Labarai

An tabbatar da mutuwar ƙanwar gwamnan Taraba da aka harba

An tabbatar da mutuwar ƙanwar gwamnan Taraba da aka harba

Atsi Kefas, ƙanwar Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas ta rasu bayan harbin ta da aka yi daga ɗaya daga cikin ƴan sanda masu tsaron lafiyarta yayin da suke ƙoƙarin kare ta daga harin ƴan bindiga. Rahotanni sun bayyana cewa ta rasu ne a wani asibiti da ke Abuja, inda aka kai ta don samun kulawa. Wani majiyarmu ya bayyana cewa, “Ta rasu daren jiya sabida raunuka da ta samu. Har yanzu gwamna da iyalansa ba su fitar da wata sanarwa kan rasuwar Atsi Kefas ba.Muna miƙa ta'aziyyarmu ga iyalan gwamnan a wannan lokaci.” Wata majiya ta ƙara tabbatar da lamarin,…
Read More
Tinubu ya naɗa Babatunde a matsayin Akanta Janar na ƙasa

Tinubu ya naɗa Babatunde a matsayin Akanta Janar na ƙasa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Mista Shamseldeen Babatunde Ogunjimi a matsayin muƙaddashin Akanta Janar na Tarayya (AGF). Wannan sanarwa ta fito daga mai ba Shugaban Ƙasa shawara Bayo Onanuga, ranar Talata. Naɗin ya fara aiki nan take bayan hutun ritaya da Akanta Janar na yanzu Dakta Oluwatoyin Sakirat Madein ta fara. Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa naɗin Ogunjimi zai tabbatar da sauyin shugabanci cikin sauƙi a fannin kula da baitulmalin ƙasa tare da ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da gwamnatin ta ke yi a harkokin baitulmalin ƙasa. Ogunjimi, wanda shi ne babban darakta mafi girma a ofishin…
Read More

NG-CARES: Gwamnan Zamfara ya ƙaddamar da raba kuɗi don rage raɗaɗin rayuwa ga mutane 44,000

Daga SANUSI Muthammad a Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da tsarin rabon kuɗaɗe ba tare da wani sharadi ba ga mutane 44,000 za su ci gajiyar shirin a ƙarƙashin ayyukan Bankin Duniya, wato NG-CARES. Da yake jawabi yayin ƙaddamar da shirin da aka gudanar a Sakatariyar JB Yakubu dake Gusau, a ranar Talata, Gwamna Dauda ya bayyana cewa shirin na da nufin inganta rayukan al’ummar jihar. A cewarsa, shirin ya kasu kashi uku inda aka zaɓo dukkan wadanda suka ci gajiyar shirin cikin tsanaki a ƙananan hukumomi 14 dake jihar. Ya yi nuni da cewa, a ƙarƙashin…
Read More
Sake naɗa Fatima Shinkafi a hukumar ma’adanai ta ƙasa ya dace – Kabiru Oro

Sake naɗa Fatima Shinkafi a hukumar ma’adanai ta ƙasa ya dace – Kabiru Oro

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wani fitaccen matashin jam’iyyar APC, Kuma mataimaki na musamman ga jamil'iyyar APC ta Ƙasa kan tsare tsare, Kabiru Oro Ƙaura Namoda, ya yaba wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bisa sake naɗa Fatima Umaru Aliyu Shinkafi a matsayin babbar sakatariyar hukumar bunƙasa ma’adinai. Yana mai bayyana cewar naɗin ya cancanta. Shugaba Bola Tinubu ya sanar da sake naɗa Hajiya Fatima Umaru Shinkafi a matsayin babbar sakatariyar asusun bunkasa ma'adanai PAGMI. Kabiru Oro Ƙaura Namoda a wata sanarwa da ya fitar yace Hajiya Fatima Umaru Aliyu Shinkafi ta nuna jajircewar ta ga ajandar sabunta fata na…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta yi watsi da buƙatar belin Yahaya Bello

Daga BELLO A. BABAJI Mai Shari'a Maryanne ta Babbar Kotun Tarayya ta yi watsi da batun neman belin tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello. Alƙalin ta yi hakan ne saboda a lokacin da aka rubuta takardar belin, tsohon gwamnan ba ya hannun Hukumar EFCC, wadda ita ta maka shi kotu. A ranar 22 ga Nuwamba ne aka shigar da takardar yayin da aka kai Yahaya Bello ofishin EFCC a ranar 26 ga watan kuma aka gurfanar da shi a ranar 27. Sauran bayanai za su zo daga baya.....
Read More
Shettima ya umarci bankuna su kawo ƙarshen ƙarancin kuɗi

