25
Nov
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Sunan Shaka Zulu na da nasaba da yaƙi. Dakarunsa kan tarwatsa duk wanda ya sha masa gaba. Kafin a haifi Shaka, wata bokanya mai suna Sithayi, ta ba da labarin cewa za a haifi wani yaro wanda zai kawo sabon sauyi da kuma sabuwar ƙasa. Ya kasance soja ɗan baiwa a Afirka. Mutum ne wanda ya gina ƙasa ba mai son kisa da zubar da jini ba. Kuma ba mutum ne mara tausayi ɗan ina da kisa ba. An haifi shi a watan Juli shekarar 1787 a cikin al'ummar eLangeni inda mahaifiyarsa ta fito. Mahaifinsa mutum…
