Labarai

Ɗan takarar jam’iyya mai mulkin Ghana ya amsa shan kaye a zaɓen Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin shugaban ƙasar Ghana kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NPP ya sha kaye a zaɓen da aka kammala a ranar Lahadi inda ya taya tsohon shugaban ƙasar, John Mahama murna bisa nasarar da ya samu. A wani jawabi da Mista Bawumia ya gabatar, ya tabbatar da nasarar da jami'iyyar adawa ta NDC a mataki na shugaban ƙasa da na ƴan majalisu ta samu. Ya kuma yaba da zaɓen kasancewar an gudanar da shi cikin lumana tare da karɓar shan kaye da ya yi. Mahama wanda ya sha kaye a hannun Nana Akufo-Addo a shekarar…
Read More
‘Yan bindiga sun sace mata sama da 50 a Zamfara

‘Yan bindiga sun sace mata sama da 50 a Zamfara

' Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wasu gungun ‘yan bindiga sun kai farmaki ƙauyen Kakin Dawa da ke ƙarƙashin gundumar Gidan Goga a ƙaramar hukumar Maradun a Jihar Zamfara inda suka yi garkuwa da mata sama da 50. Wani mazaunin yankin mai suna Malam Musa Lawali Kakin Dawa ya shaida wa wakilin mu ta wayar tarho cewa ‘yan bindigar sun yiwa ƙauyen ƙawanya da misalin ƙarfe 1 na daren jiya inda suka fara bincike gida-gida. "Lokacin da suka afkawa ƙauyen, yawancin mazaje sun gudu domin tsira da rayukan su, saboda mun san cewa mu ne abin da suke nema, amma…
Read More
Lokaci ya yi domin gyaran dokokin haraji – Idris

Lokaci ya yi domin gyaran dokokin haraji – Idris

Ministan yaɗa labarai Mohammed Idris, ya bayyana cewa haraji wani babbar hanya ce da gwamnati ke samun kuɗaɗe domin samar da ayyukan jin dadin jama’a. Duk da haka, ya ce tsarin gudanar da haraji a Nijeriya na bukatar gyara, musamman saboda matsalolin da suka shafi tsarawa da aiwatarwa, tare da halayyar masu biyan haraji. Ministan ya yi nuni da cewa sake duba dokokin haraji da ake yi a yanzu na da muhimmanci, musamman a matsayin wani ɓangare na manufofin farfaɗo da tattalin arziki na ƙasar. Ya ce cikakkun bayanai kan sabbin ƙudirorin dokokin haraji suna nan a fili, kuma ya…
Read More
‘Yan sanda a Katsina sun ceto mutane 20 a hannun ‘yan ta’adda

‘Yan sanda a Katsina sun ceto mutane 20 a hannun ‘yan ta’adda

' Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 'Yan sanda a Katsina sun sami nasarar kuɓutar da mutane 20 daga hannun 'yan ta'adda a lokacin da su kai ƙoƙarin sace mutanen a ƙananan hukumomin Jibiya da Faskari. Jami'in yaɗa labarai na hukumar 'yan sanda a Jihar Katsina ASP Sadiq Abubakar Sadiq ya bayyana wa manema labarai haka a wata takarda ɗauke da sa hannun sa. Lamarin ya faru ne da yammacin Asabar da ta wuce a Magaman Jibiya inda ƴan bindigan ɗauke da bindigar AK47 suka tare wata motar fasinja a ƙoƙarin su na karkatar da fasinjoji zuwa cikin daji. Sai dai…
Read More
Babu sabon nau’in ƙwayar COVID na XEC a Nijeriya – Gwamnatin Tarayya

