Labarai

Gwamnatin Kano za ta dawo da rusau a filayen gwamnati

Gwamnatin Kano za ta dawo da rusau a filayen gwamnati

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Jihar Kano ta fara rusa wasu haramtattun gine-gine da aka gina a filayen gwamnati a faɗin jihar. Wannan matakin da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ke jagoranta, ya shafi gine-ginen da aka gina ba tare da izinin zama a kan kadarorin gwamnati ba. Da yake jawabi a ranar Laraba a birnin Kwankwasiyya, sakataren kwamitin, Hameed Sidi, ya ce matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da jihar ke yi na kwatowa da kuma kiyaye haƙƙin al'umma domin samun ci gaba. Sidi ya bayyana cewa kwamitin ya gano sama da 10 na haramtattun gine-gine a birnin na…
Read More
Gwamnatin Kano ta yaba wa Ifing Media da One17 bisa taro kan harkar kuɗi a Musulunci

Gwamnatin Kano ta yaba wa Ifing Media da One17 bisa taro kan harkar kuɗi a Musulunci

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yaba wa Cibiyar Ifing Media ƙarƙashin shugabancin Mudathir Adesanya, da kuma Alhaji Zakari Ahmadu, shugaban cibiyar hadadar kuɗi ta Musulunci na One17 da ke najeriya sakamakon shirya taron da aka yi wa take da wayar da kan al'ummar Arewa akan hadadar kuɗi a Musulunci irinsa na farko da aka yi a Arewacin Nijeriya da aka kira Arewa Islamic Finance Summit, wanda cibiyoyin hadadar kuɗi na Musulunci suka halarta tare da manyan masana na cikin gida da na wajen Nijeriya, da aka gabatar da maƙaloli kan tasiri  da muhimmancin…
Read More
Shiyyar Kano ta samu sabon Mataimakin Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya

Shiyyar Kano ta samu sabon Mataimakin Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Shiyya ta ɗaya da ta haɗa Kano da Jigawa ta samu sabon mataimakin shugaban rudunar 'yan sandan Nijeriya, AIG Ahmed Ammani Malumfashi, wanda ya bayyana ƙudirinsa na cewa zai haɗa kai da shugabannin al'umma a kowane mataki da su kansu al'ummar tun daga ƙasa a matakin unguwanni da ƙauyuka na yankunan karkara da birane domin tabbatar da ingantaccen tsaro a wannan shiya ta Kano kamar yadda shugaban 'yan sandan Nijeriya IGP Kayode Egbetokun, ya naɗa shi a wannan aiki na mataimakin 'yan sandan Nijeriya, mai kula da Kano da Jigawa. AIG Malumfashi ya bayyana haka…
Read More
Zulum na matuƙar ƙoƙari wajen kawo cigaba a Borno – Hon. Abdu Labaki

Zulum na matuƙar ƙoƙari wajen kawo cigaba a Borno – Hon. Abdu Labaki

Daga GAMBO ISA Shugaban ƙaramar Hukumar Shani a Jihar Borno, Alhaji Hassan Abdu Labaki ya yaba wa Gwamna Farfesa Baba Gana Umar Zulum kan ayyukan ci gaban jihar a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja cikin makon nan. Abdu Labaki, ya zayyana wasu daga nasarorin da gwamnan ya samu a fannin walwalar ɗan Adam, ababen more rayuwa, inganta harka ilimi, tsaro, da dai sauransu. Abdu Labaki ya bayyana cewa nasarorin da gwamnan ya samu sun haɗa da, tsare-tsare na ci gaba kamar gina sakatariyar kansiloli na zamani a Shani, gina gidaje a babban birnin jihar…
Read More
‘Salt Lick’ da ‘yan uwansa sun nemi tallafin gwamnati don cigaban masana’antunsu

‘Salt Lick’ da ‘yan uwansa sun nemi tallafin gwamnati don cigaban masana’antunsu

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Wasu shugabannin masana'antu da ke Kano sun yi kira da Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da gwamnan Kano da sauran masu ruwa da tsaki kan su kawo tallafi na samar da ingantacciyar wutar lantarki domin bunƙasar masana'antu a Kano da Nijeriya baki ɗaya kamar dai yadda Alhaji Ado Sani Salt Lick, ya bayyana a lokacin taro nuna kayayyaki da masana'antu Kano ke sarrafawa da samarwa ga al'umma domin ci gaban jihar da ƙasa baki ɗaya. Alhaji Ado Sani wanda jami'i ne mai kula da saye da siyarwa, ya yaba wa ƙungiyar masu masana'antu ta ƙasa…
Read More
Shugaban ƙaramar Hukumar Bayo ya yaba wa Gwamna Zulum kan ayyukan raya jiha

