29
Nov
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara Hajiya Hurriyya Dauda Lawal a ranar Laraba ta jagoranci dubban mata da masu ruwa da tsaki a jihar wajen taron tattaunawa kan cin zarafin mata da yara ƙanana, tare da jaddada buƙatar dake akwai wajen haɗa ƙarfi da ƙarfe don kawo ƙarshen cin zarafin mata da yara marasa galihu a jihar ta Zamfara. Taron ya kasance wani ɓangare na fafutuka na kwanaki 16 don tunawa da ranar cin zarafin mata na shekarar 2024 a jihar. Shirin bada agaji na sa kai tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Zamfara ne suka shirya…
