13
Dec
Daga BELLO A. BABAJI Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, ta bada belin tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello akan Naira miliyan 500 da wakilcin mutune biyu. Hakan na zuwa ne a lokacin da tsohon gwamnan ya bayyana cewa ba shi da hannu a laifuka 19 da Hukumar EFCC ta shigar akansa. Tsohon gwamnan yana fuskantar tuhuma ne kan handame wasu kuɗaɗe da adadinsu ya kai Naira biliyan 80, inda ya musanta zargin da ake masa. A lokacin da aka kira sauraron ƙarar a ranar Juma'a, lauyan dake kare ɓangaren EFCC, Kemi Pinheiro (SAN) ya sanar da kotun yunƙurin bincikensu na…