Babu sabon nau’in ƙwayar COVID na XEC a Nijeriya – Gwamnatin Tarayya

Ma'aikatar Lafiya ta Ƙasa ta bayyana cewa ba a gano sabuwar nau'in cutar COVID-19 mai suna XEC a Nijeriya ba. Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Alhaji Alaba Balogun, mataimakin darakta na bayar da bayani da hulɗa da jama’a a cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja a ranar Asabar. Balogun ya ce ya zama dole a gyara bayanan ƙarya da ke haifar da tsoro a tsakanin al’umma dangane da batun dawowar COVID-19 a ƙasar. Ya kuma bayyana cewa takardar da ta ke da lamba DHS/INSPDIV/017/VOL.1/46 wadda ta yi nuni da cewa nau'in XEC yana yaɗuwa a Nijeriya…
Read More

Hukumar NDE ta shirya wa matasa 300 bita a Jigawa

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Kimanin gurabe 2,922 ne Hukumar Samar da Aikin yi ta ƙasa (NDE) ta ware wa Jihar jigawa domin bai wa matasa horo akan sana'ar kiwon awaki da kaji da kifi da da kuma waɗanda za a koyawa gyaran mota da aikin sola a ƙoƙarin gwamnatin Tarayya na magance zaman banza a tsakanin matasan ƙasar nan. Hakan na daga cikin shirin hukumar a ƙoƙarinta na samawa matasa madogara tarevda haɗin-gwiwar Hukumar Jin-daɗin Mata da walwalar Jama'a ta ƙasa da aka shirya domin a sauya rayuwar al'umma daga mawuyacin halin ƙunci da matasa suke ciki. A…
Read More

Gwamnatin Katsina ta kashe N21bn ga samar da takin zamani ga manoma a jihar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta kashe Naira biliyan 21 wajen samar da da takin zamani ga manoman jihar a wannan shekarar. Gwamna Dikko Raɗɗa ya faɗi haka ne a lokacin da ya ke gabatar da kasafin kuɗin 2025 a zauren Majalisar Dokokin jihar a kwanakin baya. Ya ce takin zamani ton 20,000 da aka sayar wa manoma 350,000, an samar ne a bisa farashi mai rahusa. Bugu da ƙari, ya bayyana cewa gwamnati kuma ta tallafa wa manoman rani 2,040 da kayan aikin gona da kuɗinsu ya kai Naira 1.9bn. "Kayan aiki noman sun haɗa da…
Read More

Babu sansani sojojin waje a Nijeriya – Janar Musa ya ƙaryata jita-jitar yarjejeniya da Faransa

Daga BELLO A. BABAJI Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa ya ƙaryata batun da ke cewa an bai wa Faransa damar kafa sansanin sojoji a Nijeriya. Hakan na zuwa ne a lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya kai ziyara Faransa inda ƙasashen biyu suka cimma yarjejeniya game da ababen da suka haɗu a kai musamman kan harkokin tattali da makamantansu, ya na mai cewa babu wani layi acikin yarjejeniyar da ya bada damar samar da sansanonin sojojin waje a Nijeriya. Janar Musa na magana ne a bikin buɗe bajin sojoji (Tattoo Logo) na shekarar 2025, a Hedikwatar Tsaro…
Read More

Dakarun adawa sun hamɓarar da Shugaba Al-Assad na Siriya

Daga BELLO A. BABAJI Ƴan ɓangaren adawa na ƙasar Siriya sun ce mayaƙansu sun yi nasarar karɓe Damascus, kuma Shugaba Bashar Al-Assad ya tsere daga ƙasar. Kwamandan tawagar Tahrir Al-sham, Abu Muhammad Al-julani ya ce baki ɗaya ma'aikatun ƙasar za su kasance ne a ƙarƙashin firaminista har sai lokacin da aka miƙa su a hukumance. Hakan na zuwa ne sa'o'i kaɗan da dakarun adawar suka karɓe birane da dama a ƙasar. Tuni ƴan adawar suka gabatar da jawabin farko a tashoshin labarai. Wata majiya ta ce har an sako fursunonin Damascus dake tsare na tsawon lokaci a kurkuku. Ƙasashen Ƙatar,…
Read More