Labarai

Trump zai sa harajin kaso 25 ga kayayyakin Mexico da Canada

Daga BELLO A. BABAJI Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump ya ce zai sa harajin kashi 25 akan dukkan kayan da aka shigar Amurka daga ƙasashen Mexico da Canada a ranar farko ta shugabancinsa. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Trump ya ce zai ƙaƙaba harajin har zuwa lokacin da ƙasashen biyu za su dakatar da shigar da ƙwayoyi da kuma kwararar baƙi ƙasar ta kan iyakokinsu. Shugaban ƙasar ya kuma yi alƙawarin ƙara kashi 10 akan harajin kayan Chana har ita ma sai ta dakatar da fataucin ƙwayoyi zuwa Amurka. BBC ta ruwaito cewa, a…
Read More

Matatar Fatakwal ta koma tace ɗanyen man fetur

Daga BELLO A. BABAJI Matatar man fetur ta Fatakwal da ke Jihar Rivers ta dawo aiki, inda ta fara tace man fetur, kamar yadda Kakakin Kamfanin Man fetur na Ƙasa (NNPCL), Femi Soneye ya bayyana. Ya ce hakan wani sabon babi ne a ɓangaren makamashi a Nijeriya da yunƙurin inganta tattalin arziƙin ƙasar kamar yadda ya bayyana a ranar Talata. Soneye ya ce za a fara lodin man fetur ɗin daga yau Talata, sannan kamfanin NNPCL na yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da ita ma matatar Warri ta Jihar Delta ta fara aiki. BBC Hausa ta ruwaito cewa, lamarin…
Read More

IHR ga NAHCON: Ki naɗa kwamitin da zai kula da raba wa mahajjatan 2023 kuɗin rarar kuɗinsu

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar Masu Ruwaito Labaran Aikin Hajji da Umara (IHR), ta yi kira ga Hukumar Jigilar alhazai (NAHCON) da ta samar da kwamiti na musamman da zai kula da raba kuɗaɗen rarar kuɗin mahajjatan Nijeriya 95,000 waɗanda da suka je aikin Hajji a shekarar 2023. Hakan na zuwa ne la'akari da tsaiko da ake samu game da bai wa mahajjatan ire-iren kuɗaɗen a Nijeriya. Ciki wata sanarwa da Kodinetan ƙungiyar na ƙasa, Ibrahim Mohammed ya fitar a ranar Litinin, ya ce su na sane da cewa an raba kuɗaɗen ga hukumomin jigilar alhazai na jihohi don biyan…
Read More
Mutane da dama sun gudu daga gidajensu saboda harin ‘yan bindiga a Benue

Mutane da dama sun gudu daga gidajensu saboda harin ‘yan bindiga a Benue

Daga USMAN KAROFI a Abuja A jiya ne mazauna wasu ƙauyuka a ƙananan hukumomin Katsina-Ala da Logo na jihar Benue suka gudu daga gidajensu bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da kashe mutane da dama. Rahotanni daga mazauna yankunan sun bayyana cewa kimanin mutane 30 ne aka kashe yayin harin, yayin da wasu suka samu munanan raunuka. Ƙauyukan da aka kai wa hari a ranar Lahadi da safiyar Litinin, sun sha fama da irin waɗannan hare-haren a baya daga wasu ‘yan bangar siyasa na cikin gida. Wani mazaunin ƙauyen da ya bayyana sunansa kawai da David ya shaida…
Read More

Gwamna Raɗɗa ya gabatar da biliyan N682 ga Majilisar Dokoki a matsayin kasafi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, ya gabatar da Kasafin Kuɗi na shekarar 2025 da adadinsa ya kai Naira biliyan 682 a zauren Majalisar dokokin jihar. Da ya ke bayyani dalla-dalla game da ababen da kasafin ya ƙunsa, gwamnan ya sanar da ƙarin kaso 40 ga kasafin wannan shekarar. "Fannin ilimi ya fi samun kaso mai tsoka na biliyan N95.9, sai harkar Noma da ta samu biliyan N81.8. Haka kuma fannin tsaro da ya sami Naira biliyan 18.9." Gwamnan ya bayyana kasafin kuɗin a matsayin kasafi na al'umma inda ya ce gwamnati ba za ta iya…
Read More

