23
Nov
Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Sakkwato ta jaddada aniyarta ta inganta harkokin wutar lantarki a jihar ta hanyar kammala aikin tashar lantarki na gashin kanta (IPP). Gwamna Aliyu Ahmed ya bayyana hakan wa manema labarai jim-kaɗan bayan kammala zaman Majalisar Zartarwa ta jihar a gidan gwamnatin jihar, a ranar Laraba. Ya ce gwamnatinsu za ta tabbatar da yin duk mai yiwuwa wajen ganin an kammala aikin tashar wanda ake fatan ya taimaka wajen bunƙasa harkokin tattalin arziƙi a jihar. Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa zata bada cikakken goyon baya ga jami'an tsaro a ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan ta'addanci wanda a…