Shettima ya umarci bankuna su kawo ƙarshen ƙarancin kuɗi

Mataimakin shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya yi kira ga babban bankin Nijeriya (CBN) da bankunan kasuwanci su gaggauta magance matsalolin ƙarancin kuɗi da kuma cajin POS da ‘yan Nijeriya ke ƙorafi akai. Shettima ya bayyana hakan yayin jawabi a taron shekara-shekara na kwamitin bankuna da aka gudanar a Abuja ranar Juma’a. An wakilce shi ne ta mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tattalin arziki Dakta Tope Fasua, wanda ya ce, “Wannan dama ce ta roƙon ku da ku kawo ƙarshen matsalolin da ke shafar ƙoƙarin gwamnati na haɗa kowa da tsarin kuɗi da tattalin arziki.” Mataimakin shugaban Ƙasa ya…
Read More

Ƙungiyar SCDGG ta ƙi amincewa da sake naɗin Fatima Shinkafi a hukumar ma’adanai

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ƙungiyar nan mai fafutukar tabbatar da dimokuraɗiyya da shugabanci na gari (SCDGG) da ke da hedikwata a Jihar Zamfara ta nuna damuwa kan yadda Shugaban ƙasa ya tsawaita wa’adin aikin Hajiya Fatima Shinkafi a matsayin Babbar Sakatariyar Hukumar Kula da Ma’adinai ta Ƙasa, inda ƙungiyar ta yi Allah wadai da sake ba ta muƙamin. Ko’odinetan ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Ibrahim A. Sahabi, ne ya yi tsokacin a taron manema labarai a Gusau, Babbab Birnin Jihar Zamfara, a ranar Litinin. A cewarsa, Fatima Shinkafi ta yi aiki na tsawon shekaru takwas a matsayin Babbar Sakatariyar hukumar,…
Read More
Faɗan daba ya yi sanadiyyar rasuwar mutane biyu a Kano

Faɗan daba ya yi sanadiyyar rasuwar mutane biyu a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Rundunar 'yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar mutane biyu biyo bayan faɗan daba da ake zargin wasu matasa daga unguwannin Zango da kuma Ƙofar Mata. Kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan a zantawarsa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke unguwar Bompai Kano. SP Abdullahi Kiyawa ya ce tun a ranar Lahadi, suka samu kiraye-kiraye daga unguwar Ƙofar Mata daidai lokacin da aka tashi wasa a filin wasa na Sani Abacha Stadium, inda wasu matasa suka dinga yin faɗace-faɗacen daba tsakanin Unguwa da…
Read More
Shettima ya caccaki shugabar jam’iyyar Conservative ta Ingila, Kemi Badenoch, bisa ƙasƙanta Nijeriya

Shettima ya caccaki shugabar jam’iyyar Conservative ta Ingila, Kemi Badenoch, bisa ƙasƙanta Nijeriya

Daga USMAN KAROFI Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya caccaki sabon shugabar jam’iyyar Conservative ta Birtaniya, Kemi Badenoch, kan kalamanta masu zafi ga Nijeriya. Shettima ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin taron tattaunawa na shekara-shekara karo na 10 kan batutuwan hijira, wanda aka gudanar a fadar shugaban ƙasa, Abuja. A cikin jawabinsa, mataimakin shugaban ƙasa ya ce, "Kemi Badenoch, shugabar jam’iyyar Labour ko Conservative ta Birtaniya, muna alfahari da ita duk da ƙoƙarinta na yin watsi da ƙasar da ta fito. Tana da ‘yancin faɗin ra’ayinta, har ma da cire sunan Kemi daga sunanta, amma hakan ba zai sauya…
Read More
Ba za a sanya hukumar da ta gaza bayyana yadda ta kashe kuɗaɗenta a kasafin 2025 – Majalisar Dattawa

Ba za a sanya hukumar da ta gaza bayyana yadda ta kashe kuɗaɗenta a kasafin 2025 – Majalisar Dattawa

Majalisar Dattawa ta Nijeriya ta hannun kwamitin Kuɗi ƙarƙashin jagorancin Sanata Sani Musa, ta yi gargadi ga hukumomin gwamnatin tarayya da ke ƙin bayar da rahotannin yadda suka kashe kuɗaɗen kasafin kudinsu na shekarar 2024. Sanatan ya bayyana haka a wani bincike na musamman a ranar Litinin cewa majalisar za ta dakatar da ware kuɗaɗe ga duk wata hukuma da ba ta bi umarnin majalisar ba na bayar da bayanan kuɗaɗe. A yayin ganawar da Akanta Janar na Tarayya, Miss Oluwatoyin Madein, kwamitin ya nuna rashin jin daɗin sa da tsarin biyan albashi na bai ɗaya wato IPPIS da ofishin…
Read More