Sarkin Katsina ya naɗa ɗan marigayi, Jakada Ibrahim Zakari a matsayin Talban Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Sarkin Katsina, Alhaji (Dr.) Abdulmummuni Kabir Usman ya naɗa Ibrahim Babangida Zakari, babban ɗan marigayi Talban Katsina, Jakada Ibrahim Zakari, a matsayin Talban Katsina. A wata wasiƙa da ke ɗauke da sa hannun mai martaba Sarkin, wanda ya aika wa sabon Talban, ya tabbatar masa da Sarautar ne bayan rasuwar mahaifinsa wanda shi ke riƙe da matsayin. Sarkin ya taya sabon Talban murnan samun Sarautar da fatan zai gaji mahaifinsa wajen kyautata wa al'umma da kawo cigaba a jihar. Mai martaba Sarkin ya kuma bayyana cewa nan bada jimawa ba za a sanya ranar da…
Read More
Dole mu rungumi fasahar zamani wajen yaƙi da matsalolinmu – Shettima

Dole mu rungumi fasahar zamani wajen yaƙi da matsalolinmu – Shettima

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya jaddada buƙatar amfani da dabarun fasahar zamani wajen yaƙi da ta'addanci, da manyan laifukan da ake aikatawa ta yanar gizo da ma sauran ƙalubalen tsaron kan iyaka a Nijeriya da Afirka baki ɗaya.Shettima ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin kwamitin gudanarwa na sashen sarrafa bayanan sirri na 17 ƙarƙashin Cibiyar Nazarin Tsaro ta ƙasa (NISS). Masu ziyarar suka ce Kwas ɗin ya mayar da hankali kan " Samar da hanyoyin Ƙarfafa tattalin arziki a Afirka tare da daƙile Ƙalubalen da nahiyar ke…
Read More

‘Ƴan sanda sun ceto fasinjoji 14 daga hannun ƴan bindiga a Katsina

Daga BELLO A. BABAJI Jami'an ƴan sanda a Katsina sun yi nasarar ceto fasinjoji 14 daga harin ƴan bindiga a ƙauyen Ɗan'arau dake Magama a ƙaramar hukumar Jibia ta Jihar Katsina. Kakakin ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Aliyu ya bayyana hakan cikin wata takarda da ya fitar, inda ya ce lamarin ya auku ne a ranar Lahadi. Ya ce ƴan bindigar sun farmaki wasu motoci biyu ne akan hanyar da nufin garkuwa da su inda suka yi ta harbe-harbe. A yayin haka ne ƴan sandan yankin suka samu labarin lamarin inda cikin hanzari suka kai ɗauki tare da yin ba-takashi…
Read More
Jihohi 11 da suka hana malamai ƙarin girma zuwa mataki na 16

Jihohi 11 da suka hana malamai ƙarin girma zuwa mataki na 16

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani bincike ya nuna cewa an hana malamai a jihohin Nijeriya 11 ƙarin girma zuwa mataki na 16 a aikin gwamnati. Bayanan da aka samu daga ƙungiyar malamai ta ƙasa (NUT) a Abuja, sun nuna cewa mafi yawan malaman da abin ya shafa suna makarantun firamare ne, inda a kodayaushe suke gaza samun ƙarin girma zuwa wasu matakai. Tun shekaru da dama da suka gabata, ƙungiyar NUT ta caccaki gwamnonin jihohin ƙasar kan gazawa wajen inganta malaman firamare zuwa mataki na 16 zuwa sama. Batun na nuna manyan ƙalubale a fannin ilimi, ciki har da rashin…
Read More
Yadda ‘yar Chana ta haifi jariri baƙar fata

Yadda ‘yar Chana ta haifi jariri baƙar fata

Kamar yadda kowa ya sani, ya kamata ranar haihuwa ta zama ranar da ta fi kowace ranar zama ranar farin ciki a rayuwar iyaye, amma ga wata matashiya ’yar asalin ƙasar Chana, ranar ta zama ta baƙin ciki bayan mijinta ya nemi a yi masa gwajin halittar ɗa da uba saboda sanin ko shi ne ya mahaifin ɗa baƙar fata da matarsa ta haifa ko akasin haka. A baya-bayan nan Jaridar China Times ta ƙasar Chana ta ba da labarin wani lamari mai ban mamaki na wata mata ’yar ƙasar a yankin Shanghai mai shekara 30 da ke da burin…
Read More