Labarai

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sojojin Nijeriya sun halaka mayaƙan Boko Haram 30 a yayin artabu da mayaƙan Boko Haram da suka kai musu hari a Jihar Borno. Kakakin Rundunar Tsaro ta Nijeriya, Manjo-Janar Edward Buba, ya ce sojojin sun aika mayaƙan na Boko Haram lahira tare da ƙwato malamansu ne a yankin Gubio, inda dakarun ke aikin wanzar da zaman lafiya. Sai dai ya ce an yi rashin sa’a mutum biyar daga cikin sojoji sun kwanta dama, wasu 10 sun samu raunuka a yayin da ake ci gaba da neman wasu huɗu da ba a gani ba bayan…
Read More
Cibiyar horas da malaman makaranta ta NTI ta samu izinin ba da shaidar digiri

Cibiyar horas da malaman makaranta ta NTI ta samu izinin ba da shaidar digiri

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kwalejin Horas da Malaman Makaranta (NTI) ta samu izinin ba da shaidar digiri a fannin koyo da koyarwa na ilimi-daga-nesa kamar yadda darakta-janar Farfesa Musa Garba-Maitafsir, mai barin gado, ya bayyana. Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN) ta rawaito a ranar Litinin a Kaduna a yayin da yake miƙa ragamar jagorancin kwalejin ga mai maye gurbinsa, Farfesa Sa’adiyya Sani-Daura. Garba-Maitafsir ya ce, shugabar na karɓar shugabanci ne a lokacin da komai ya daidaita idan aka kwatanta da lokacin da ya karɓi jagorancin kwalejin. Ya ce ya karɓi kwalejin ne a lokaci mai wahala, amma…
Read More
Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50 a Kaduna

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50 a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jami’an hukumar tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) sun aika mayaƙan Boko Haram kimanin 50 lahira a yayin musayar wuta a Jihar Kaduna. Hukumar NSCDC ta bayyana cewa mayaƙan na Boko Haram sun gamu da ajalinsu ne bayan sun kai wa jami’anta harin kwanton ɓauna ranar Litinin. Kakakin Hukumar NSCDC, Babawale Afolabi, ya ce jami’an hukumar sun yi arangama da mayaƙan ne a lokacin da suke zagayen sintirin kare babban layin wutar lantarki da ya taso daga  yankin Shiroro ne a Jihar Neja. “Mayaƙan Boko Haram kimanin 200 ɗauke da muggan makamai ne suka kai…
Read More
Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da aikin hanyar Shargalle zuwa Ingawa

Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da aikin hanyar Shargalle zuwa Ingawa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina. Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da fara aikin hanyar Shargalle zuwaIngawa, inda ya shaida cewa, shimfiɗa sabuwar kwalta za a yi ba gyare-gyare ba. Ya bayyana aikin hanyar mai tsawon kilomita 39 zai ci kuɗi Naira biliyan 3.8 kuma ana sa ran nan da shekara ɗaya za a kammala aikin hanyar. Gwamnan ya sanar da bada kashi arba'in na kuɗin aikin ga ɗan kwangilar. Akan haka ne ya jawo hankalin al'ummar yankin da su sa idon akan yadda ake aikin hanyar da zarar kun ga hankalin ku bai kwanta da aikin ba ku sanar da…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotun Ƙoli ta soke dokar caca ta Lottery

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Juma'a ne Kotun Ƙoli ta soke Dokar Caca ta Lottery da Majalisa ta samar a shekarar 2005. Kotun, cikin wani hukunci da tawagar Alƙalai bakwai suka jagoranta, ta ce Majalisar ba ta da damar kafa doka game da lamuran da suka shafi Lottery da wasu nau'ukan caca. Ta ce ire-iren waɗannan damanmakin majalisun dokokin jihohi kaɗai ke da alhakin kafa su. Cikin hukuncin nata wanda Mai Shari'a, Mohammed Idris ya gabatar, kotun ta yi umarni cewa daga yanzu ba za a cigaba da yin aiki da dokar ba a duka jihohin Nijeriya sai dai…
Read More

Gwamnatin Tarayya da jihohi za su yi matsaya kan kafa ƴan sandan jihohi makon gobe

