Labarai

Muna horar da matasa da ɗaukar su aiki – Sani Diso

Muna horar da matasa da ɗaukar su aiki – Sani Diso

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano  Shugaban kamfanin samar kujerun zamani da dangoginsu da ke Kano, Alhaji Sani Diso, wanda aka fi sani da Uncule, ya bayyana cewa wannan kamfani na iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya ba al'ummar Kano da ma Nijeriya baki ɗaya gudunmawa ta fuska ɗaukar matasa aiki da kuma horar da su ta hanyar ɗorasu akan kyakkyawan tsari da tarbiyya yadda za a samu bunƙasar tattalin arziƙi da tsaro. Sani Diso ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da wakilinmu ya yi da shi cikin satin nan a Kano. A ƙarshe Sani Ancule, ya ƙara da cewa matasa…
Read More
An yaudari Gwamnan Kebbi da ma’aikata kan sabon albashi na N70,000 

An yaudari Gwamnan Kebbi da ma’aikata kan sabon albashi na N70,000 

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi  Akwai yiwuwar ko dai ma'aikatan ƙananan hukumomi da malaman firamare a Jihar Kebbi su yi bore ko su tsunduma cikin yajin aiki ko kuma a sake lale dangane da maganar sabon albashi na Naira 70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, saboda tun watan goma da aka ƙaddamar da shirin sabon albashin ba a biya su ba, aka ce akwai waɗansu 'yan gyare-gyare da za a yi da zummar za a biya bayan sati biyu, sai ga shi har watan ya ƙare ba a biya ba har kuma zuwa watan goma sha ɗaya, inda aka biya…
Read More
Bafarawa da Naja’atu sun kafa sabuwar tafiyar matasan Arewa 

Bafarawa da Naja’atu sun kafa sabuwar tafiyar matasan Arewa 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Fitacciyar ’yar gwagwarmayar Arewa, Hajiya Naja’atu Mohammed da tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa sun ƙaddamar da wata sabuwar tafiyar matasa domin ceto yankin Arewacin Nijeriya. A ranar Talata ne manyan ’yan siyasan Arewan suka ƙaddamar da tafiyar matasan da nufin tallafa wa matasan Arewa da kuma lalubo mafita daga matsalolin siyasa da tattalin arziki da suka dabaibaye yankin. A jawabinsa, Bafarawa wanda tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a Jam’iyyar DPP ne, ya shaida wa mahalarta taron cewa, “lokaci ya yi da matasa za su karɓi jagoranci. Idan aka ba su dama, za su…
Read More
’Yan ta’adda 129,417 suka miƙa wuya ga dakarun Nijeriya a wata shida – Janar Musa

’Yan ta’adda 129,417 suka miƙa wuya ga dakarun Nijeriya a wata shida – Janar Musa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa adadin ‘yan ta’addan Boko Haram 129,417 da iyalansu su ka miƙa wuya ga jami’an tsaro tsakanin 10 ga watan Yuli zuwa 9 ga Disamba, 2024. CDS ya bayyana haka ne a taron tsaro na Afrika karo na 18 da ake gudanarwa a birnin Doha na ƙasar ƙatar wanda wakilin Daily Trust ya sanya wa ido manhajar zoom. Taron ya samu halartar mahalarta daga Najeriya, Guinea Bissau, Gambia, Afirka ta Kudu, Kenya, da ƙatar. Janar Musa a jawabinsa ya bayyana cewa alkaluman sun…
Read More
Matatar Ɗangote ta fara fitar da man fetur zuwa Kamaru

Matatar Ɗangote ta fara fitar da man fetur zuwa Kamaru

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Matatar man Ɗangote, matatar mai mafi girma a Afirka, ta yi nasarar fitar da man fetur na farko zuwa Kamaru. Kamfanin Neptune Oil ne zai karɓi wannan man a ƙasar da ke tsakiyar Afirka, in ji sanarwar haɗin gwiwa da ƙungiyoyin biyu suka fitar a ranar Laraba. Kamfanonin sun bayyana jigilar kayayyaki a matsayin wata dabarar haɗin gwiwa da nufin ƙarfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin Nijeriya da Kamaru tare da magance ƙaruwar buƙatar makamashi a yankin. Kamfanonin biyu na ci gaba da binciken wasu tsare-tsare don kafa amintacciyar hanyar samar da kayayyaki, da nufin…
Read More
Zamfara za ta dawo da ɗaliban Cyprus don kammala karatu a gida

