Labarai

PDP Kano: Mu haɗu mu ɗinke ɓarakar cikin gida don cimma nasara – Yahaya Bagobiri

PDP Kano: Mu haɗu mu ɗinke ɓarakar cikin gida don cimma nasara – Yahaya Bagobiri

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An jaddada kira ga 'ya'yan Jam'iyyar PDP musamman jagorori da masu faɗa a ji su yi haƙuri su taho a haɗa hannu da ƙarfe a gina cigaban jam'iyyar a jihar Kano. Shugaban Kwamitin Dattawan jam'iyyar na jihar Kano, Alhaji Yahaya Umar Bagobiri ne ya jaddada hakan, ya ce Kano wuri ne da yake da muhimmanci sosai a siyasa, jiha ce da take da faɗi da tasiri da bai kamata ace  ana samun rarraba a jam'iyyar da ake ganin ita ce mafita ga al'umma daga halin ƙunci da jam'iyya mai mulki ta jefa su a ciki…
Read More
Gwamnatin Nijeriya ta zuba jarin sama da Dala miliyan 450 a harkar iskar gas na CNG

Gwamnatin Nijeriya ta zuba jarin sama da Dala miliyan 450 a harkar iskar gas na CNG

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Litinin, Kwamitin Fadar Shugaban ƙasa kan shirin inganta amfani da iskar gas (PCNGi) ya bayyana zuba hannun jarin sama da dala miliyan 450 kan shirin samar da iskar gas samfurin CNG. Daraktan shirin inganta amfani da iskar gas, Michael Oluwagbemi, ne ya bayyana hakan a yayin wani taro kan makamashi a Nijeriya karo na 9 na rana ta biyu da aka yi a jihar Legas mai taken taron shi ne “Makamashi domin ɗorewar masana’antu”. Oluwagbemi, wanda Tosin Coker, ya wakilta kuma shugaban sashen kasuwanci na PCNGi, ya ce, shirin ya yi nasarar…
Read More
Masu ƙananan sana’o’i za su amfana da sabbin dokokin haraji – Shugaban NOA

Masu ƙananan sana’o’i za su amfana da sabbin dokokin haraji – Shugaban NOA

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babban daraktan hukumar wayar da kan jama’a ta ƙasa, NOA, Lanre Issa-Onilu, a ranar Talata ya bayyana cewa, ƙudirin gyaran dokar harajin da ake shirin yi zai kawar da yawan haraji kuma tagomashi ne ga masu ƙananan sana'o'i a ƙasar. Mista Issa-Onilu ya bayyana haka ne a yayin wani tattaki na wayar da kan al’umma kan kaucewa son yin arziki da gaggawa da kuma sake fasalin haraji. Tattakin, wanda ya faro daga harabar Obasanjo ta Sabon-Gari, ya kare ne a ofishin NOA da ke Ladi-Kwali IBB Way a Minna, jihar Neja. Issa-Onilu, wanda ya…
Read More
An yi garkuwa da hadimin Yahaya Bello

An yi garkuwa da hadimin Yahaya Bello

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan ta’adda sun yi garkuwa da Honorabul Kabiru Onyene, sanannen hadimi ga tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello. A ranar Litinin ne ’yan bindiga suka yi awon gaba da Hon. Kabiru a ofishinsa da ke garin Okene da misalin ƙarfe 7 na dare, bayan sun yi ta harbi kan mai uwa da wabi. Wani ganau ya ce “kwatsam muka jin harbe-harbe, jama’a sun fara guje-guje, shi ne muka gane cewa ƙarar bindiga ne. “Bayan ’yan mintoci sai muka ji harbe-harben a wurin ofishin Kabiru, inda suka tafi da shi. “Amma abin mamaki shi ne…
Read More
Ɗalibai 91 sun kammala haddar Alƙur’ani a makarantar Aƙsat a Gombe

Ɗalibai 91 sun kammala haddar Alƙur’ani a makarantar Aƙsat a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Makarantar Aƙsat da ke Gombe ta kammala yaye ɗalibai 91, ciki har da matan aure guda takwas, a bikin yaye ɗaliban ta karo na goma.  Wannan makaranta, wacce aka kafa a shekarar 2009, ta riga ta yaye mahaddatan Alƙur’ani guda 600 tun daga lokacin da ta fara. A cikin bikin, shugaban ƙaramar hukumar Gombe, Barista Sani A.A Haruna, ya yaba wa mamallakin makarantar, Dakta Auwal Abdullahi Gafakan Akko, saboda ƙoƙarinsa na yaɗa ilimin Alƙur’ani a jihar.  Haruna ya kuma yi kira ga Dakta Auwal da ya faɗaɗa makarantar zuwa sauran ƙananan hukumomi 11 na…
Read More
Tsaro: Gwamnatin Yobe ta bai wa ’yan banga da mafarauta kyautar babura

