Labarai

Hamɓararren shugaban ƙasar Siriya, Al-Assad da iyalansa sun samu mafaka a Rasha

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Al-Assad da iyalansa suna Birnin Moscow, kamar yadda hukumomin labarai a ƙasar Rasha suka bayyana, sa'o'i bayan ya tsere daga Siriya a lokacin da dakarun addinin Islama suka shiga Damascus. Hakan na zuwa ne a lokacin da Rashar, wadda ƙawa ce ga Al-Assad, ta kira taron gaggawa na majalisar tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) don samar da mafita bisa halin da ƙasar ta tsinci kanta aciki. Tuni dai wani jami'an Gwamnatin Rasha ya tabbatar da cewa hamɓararren shugaban ƙasar da iyalansa sun samu mafaka a Moscow. Rasha tare da takwararta ta Iran sune manyan…
Read More

Kamfanin Turkiyya zai fara noman zamani a Zamfara don bunƙasa harkar noma

Daga BELLO A. BABAJI Sanannen kamfanin Turkiyya mai suna 'Direkci Group' zai fara aiki noman zamani da haɗe kai da gidajen gonaki a Jihar Zamfara don bunƙasa harkokin noma. A ranar Asabar ne Darakta-Manaja na kamfanin, Nurullah Mehmet ya jagoranci wata tawaga zuwa ofishin Gwamna Dauda Lawal dake gidan gwamnatin jihar. Kamfanin ya ƙudiri aniyar inganta harkar noma a jihar ta hanyar samar da auduga da rake da kuma waken suya a ma'auni mai girman gaske. Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, kamar yadda ya fitar a wata takarda, ya ce kamfanin za ta gabatar da tsare-tsare na zamani wajen yin…
Read More
Ministan yaɗa labarai zai shugabanci taron IPI

Ministan yaɗa labarai zai shugabanci taron IPI

An sanar da cewa Ministan yaɗa labarai na Nijeriya, Mohammed Idris, zai jagoranci taron shekarar 2024 na reshen Nijeriya na International Press Institute (IPI) wanda za a gudanar a ranar Laraba a birnin Abuja. Wannan sanarwa ta fito daga bakin Ahmed I. Shekarau, sakataren IPI Nijeriya, a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin. Sanarwar ta bayyana sunayen fitattun baƙi da suka tabbatar da halartar taron, ciki har da mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, tsohon gwamnan Jihar Ogun, Olusegun Osoba, mai wallafa jaridar Vanguard, Sam Amuka Pemu, Shugaban ƙungiyar masu jaridu ta Nijeriya (NPAN) Kabiru…
Read More

Gwamnan Zamfara ya yi garambawul ga kwamishinoninsa

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi kwaskwarima tawagar kwamishinoninsa inda ya rantsar da sabon kwamishina. A ranar Litinin ne gwamnan ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwar wanda a lokacin ne aka gabatar da rantsarwar. A wata sanarwa da Kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, gwamnan ya yi ƙaramin gyara ne ga kwamishinonin nasa. Bayan murabus da Mannir Mu'azu Haidara ya yi sakamakon lashe zaɓen ciyaman na ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda, sai aka naɗa Ƙasimu Sani Ƙaura a matsayin sabon kwamishinan don ya wakilci ƙaramar hukumar saboda jajircewarsa. Gwamna Dauda ya ce hakan wani ɓangare ne na…
Read More
FRSC ta yi Allah wadai da yadda ake kai ɗalibai jami’ar FUDMA cikin motar tanki

FRSC ta yi Allah wadai da yadda ake kai ɗalibai jami’ar FUDMA cikin motar tanki

Daga UMAR GARBA a Katsina A makon da ya gabata ne aka riƙa yaɗa wani faifan bidiyo a shafukan sada zumunta, inda aka ga ɗaliban jami'ar gwamnatin tarayya dake Dutsimma a Katsina sun hau wata babbar motar dakon man fetur a hanyarsu ta zuwa jami'ar. Saboda haka ne hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) ta buƙaci jami’ar da ta ƙara ƙaimi wajen samar da isassun motocin bas da za su kai ɗalibai daga tshohuwar harabar makarantar zuwa sabon mazaunin jami'ar. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kwamandan hukumar FRSC, Aliyu Ma’aji ya fitar ta hannun mai magana da…
Read More
An hana shugaban ƙasar Koriya ta Kudu fita daga ƙasar

