi wa huɗuba ba sa yin nasara – Obasanjo

Shugabannin da shaiɗan ya yi wa huɗuba ba sa yin nasara – Obasanjo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ce shugabannin da shaiɗan ya yi wa huɗuba ba sa yin nasara, yayin da waɗanda Allah ya zaɓa ne ke yin nasara. Ya musanta cewa da yawan shugabanni na yin abin da Allah Ya tsara, inda ya jaddada cewa wasu shaiɗan ne ke musu huɗuba. Yayin wata tattaunawa ta yanar gizo mai suna “Boiling Point Arena” a ranar Lahadi, Obasanjo ya ce, “Yawancin shugabanni Allah ne ke ɗora su a kan mulki. Amma ba dukkaninsu ne ke yin nasara ba. “Shaiɗan ma yana iya ɗora shugabanni a kan…
Read More