Labarai

An yi naɗin Chiroman Kano kan cancanta – Uwa Matar Ɗansanda 

An yi naɗin Chiroman Kano kan cancanta – Uwa Matar Ɗansanda 

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano  Hajiya Uwa Matar Ɗan Sanda, Sarkin Guɗar Giwa matar Sarkin Kano, ta bayyana naɗin da aka yi wa ɗan Sarkin Kano, Muhammad Sanusi, a matsayin Chiroman Kano da cewa, an yi akan dacewa da cancanta. Ta ce, Chiroma yana koyi da mahaifinsa, don jama'a da akhairi da kyauta da karrama ɗan'adam da yin bajinta duk ya gada yana yi. Ta yi kira ga al'ummar Kano su haɗa kai da bai wa gwamnatin jihar ƙarƙashin Injiniya Abba Kabir Yusuf goyon baya ajiye duk hayaniya saboda a kyautata baya na 'ya'ya da jikoki su riƙa koyi da…
Read More
Takarar Musulmi da Musulmi: Ndume ya buƙaci Bwala ya nemi gafarar Shettima

Takarar Musulmi da Musulmi: Ndume ya buƙaci Bwala ya nemi gafarar Shettima

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya shawarci Daniel Bwala da ya nemi gafarar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima. A ranar Alhamis ne shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa Daniel Bwala, tsohon mai magana da yawun yaƙin neman zaɓen Atiku a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa. Dangane da yaƙin neman zaɓe kafin zaɓen 2023, Tinubu ya zaɓi Shettima a matsayin abokin takararsa. Bayan haka, Bwala ya yi murabus daga naɗin nasa a matsayin ɗan jam’iyyar APC, inda ya bayyana cewa ba zai iya goyon bayan tikitin…
Read More
Odita-Janar ya bankaɗo badaƙalar tiriliyan N3.4 a wasu ma’aikatun Nijeriya

Odita-Janar ya bankaɗo badaƙalar tiriliyan N3.4 a wasu ma’aikatun Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ofishin babban mai binciken kuɗi na tarayya (OauGF) ya bankaɗo badaƙalar kuɗi da suka kai Naira Tiriliyan 3.403 a wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati da dama. Laifukan guda 28 suna ƙunshe ne a cikin rahoton tantance ayyuka na shekarar 2021 na rashin bin ƙa’ida da gazawar kula da Ma’aikatun Tarayya na shekarar kuɗi ta 2021, wanda aka gabatar da su ga Majalisar Dokoki ta ƙasa ta hanyar wasiƙar lamba AuGF/AR. 2021/02, mai kwanan wata 15 ga Oktoba 2024 wanda babban mai binciken kuɗi na tarayya, Shaakaa Kanyitor Chira ya sanya wa hannu. Rahoton ya ce Naira…
Read More
Tinubu ya kafa asusun bunƙasa fasaha da ƙere-ƙere na ƙasa 

Tinubu ya kafa asusun bunƙasa fasaha da ƙere-ƙere na ƙasa 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban ƙasa Bola Tinubu, a ranar Talata ya sanar da kafa asusun bunƙasa harkar fasaha da ƙere-ƙere na ƙasa. Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a taron baje ƙolin Injiniya na ƙasa da ƙasa na NSE, 2024 a taron shekara-shekara a Abuja. ƙaramin ministan ayyuka Bello Goronyo ne ya wakilci shugaban. Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, taken taron shi ne, “Maganin fasaha mai ɗorewa ga Tsaron Abinci da Sauyin yanayi”. “Ina alfahari da sanar da kafa Asusun Injiniya da ƙere-ƙere na ƙasa. “Sabon yunƙuri ne da aka ƙera don ba…
Read More
Za mu ci gaba da talafa wa al’umma kamar yadda Khalifa ya yi – Jarumar Hausa  

Za mu ci gaba da talafa wa al’umma kamar yadda Khalifa ya yi – Jarumar Hausa  

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Shugabar gidauniyar USIR, Hajiya Ummasalama Ishaƙa Rabiu, sabuwar Jarumar Hausa da mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk ya naɗa a ranar Asabar da ta gabata, ta bayyana cewa wannan tallafi ba shi ne na farko ba kuma ba shi ne na ƙarshe ba, ta ce duk wanda ya ke ƙasar nan musamman a nan Arewa yana da gudunmawar da mahaifinsu Sheikh Ishaƙa Rabiu Khadimul ƙur'an ya bayar a lokacin rayuwarsa, don haka suka ɗora a inda ya tsaya musamman wajen taimakawa almajirai da sauran mabuƙata, kasancewar su ma almajirai ne masu girmama Alƙur'ani da…
Read More
Ba makarantu kariya da hana lalata kayan gwamnati na daga cikin aikinmu – NSCDC Kano

