Labarai

Kotu ta umarci EFCC ta riƙe Yahaya Bello zuwa 10 ga Disamba

Daga BELLO A. BABAJI Mai Shari'a Maryanne Anenih ta Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, ta ayyana ranar 10 ga watan Disamba a matsayin ranar da za ta yi hukunci game da belin tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello. Ana tuhumar Bello ne tare da wani Shua'ibu Oricha da AbdulSalami Hudu akan zargin su da laifin zamba cikin aminci da almundahanar wasu kuɗaɗe da adadinsu ya kai Naira biliyan 110.4. Bayan sauraron buƙatar mai kare waɗanda aka shigar ƙarar ne na a bada belin tsohon gwamnan, sai Alƙalin ta ayyana ranar gabatar da hukunci game da hakan. An tsare Yahaya Bello…
Read More

Yadda Yahaya Bello ya kwana a ofishin EFCC

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta'annati, EFCC ta tabbatar da kamawa tare da tsare tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello. Kakakin hukumar, Dele Oyewale ya bayyana hakan a yayin hira da manema labarai a ranar Talata inda ya ce Yahaya Bello na amsa tambayoyi daga wasu jami'an bincike na EFCC. Ya ce za kuma a gabatar da shi a gaban kotu bayan an kammala bincike akan sa. A gefe guda kuma, a miƙa ƙarar ne ga Mai Shari'a Maryanne Anenih ta Babbar Kotun Abuja inda a nan ne aka maka tsohon gwamnan, wanda ake…
Read More
Da Ɗumi-Ɗumi: An gurfanar da Yahaya Bello a kotu

Da Ɗumi-Ɗumi: An gurfanar da Yahaya Bello a kotu

Hukumar yaƙi da yiwa tattalin arziki ta’annati (EFCC), ta gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, a gaban babbar kotun birnin tarayya da ke Maitama. Ana sa ran Bello zai amsa tuhume-tuhume 16 da suka shafi zargin almundahanar Naira biliyan 110. A tuna cewa tsohon gwamnan ya miƙa kansa ga EFCC a ranar Talata bayan dogon wasan ɓuya da ya yi da hukumar. Sanye da farar riga da kuma hula mai shuɗi, jami'an tsaro na EFCC suka raka shi zuwa harabar kotun don gurfanarwar.
Read More
Shawarwarin masoyana ba sa canja min ra’ayi kan abin da zan rubuta – Ummu Maheer

Shawarwarin masoyana ba sa canja min ra’ayi kan abin da zan rubuta – Ummu Maheer

"Masu karatu ba sa mana uzuri" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Ummu Maheer ko kuma Miss Green kamar yadda wasu suka fi saninta, na daga cikin matasan marubutan onlayin da Allah Ya tarfa wa garinsu nono, sakamakon yadda littattafanta ke samun karɓuwa a wajen masu karatu, har da tsakanin 'yan'uwa marubuta. Shekaru biyar da fara rubutunta a zaurukan sada zumunta, Rabi'atu Bashir Abdullahi, kamar yadda asalin sunanta yake ta rubuta littattafai sun kai 19, yayin da take shirye-shiryen wallafa wasu a ciki. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba AbubakarYakubu, marubuciyar ta bayyana burinta na ganin marubuta sun haɗa kai wajen…
Read More
An bankaɗo ɓoyayyiyar shinkafar tallafi da Gwamnatin Tarayya ta aika Kano

An bankaɗo ɓoyayyiyar shinkafar tallafi da Gwamnatin Tarayya ta aika Kano

Daga USMAN KAROFI Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta kai sumame a wata ma’ajiya da ke unguwar Hotoro Ring Road, kusa da Farin Masallaci, inda aka gano ana sauya buhunan shinkafa 16,800 da ake zargin tallafin gwamnatin tarayya ne. Wannan shinkafa an ware ta ne don tallafawa jama’a, kuma an gano ana canza buhunta domin sayarwa a kasuwa. Shinkafar na ɗauke da hoton Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, tare da rubutun "Ba don sayarwa ba." Shugaban PCACC, Muhuyi Magaji Rimingado, yayin da yake jawabi a wurin sumamen, ya bayyana cewa, “Mun gano cewa wasu…
Read More
Tinubu zai tafi Faransa amsa gayyatar Macron