Zamfara za ta dawo da ɗaliban Cyprus don kammala karatu a gida

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau  Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce an kammala shirye-shiryen dawo da ɗaliban ta da ke karatu a jami’ar ƙasar Cyprus a halin yanzu, domin ba su damar kammala karatun digiri a jami’o’in Nijeriya.  Kwamishinan Ilimi, Kimiya da Fasaha na Jihar Zamfara, Alhaji Wadatau Madawaki ya bayyana haka lokacin da yake karɓar masu ruwa da tsaki na ƙungiyar ɗaliban Jihar Zamfara (FAZAMS) da suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa jiya Alhamis.  A cewarsa, nan ba da jimawa ba za a dawo da ɗaliban kafin ƙarshen wannan shekara.  Ya ƙara da cewa, ma’aikatarsa ​​tare da haɗin…
Read More
Majalisar Dattijai ta taka wa Wike burki kan rusau a Abuja

Majalisar Dattijai ta taka wa Wike burki kan rusau a Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar dattijan Nijeriya ta buƙaci Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da ya dakatar da rushe gidaje a Abuja har sai an kammala binciken da kwamitin riƙon ƙwarya na majalisar zai gudanar. An cimma wannan matsaya ne a ranar Alhamis bayan wani ƙudiri da Sanata Ireti Kingibe ta gabatar, inda ta nuna damuwa cewa rusau a FCT sun ɗauki wani mummunan yanayi. Kingibe ta dage cewa akwai buƙatar Majalisar Dattijai ta sa baki. “Har ila yau, akwai damuwa na cewa ana rusau a Abuja ba bisa ƙa’ida ba, kuma wasu mutane da dama sun…
Read More
Gwamnan Kano ya kori Sagagi, Bichi da Ɗantiye daga gwamnatinsa

Gwamnan Kano ya kori Sagagi, Bichi da Ɗantiye daga gwamnatinsa

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi garambawul a Majalisar Zartarwarsa. Mai magana da yawun gwamnan na Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai jiya Alhamis. Sanarwar ta ce, gwamanan cire Shugaban Ma’aikata na Fadar Gwamnatin Jihar Kano, Shehu Sagagi, da Kwamishinan Yaɗa Labarai, Halilu Dantiye, da kuma Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Baffa Bichi, wanda shi saboda rashin lafiya ne aka sauke shi, sannan kuma ya rushe Ofishin Shugaban Ma’aikatansa, Shehu Wada Sagagi. Sauran kwamishinonin da aka sauke sun haɗa da Kwamishinan…
Read More

Sabon ciyaman a Kano ya yi barazanar sauka daga kujerarsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Shugaban ƙaramar hukumar Gwale, Abubakar Muazu Mojo ya yi barazanar ajiye aikinsa na shugabancin ƙaramar hukumar muddin ba’a sauya masa Daraktan Mulki, wato DPM ba. Rahotanni sun bayyana cewa tuni ciyaman ɗin ya bada umarnin rufe ofishin DPM ɗin, wato Danjuma Zubairu Bebeji. A wani saƙon murya da Mojo ya aika wa manema labarai, ya yi ikirarin cewa idan har Daraktan Mulkin bai bar ƙaramar hukumar ba, to shi zai bar masa wajen. Ya kuma ce manufofin DPM ɗin sun saɓa da tsarin Kwankwasiyya na yi wa jama’a hidima da taimako. Rahotanni sun bayyana cewa…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar Dattawa ta bada umarnin kamo Darakta-Manaja na Julius Berger

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Dattawa ta bada umarnin kamo Darakta-Manaja na kamfanin Julius Berger, Dakta Peter Lubasch saboda ƙin amince wa haɗuwa da kwamitinta na ayyuka. Majalisar ta yi hukuncin ne a lokacin da Mai tsawatarwa na ɓangaren marasa rinjaye, Sanata Osita Ngwu (PDP Enugu ta Yamma) ya shigar da batun. Batun, wanda Sanata Asuquo Ekpenyong da Mpigi Barinada suka ɗauki nauyinsa, ya sanar da Majalisar cewa Manajan Kamfanin ya ƙi amince wa bayyana a gaban kwamitin ne wanda ke neman ya bada bayanai game da ayyukan da aka jingine waɗanda kuɗinsu ya kai N54bn zuwa N195bn. Shugaban majalisar,…
Read More