Tsaro: Gwamnatin Yobe ta bai wa ’yan banga da mafarauta kyautar babura

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bai wa ’yan banga da mafarauta kyautar babura don kyautata harkar tsaro a jihar. Mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkar tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritaya) ne, ya miƙa baburan ga ’yan bangar. A lokacin, ya bayyana cewa wannan tallafin yana daga cikin ƙoƙarin gwamnatin na tabbatar da zaman lafiya a jihar. Abdulsalam, ya ce wannan ba shi ne karon farko da gwamnati ke tallafa wa ’yan banga da kayan aiki ba. Ya ce ko a baya gwamnatin ta ba su irin wannan…
Read More
Yahaya Bello zai yi bikin Kirsimeti da Sabuwar Shekara a gidan yari

Yahaya Bello zai yi bikin Kirsimeti da Sabuwar Shekara a gidan yari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kotu ta tura tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello zuwa Gidan Yarin Kuje kan almundahanar Naira biliyan 110.4. A ranar Talata Mai Sharia Maryann Anenih ta bayar da umarnin tare da dage sauraron shari’ar zuwa ranar 29 da watan Janairun 2025. Umarnin na zuwa ne bayan Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arzikin ƙasa (EFCC) ta kama tsohon gwamnan wanda suka jima suna wasan ɓuya da shi. Tun da farko alƙalin ta yi watsi da neman belin Yahaya Bello, wanda ta ce an yi riga malam masallaci, saboda an shigar da buƙatar ce kafin…
Read More

Shettima ya yi jimamin hatsarin da ya rutsa da sabbin ɗaliban da aka yaye a Jami’ar Borno

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya bayyana kaɗuwarsa game da mummunan hatsarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu ɗaliban da aka yaye a Jami'ar Borno. Lamarin ya auku ne a Maiduguri babban birnin jihar inda ya kuma raunata wasu da dama. Cikin wani saƙon ta'aziyya da mataimakin shugaban ƙasar ya aika a ranar Alhamis, ya yi jimamin yadda ɗaliban suka rasa damar cigaba da rayuwa bayan kammala karatu. Ya ce rasa rayukan da aka yi ba ga iyalansu bane kaɗai, har ma da Jihar Borno da Nijeriya baki ɗaya ƙasancewar sun bar giɓin da ba za…
Read More
Gwamnoni 36 sun miƙa rahoto kan ‘yan sandan jihohi

Gwamnoni 36 sun miƙa rahoto kan ‘yan sandan jihohi

Majalisar tattalin arzikin Ƙasa (NEC) ta karɓi rahotanni daga gwamnonin jihohi 36 kan batun kafa ‘yan sandan jihohi a ƙasar nan. Taron wanda mataimakin shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranta, ya samu halartar gwamnonin jihohi, mataimakan gwamna, ministoci da wasu hadiman shugaban ƙasa. Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya bayyana wa manema labarai bayan taron cewa gwamnonin sun nuna goyon baya sosai ga kafa ‘yan sandan jihohi, duba da matsalolin tsaro da ke addabar jihohinsu. Sai dai majalisar ta ɗage tattaunawa kan batun zuwa watan Janairu 2024 domin samun cikakken rahoto daga ofishin NEC. Gwamna Uba Sani ya yi…
Read More

Rundunar sojoji ta yi wa jami’ai 656 ritaya

Daga BELLO A. BABAJI Sojojin sun yi wa ƙasa hidima ne ta tsawon shekaru 35 inda suka ɗauki watanni shida suna karɓar horon tantancewa kafin yi musu ritayar, a Cibiyar Sansanin Sojojin Nijeriya (NAFRC) dake Oshodi a Jihar Legas. Sojojin sun haɗa da na ƙasa guda 535 da na ruwa guda 86, da na sama 35 da kuma wasu biyu daga Hukumar Leƙen Asiri (NIA). A lokacin da ya ke jawabi, Shugaban sojojin Sama, Iya Mashal Hassan Abubakar ya jinjina wa sojojin bisa ƙoƙarinsu da horo da suka samu waɗanda hakan suka yi sanadiyyar yaye su. Ya ce samuwar rundunar…
Read More