Labarai

Kasafin kudi 2025: An ware miliyan 50 ga kowace ƙaramar hukuma don sayen taki a Kano – Hon. Massu

Kasafin kudi 2025: An ware miliyan 50 ga kowace ƙaramar hukuma don sayen taki a Kano – Hon. Massu

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Shugaban kwamitin ƙananan hukumomi da sha'anin masarautu na majalisar dokokin Jihar Kano Zubairu Hamza Massu ya bayyana cewa an warewa kowace ƙaramar hukuma naira Miliyan 50 domin sayen iri a kasafin kuɗi na shekarar 2025. Honarabul Massu wanda shi ne wakilin ƙaramar hukumar Sumaila ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan zaman majalisar. Hamza Massu ya ce babban abin da ya fi burgeni shi ne kwakyawan tanadi da aka yi wa noma, wanda ya ce a halin da ake ciki yanzu harkar noma yana da matukar muhimmanci. Ya ƙara da cewa "Noma ne hanya mafi…
Read More
‘Yan sanda a Katsina sun kama mutane bakwai da zargin yi wa ‘yan mata fyaɗe

‘Yan sanda a Katsina sun kama mutane bakwai da zargin yi wa ‘yan mata fyaɗe

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Yanzu haka mutane bakwai sun shiga hannun 'yan sanda bisa zargin su da aikata fyaɗe wa yan mata su hudu a garin Kaita, ƙaramar hukumar kaita. Mai magana da yawun 'yan sanda a Katsina ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya faɗi haka a yayin da yake gabatar da masu laifin ga manema labarai a ofishin sa. Ya bayyana cewa dubun ya cika ne bayan da aka kwarmatawa 'yan sanda a ofishin su da ke garin Kaita inda nan take suka kai sumame a gidan ɗaya da a ke zargi. ASP Abubakar Sadiq ya ce 'yan sandan…
Read More
Gwamna Lawal ya raba tallafin Naira biliyan huɗu ga mutum 44,000 a Zamfara

Gwamna Lawal ya raba tallafin Naira biliyan huɗu ga mutum 44,000 a Zamfara

Daga USMAN KAROFI Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da rabon tallafin kuɗi na sama da naira biliyan huɗu ga mutane 44,000 a faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar. Wannan tallafi wani ɓangare ne na shirin COVID-19 Action Recovery and Economic Stimulus (NG-CARES) da aka gudanar a ɗakin taro na Garba Nadama, JB Yakubu Secretariat, Gusau. Da yake jawabi a wurin bikin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa an tsara shirin don tallafawa masu rauni, inda aka ba mata kaso 60% na kuɗaɗen da aka ware don tabbatar da daidaito da adalci. Ya ce, “Mata zawarawa, waɗanda aka saki da…
Read More

Majalisar Wakilai ta umarci a gaggauta bincike kan zargin fasa-ƙwauri da cin zarafi a hukumar Kwastom

Daga BELLO A BABAJI A ranar Laraba ne Majalisar Wakilai ta yanke gudanar da bincike game da zargin ayyukan fasa-ƙwauri da cin zarafi daga wani jami'in Hukumar Kwastom (NCS). Majalisar ta yi hakan ne a yayin zama tsakanin ƴaƴanta da aka saba, a lokacin da ɗan Majalisa Mista Oluwaseun Whingan daga Jihar Legas ya gabatar da ƙudirin al'umma na gaggawa. Ɗan majalisar ya bayyana yadda gidajen jaridu daga kafafen sadarwa da Sahara Reporters suka ruwaito yadda aka yi fasa-ƙwaurin wasu motoci sama da 2,000 waɗanda ke ɗauke da shinkafa a yankin Badagry, akan idon jami'an Kwastom. Ya ƙara da cewa…
Read More

A karon farko za a yi gasar Kofin Duniya a Saudiyya

Daga BELLO A. BABAJI A karon farko a tarihin ƙwallon ƙafa, Hukumar FIFA ta na shirin tabbatar da ƙasar Saudiyya a matsayin wadda za ta jagoranci gudanar da wasannin Kofin Duniya na shekarar 2034. Haka ma ƙasashen Morocco da Sifaniya da Portugal za su jagoranci gudanar da gasar ta shekarar 2030. Za a gudanar da batun tabbatar da ƙasashen a matsayin waɗanda za su jagoranci wasannin a yayin zaman FIFA, amma hakan ba zai sauya su matsayinsu ba kasancewar babu wasu ƙasashen da ke gogayya da su wajen neman riƙe jagorancin. FIFA ta bada damar zaɓo ƙasa daga Nahiyoyin Asia…
Read More
Ƙidayar jama’a: Majalisar Dokokin Kano za ta haɗa kai da NPC don wayar da kan al’umma

