29
Nov
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sheikh Abdallah Gadon ƙaya ya bayyana cewa shi ma kusan shekaru biyu ya kwashe yana neman Aminu Abdullahi, mutumin da 'yan sanda suka kama shi bisa zargin damfarar 'yan kasuwa a jihar Kano. Rundunar 'yan sandan jihar Kano a ranar Laraba ta sanar da cafke Abdullahi, mai shekaru 50 da haihuwa bisa zargin amfani da sunan Sheikh Abdallah ya cuci al'umma. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an kama shi ne bisa ƙorafe-ƙorafen da wajen mutane 20 suka kawo cewa ya sayi kayansu amma bai tura musu kuɗin ta banki ba, inda…