Ba makarantu kariya da hana lalata kayan gwamnati na daga cikin aikinmu – NSCDC Kano

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Shugaban rundunar Cibil Difens na Jihar Kano, Muhammad Lawal Falala ya bayyana cewa hukumarsu bisa umarnin Gwamnatin Tarayya na bai wa makarantun ƙasar nan kariya ta fuskar wayar da kai ga shugabanin makarantu, malamai da ɗalibai, wanda ya ce ita ma Kano ba a barta a baya ba wajen bada wannan kariyar tsaro na musamman ga makarantun jihar, inda ya ce wannan na daga cikin aikin rundunar ta NSCDC na ba fararen hula kariya da hana lalata da satar kayayyakin amfanin al'umma na gwamnati da dai sauransu. SC Lawal Muhammad Falala ya bayyana haka ne…
Read More
Muna farin ciki da yadda Sarkin Gaya ke tafiyar da al’amuran sarauta – Talban Gaya

Muna farin ciki da yadda Sarkin Gaya ke tafiyar da al’amuran sarauta – Talban Gaya

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Al'ummar Gaya na alfahari da nuna soyayya da biyayya ga mai martaba Sarkin Gaya Dakta Aliyu Ibrahim Abdulƙadir, musamman ganin yadda yake da dattaku da kuma miƙa lamarinsa ga Allah wanda wannan abin koyi ne ga shugabanni da sauran al'umma wanda babu wani abu dake jawo alkairi da zaman lafiya kamar haƙuri da kyakyawan shugabanci a tsakani, don haka al'ummar gaya na farin ciki da alfahari da irin mulkin mai martaba Sarkin Gaya kamar yadda Talban Gaya Alhaji Kamal, ya bayana a wannan lokaci.   Shi ma shugaban ma'aikata na ƙaramar hukumar Gaya ya ce yadda…
Read More
Obasanjo ba shugaban da za a yi koyi da shi ba ne – Fadar Shugaban ƙasa

Obasanjo ba shugaban da za a yi koyi da shi ba ne – Fadar Shugaban ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Fadar gwamnatin Nijeriya ta ce tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ba shugaba ba ne da za a yi koyi da shi a fannin gudanar da mulki da ma sauran harkokin shugabanci. Gwamnatin ta yi wa Obasanjo wannan kakkausar suka ne a martanin da ta mayar masa na sukar gwamnatin Bola Tinubu da Muhammadu Buhari da ya yi a wata lacca da ya gabatar ta tunawa da Marigayi Chinua Achebe a Jami'ar Yale ta Amurka. A wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasar shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru Bayo Onanuga ya…
Read More
Har yanzu ba mu ɗauki matsaya kan ƙudurin harajin Tinubu ba – Kakakin Majalisa

Har yanzu ba mu ɗauki matsaya kan ƙudurin harajin Tinubu ba – Kakakin Majalisa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban majalisar wakilan Nijeriya, Abbas Tajudeen, ya ce har yanzu majalisar ba ta ɗauki matsaya ba a kan sabon ƙudirin haraji na gwamnatin Tinubu. Ya bayyana hakan ne kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a jawabinsa na buɗe tattauna kan sabon ƙudirin harajin a zauren majalisar da ke Abuja a ranar Litinin. Sai dai kamar yadda jaridar Manhaja ta ruwaito, ya ce majalisar za ta yi aikin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata na tantancewa duk tanadin ƙudurin tare da yin gyara inda ya zama wajibi. A watan da ya gabata ne…
Read More
Mutum uku ke magana da yawuna – Tinubu

Mutum uku ke magana da yawuna – Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Fadar Shugaban Nijeriya ta ce Shugaba Tinubu ya yi garambawul game da ayyukan jami'ansa da ya naɗa a sashen hulɗa da kafafen yaɗa labaru, domin bunƙasa ɓangaren. Wata sanarwa da mai taimaka wa Shugaba Tinubu kan yaɗa labaru da tsare-tsare, Bayo Onanuga ya fitar ta ce a yanzu dukkanin mutane uku da aka naɗa a muƙaman yaɗa labaru za su zamo masu magana da yawun shugaban ƙasa. Sai dai sanarwar ta ce Mista Sunday Dare a yanzu shi ne mai bai wa shugaban ƙasar shawara na musamman kan kafafen yaɗa labaru da hulɗa da…
Read More