Ƙidayar jama’a: Majalisar Dokokin Kano za ta haɗa kai da NPC don wayar da kan al’umma

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Majalisar dokokin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore ta ƙaddamar da haɗin gwiwa tare da hukumar ƙidayar yawan jama’a ta ƙasa NPC domin gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a game da ƙidayar jama’a da za a yi a shekarar 2025. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban majalisar Kamaluddeen Sani Shawai ya fitar ranar Talata, ya jaddada cewa akwai muhimmiyar rawar da sahihan bayanan ƙidayar jama’a ke takawa wajen ciyar da ɓangarori masu muhimmanci a cikin al’umma. Falgore ya jaddada ƙudurin majalisar dokokin Kano na haɗin gwiwa da…
Read More
Ƙungiyar ma’aiktan aikin gona ta Kano ta zaɓi shugabannin riƙon ƙwarya

Ƙungiyar ma’aiktan aikin gona ta Kano ta zaɓi shugabannin riƙon ƙwarya

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ma'aikatan aikin gona ta ƙasa reshen Jihar Kano, wato Nigerian Union of Agriculture and Allied Employees, (UNAAE)ta ƙaddamar da shugabannin shiyyoyin ƙungiyar da za su jagoranci yankinsu na wata uku. A jawabinsa, manajan darakta na hukumar aikin gona na Jihar Kano KNARDA Dr. Faruku Kurawa wanda daraktan istanshan na KNARDA Gambo Isa Garko ya wakilta, ya yaba da shugabannin riƙon na ƙungiyar reshen Jihar Kano da suka zaɓo waɗannan jajirtattun masu riƙon kwaryar. Ya Kuma ja hankalin waɗanda aka naɗa da su fahimci cewa riƙon ƙwarya aka ba su ba na dindin ba,…
Read More

Yanzu-yanzu: A karo na 12, rumbun lantarki na ƙasa ya sake lalacewa

Daga BELLO A. BABAJI Cikin wani saƙo da ofishin ya wallafa a shafinsa na X, ya ce lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 2:09 na ranar Laraba. Wannan shi ne karo na 12 cikin shekarar 2024 da irin hakan ke faruwa. Acikin saƙon, ofishin ya ce nan ba da jimawa za a fara aikin gyara a kai. Haka ma kamfanin raba wutar lantarki na Jos ya fitar da sanarwa game da batun inda ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:33 na rana wanda hakan ya sanya kwastomominsa suka rasa wuta, kamar yadda Kakakin Kamfanin, Dakta Friday…
Read More

‘Yan sandan Kano sun kama jabun kuɗi na Naira 129bn

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Rundunar ƴan sanda a Jihar Kano, ta kama wasu mutane uku da aka samu jabun kuɗaɗe a wajensu da adadinsu ya kai Naira biliyan 129 da miliyan 542 da kuma naira 824 (N129,542,824,000). Kuɗaɗen sun haɗa da jabun Dalar Amurka, CFA da kuma Naira. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke holen waɗanda ake zargin a shelkwatar rundunar dake unguwar Bompai. SP Kiyawa ya ce sun samu nasarar kama mutum na farko mai suna Ahmad Abdullahi, ɗan shekaru 30 mazaunin ƙaramar hukumar Kaga ta jihar Borno, bayan…
Read More
‘Yan sanda a Katsina sun kama ‘yan ta’adda ɗauke da kayan sojoji

‘Yan sanda a Katsina sun kama ‘yan ta’adda ɗauke da kayan sojoji

' Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Aminu Hassan ɗan shekara 25 da ya fito daga ƙauyen Dundubus a ƙaramar hukumar Ɗanja ya fara zuwa hannu. Da yake gabatar da waɗanda ake zargi da ta'adancin, jami'in yaɗa labarai na rundunar 'yan sanda ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce sun kama Aminu Hassan ne a ƙaramar hukumar Ɗanmusa ɗauke da kayan sojoji har guda biyu . Ya ƙara da cewa shi wannan ɗan ta'adda ya maida garuruwan da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa a matsayin wajen da yake aikata ta'adancin sa. ASP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa binciken da 'yan sanda suka gudanar…
Read More