Tinubu zai tafi Faransa amsa gayyatar Macron

Daga USMAN KAROFI Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja a ranar Laraba don kai ziyara zuwa ƙasar Faransa bayan gayyatar da Shugaban Ƙasar Faransa, Emmanuel Macron ya yi masa. Ziyarar ta kwanaki uku tana da nufin ƙarfafa dangantakar siyasa, tattalin arziki da al'adu tsakanin ƙasashen biyu. Har ila yau, za a mai da hankali kan samar da damarmaki a fannoni kamar noma, tsaro, ilimi, lafiya, matasa da aikin yi, ƙirkire-ƙirkire da sauyin yanayi. A ranar Alhamis, Shugaba Tinubu da mai ɗakinsa, Sanata Oluremi Tinubu, za su karɓi tarba a gidajen tarihi na sojoji na Les Invalides da kuma…
Read More
EFCC za ta gurfanar da Yahaya Bello a kotu Larabar nan

EFCC za ta gurfanar da Yahaya Bello a kotu Larabar nan

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) za ta gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, a gaban kotu a ranar Laraba domin fuskantar tuhume-tuhume kan almundahanar kuɗaɗe da rashin gaskiya yayin gwamnatinsa. Rahotanni da Manhaja ta samu sun bayyana cewa an kama Yahaya Bello ne ranar Talata, 26 ga Nuwamba, 2024, yayin da bincike kan zarge-zargen almundahanar kuɗaɗe ke ci gaba. Wani jami'in hukumar ya tabbatarwa Jaridar Sahara Reporters cewa, "Za a tisa ƙeyarsa zuwa kotu yau Laraba domin fara shari'a." An tabbatar da cewa ana tsare da shi a hedikwatar EFCC da ke Abuja yayin da…
Read More

Gwamnatin Katsina za ta biya ƴan fansho duka bashin da suke bi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina za ta biya ƴan fansho duka kuɗaɗen da suke bi nan ba da jimawa ba. Kwamishinan Kasafin kuɗi, Hussaini Bello ya faɗi hakan a lokacin da ya ke wa manema labarai bayanin kasafin kuɗi na 2025. Ya ce gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan 15 domin biyan ƴan fanshon kuɗaɗensu. Kwamishinan ya ƙara da cewa ƴan fansho daga ƙananan hukumomi 34 na jihar za a biya su ne a tsakiyar shekara mai zuwa. Ya kuma ce cikin kasafin kuɗi na 2025, gwamnatin za ta kashe Naira biliyan 524 daidai da kashi 17,…
Read More

Tanka 200 matatar Fatakwal za ta riƙa fitarwa a kullum – Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Talata ne Fadar Shugaban Ƙasa ta ce aƙalla manyan motoci 200 na man fetur ne za a riƙa samarwa a kowacce rana daga matatar mai ta Fatakwal dake Jihar Ribas. Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X, Mai taimaka wa shugaban ƙasa na musamman kan harkar Sadarwa da Wayar da kan al'umma, Sunday Dare ya ce matatar ta sake dawowa don cigaba da aiki, wadda ake sa ran za ta riƙa samar da ganga 60,000 a kullum. Da farko dai Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPCL ya sanar da cewa matatar ta koma…
Read More

Yahaya Bello ya sake miƙa kansa ga EFCC

Daga BELLO A. BABAJI Alamu masu ƙarfi sun nuna cewa tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya sake amsa gayyatar Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta'annati, EFCC kan zargin sauya akalar wasu kuɗaɗe. Wata majiya daga hukumar ta bayyana wa manema labarai cewa a safiyar ranar Talata ne Yahaya Bello tare da lauyoyinsa suka halarci ofishin hukumar dake Abuja. Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar da ke ƙalubalantar halascin EFCC. A makon da ya gabata ne aka yi ta raɗeraɗin cewa tsohon gwamnan zai je ofishin hukumar a wani karon…
Read More