Shugaban ƙaramar Hukumar Bayo ya yaba wa Gwamna Zulum kan ayyukan raya jiha

Daga GAMBO ISA Shugaban ƙaramar Hukumar Bayo a Jihar Borno, Alhaji Haruna Chibra ya yaba wa Gwamna Farfesa Baba Gana Umar Zulum kan ayyukan ci gaban jihar a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja cikin makon nan. Chibara, ya zayyana wasu daga nasarorin da gwamnan ya samu a fannin walwalar ɗan Adam, ababen more rayuwa, inganta harka ilimi, tsaro, da dai sauransu. Haruna Chibra ya bayyana cewa nasarorin da gwamnan ya samu sun haɗa da, tsare-tsare na ci gaba kamar gina sakatariyar kansiloli na zamani a Bayo, gina gidaje a babban birnin jihar da tsarin…
Read More
Google, Meta da TikTok sun biya Nijeriya harajin tiriliyan N2.55 a 2024

Google, Meta da TikTok sun biya Nijeriya harajin tiriliyan N2.55 a 2024

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kamfanonin dijital na ƙasashen waje da ke aiki a Nijeriya, da suka haɗa da Google, Microsoft, da TikTok, da dai sauransu, sun biya Gwamnatin Tarayyar Nijeriya jimillar harajin Naira Tiriliyan 2.55 a farkon rabin shekarar nan. Hukumar bunƙasa Fasahar Sadarwa ta ƙasa (NITDA) ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata ta hannun daraktar sashen sadarwa da hulɗa da manema labarai, Hadiza Umar, inda ta nakalto bayanai daga Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga ta Tarayya (FIRS) da Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS). NITDA, musamman, ta yaba wa Google, Microsoft, manhajar ɗ, da…
Read More
Gwamnan Zamfara ya tanadi biyan sabon tsarin albashi a sabon kasafin kuɗi

Gwamnan Zamfara ya tanadi biyan sabon tsarin albashi a sabon kasafin kuɗi

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da Naira biliyan 545,014 a matsayin kasafin kuɗin shekarar 2025 a ranar Alhamis ga Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, inda a cikin kasafin ya yi cikakken tanadin biyan ma’aikatan jihar sabon tsarin albashi na Naira 70,000. A cewarsa, kasafin kuɗin na tafiyar da ayyukan yau da kullum ya tsaya akan Naira biliyan 151,680, wanda shine kashi 28% na jimillar kuɗin da ake kashewa, inda ya ce, da gaske za a biya kuɗin ma’aikata, da suka haɗa da ƙarin mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000, fansho, gratuti da kuma samar…
Read More
Barnier ya yi murabus daga matsayin Firaministan Faransa

Barnier ya yi murabus daga matsayin Firaministan Faransa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Firaministan Faransa Michel Barnier, a ranar Alhamis, ya gana da Emmanuel Macron, domin miƙa takardar murabus ɗinsa, bayan da ya sha kaye a majalisar dokokin ƙasar, inda shugaban ƙasar ya yi gaggawar neman hanyoyin da za a dakatar da ruɗanin siyasa da na kuɗi. Barnier ya isa fadar Elysee ne domin yin murabus daga muƙaminsa, inda kundin tsarin mulkin ƙasar ya wajabta wa Firamiyan mai barin gado ya sauka bayan shan kaye a majalisar. Mafi yawan 'yan majalisar sun goyi bayan ƙuri'ar rashin amincewa da zaɓen da 'yan adawa masu ra'ayin riƙau da kuma…
Read More
An shigo da litar mai biliyan 2.3 Nijeriya duk da matatun Ɗangote da NNPC

An shigo da litar mai biliyan 2.3 Nijeriya duk da matatun Ɗangote da NNPC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Duk da fara aikin haƙo mai da wasu manyan matatun mai guda biyu suka yi a Nijeriya cikin watanni ukun da suka gabata, ‘yan kasuwar man sun ci gaba da shigo da man da kuma rarraba shi a faɗin ƙasar. An tattaro a ranar Laraba cewa ‘yan kasuwa sun shigo da litar mai biliyan 2.3 na fetur tsakanin 11 ga Satumba zuwa 5 ga Disamba, 2024. Ci gaba da shigo da man fetur ɗin ya saɓa wa sanarwar da wasu gungun ‘yan kasuwar suka yi a baya waɗanda tun farko suka bayyana aniyarsu ta dakatar da…
Read More