08
Dec
Babu wata al'ada, matsin tattalin arziƙi, ko zamantakewa da zai iya tabbatar da wahalar da miliyoyin mata da ƴan mata ke sha. Aikinmu shi ne mu kalubalanci waɗannan labarai masu cutarwa. Rashin daidaito tsakanin jinsi da cin zarafin mata na daga cikin manyan ƙalubalen da ke fuskantar ci-gaba mai ɗorewa, ba kawai a Nijeriya ba, har ma a duniya baki ɗaya. A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, a duniya kimanin mata miliyan 736, kusan kaso ɗaya daga cikin uku na fuskanci cin zarafi ta jiki ko ta hanyar jima'i, cin zarafi na jima'i, ko duka biyu aƙalla sau ɗaya a rayuwarsu,…