An hana shugaban ƙasar Koriya ta Kudu fita daga ƙasar

Ma’aikatar Shari’a ta Koriya ta Kudu ta sanar a ranar Litinin cewa an hana Shugaban Ƙasa Yoon Suk Yeol fita daga ƙasa, bayan mako guda da kafa dokar ta ɓaci na ɗan gajeren lokaci. A daren ranar 3 ga Disamba, Shugaba Yoon ya aika da rundunar sojoji na musamman da jiragen sama masu saukar ungulu zuwa majalisar dokoki, sai dai ‘yan majalisar sun yi watsi da dokar ta ɓacin da ya kafa, wanda hakan ya sa ya janye umarnin. Wannan matakin ya haifar da tashin hankali a ƙasar, inda jama’a suka yi zanga-zanga, suna kira da a sauke shi daga…
Read More
Opay, Moniepoint da Palmpay sun fara cajin N50 kan hada-hadar N10,000

Opay, Moniepoint da Palmpay sun fara cajin N50 kan hada-hadar N10,000

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Al'umma sun koka biyo bayan aiwatar da cire N50 kan duk hada-hadar kuɗi da ta kao N10,000 zuwa sama da Opay, Moniepoint da sauran bankunan intanet suka fara a Nijeriya. A cikin wata sanarwa ga kwastomomi a ranar Lahadi, 1 ga Disamba, 2024, Moniepoint, ta ce matakin ya bi ƙa’idojin Hukumar Harajin Cikin Gida ta Tarayya (FIRS), tare da lura da cewa za a yi amfani da kuɗin ne zuwa asusun sirri da kasuwanci. Harajin da ake cirewa, wanda ake kira 'electronic money transfer leɓy' (EMTL) kuɗi ne da ya kai Naira 50 akan duk wara…
Read More
Tallafin fetur: Gwamnatin Tarayya ta fara binciken NNPC kan tiriliyan N2.7

Tallafin fetur: Gwamnatin Tarayya ta fara binciken NNPC kan tiriliyan N2.7

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ofishin Odita-Janar na Tarayya ya karɓi cikakkun takardun da ake buƙata don tantance tallafin man fetur na Naira Tiriliyan 2.7 da Kamfanin Man Fetur na Nijeriya ya samu gwamnati. An aiwatar da hakan ne domin sanin haƙiƙanin yadda ake tafiyar kuɗaɗen cire tallafin mai. Idan dai ba a manta ba, a watan Afrilun 2024, gwamnatin tarayya ta fara wani sabon bincike na neman tallafin man fetur na Naira Tiriliyan 2.8 da hukumar NNPC ta samu. Wani kamfanin binciken kuɗi mai suna KPMG, ya gudanar da bincike na farko, inda ya rage kuɗin daga tiriliyan N6 zuwa…
Read More
Shekarar 2024 ce mafi tsanani ga ma’aikatan Nijeriya, inji NLC

Shekarar 2024 ce mafi tsanani ga ma’aikatan Nijeriya, inji NLC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC), ta bayyana shekarar 2024 a matsayin shekarar da ma’aikata suka fi fuskantar ƙalubale a ƙasar. Joe Ajaero, Shugaban NLC, ya bayyana haka a ranar Litinin a Abuja, a wajen wani taron Makarantar Harmattan na 2024. Taron na Makarantar Harmattan, taro ne na shekara-shekara da NLC ke shiryawa, wanda ke aiki a matsayin shirin ilimantar da ma'aikata da sauran tsare-tsare. Ya ce, shekarar 2024 ga ma’aikata a ƙasar nan ta zo da tsananin wahala. Ajaero ya umarci ma'aikatan da ke shiga makarantar harmattan da su himmatu a cikin horon wanda a cewarsa,…
Read More

FAZAMS ta yaba wa Gwamna Dauda kan farfaɗo da harkar Ilimi a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ƙungiyar daliban Zamfara ta FAZAMS, ta yaba wa gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal kan inganta fannin ilimi a jihar. Shugaban ƙungiyar mai barin gado, Kwamared Abubukar Galadima ya bayyana hakan a wani taron ƙungiyar da manema labarai wanda aka gudanar a Hedikwatar hukumar ilimin bai ɗaya ta jihar. A cewarsa, yabon ya zama dole duba da yadda gwamnan ya ayyana dokar ta-ɓaci akan ilimi wanda ya haifar da kyakkyawan sakamako na kawo sauyi a fannin cikin shekara ɗaya da rabi. Kwamared Galadima ya ce, taken taron shi ne 'Gina nasarorin da aka samu,…
Read More