07
Dec
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 'Yan Majalisar Dattawa daga shiyyar Arewacin Nijeriya sun buƙaci a dakatar da ƙudirin sabuwar dokar haraji da ke gaban majalisar da Shugaban ƙasa ke neman amincewarsu. 'Yan majalisar dattawan na Arewacin Nijeriya sun ce sun cimma wannan matsayar ne bayan tattaunawa tsakaninsu a ranar Litinin. Wannan na zuwa bayan majalisar wakilai ta dakatar da duk wata muhawara da ta shafi kuɗirin dokar harajin bayan wakilan jihohin arewacin kasar a majalisar sun nuna adawa da ƙudirin dokar. 'Yan majalisar sun cimma wannan matsaya ne bayan kudirin sabuwar dokar harajin ya tsallake karatu na biyu kuma…