Daga BELLO A. BABAJI A sati mai zuwa ne Gwamnatin Tarayya da gwamnoni za su yi hukunci game da samar da ƴan sandan jihohi. Gwamnan Jihar Bayelsa, Duoye Diri ya bayyana hakan wa manema labarai a Fadar shugaban ƙasa dake Abuja, bayan kammala taron Majalisar Tattalin Arziƙin Ƙasa (NEC). Ya ce, Majalisar ta bai wa jihohin Adamawa da Kebbi da Kwara da kuma Abuja mako guda (28 ga watan Nuwamba) su gabatar da matsayarsu game da lamarin. Diri ya ce a yayin zaman majalisar na mako mai zuwa ne, za a cimma matsaya. A ranar 15 ga watan Fabrairun shekarar…
Read More
Kwartanci: ‘Yan sanda sun cafke Nasir Buba da ke zargin Kwamishinan Jigawa da mu’amala da matarsa

Kwartanci: ‘Yan sanda sun cafke Nasir Buba da ke zargin Kwamishinan Jigawa da mu’amala da matarsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kwana guda  bayan Kotun Shari’ar Musulunci ta wanke Kwamishinan Jigawa Auwal Sankara, daga zargin yin lalata da matar aure, 'yan sanda a Kano sun kama Nasir Buba, tsohon mijin wacce ake zargin tana soyayya da kwamishinan, Tasleem Baba-Nabegu. An kama Buba ne a ƙofar ofishin lauyansa a ranar Talata. Blueprint Manhaja ta rawaito cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano kwanan nan ta kama Sankara ta tsare shi bayan Buba ya kai ƙarar cewa kwamishinan na neman matarsa. Buba ya shigar da ƙara a kotun Shari’a bisa zargin. Sai dai a zaman kotun na ranar…
Read More
Farfesa Sa’adatu Liman ta yaba wa Gwamna Sule kan gina hanyar kilomita 4.5 a cikin Jami’ar NSUK

Farfesa Sa’adatu Liman ta yaba wa Gwamna Sule kan gina hanyar kilomita 4.5 a cikin Jami’ar NSUK

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Shugabar Babbar Jami’ar Jihar Nasarawa dake garin Keffi, hedikwatar ƙaramar hukumar Keffi a jihar Nasarawa, Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta yaba wa gwamnan jihar, Injiniya Abdullahi Sule dangane da kwangilar gina sabbin hanyoyi da kwalbati irin na zamani na kilomita 4 da rabi a cikin jami’ar ta jihar da ake yi a yanzu, inda ta ce tabbas idan aka kammala aikin zai je nesa ba kusa ba wajen inganta harkokin karatu da zirga-zirgar ɗalibai da malamai a jami’ar baki ɗaya. Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta yabi gwamnan ne a lokacin da take tattauna da…
Read More
Hamza Almustapha na da ingancin da zai iya kyakkyawan jagoranci a ƙasar nan – Mustapha Ɗahiru 

Hamza Almustapha na da ingancin da zai iya kyakkyawan jagoranci a ƙasar nan – Mustapha Ɗahiru 

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana Manjo Hamza Almustapha da cewa mutum ne da yake da inganci da son cigaban ƙasa da zai iya samar da kyakkyawan jagoranci da fitar da al'ummar ƙasar nan daga yanayi na ƙuncin rayuwa. Shugaban Network for Better da ke fafutukar ganin Manjo Hamza Almustapha ya zama shugaban ƙasar Nijeriya reshen jihar Kano, Mustapha ɗahiru ne ya bayyana hakan da yake zantawa da manema labarai. Ya ce su suna da yaƙinin Almustapha zai iya kawo sauyi a halin da ake ciki a ƙasar nan domin waɗanda suke da tunani ada na ganin ba zai…
Read More
Gwamnoni sun yi wa ’yan majalisa barazana kan goyon bayan ƙudirin haraji

Gwamnoni sun yi wa ’yan majalisa barazana kan goyon bayan ƙudirin haraji

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Philip Agbese, ya bayyana cewa wasu gwamnonin jihohi na barazanar hana ’yan majalisar tarayya tikitin takara a zaɓen 2027 idan har ba su janye goyon bayansu ga ƙudirin gyara haraji na shugaban ƙasa Bola Tinubu ba a yanzu da ke gaban majalisar ƙasa. Agbese ya kuma bayyana cewa a ranar Litinin ’yan majalisar za su tattauna da shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan gyaran kasafin kuɗi da haraji, Taiwo Oyedele da wasu fitattun masana harkokin haraji kan ƙudirin. Idan za a iya tunawa, a ranar 3 ga Satumba, 2024, shugaban ƙasar ya miƙa…
Read More