06
Dec
Daga BELLO A. BABAJI Aƙalla boma-bomai biyu ne suka tashi a wurare mabanbanta a yankin Ɗan-Sadau dake ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara. Rahotonni sun bayyana cewa ɗaya daga cikin boma-boman ya tashi ne akan hanyar dake tsakanin Ɗan-Sadau da Malamawa yayin da ɗayan ya fashe a hanyar Malele duk a gundumar ta Ɗan-Sadau. Wani mazaunin yankin mai suna Nuhu Babangida ya ce wata babbar mota ɗauke da hatsi da fasinjoji, ta tsallake rijiya da baya a lokacin da ta gitta kusa da bom ɗin. Ya ce a lokacin da boma-boman suka fashe a Malamawa da hanyar Malele, ba a…
