Labarai

Ɗangote da IPMAN sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar lita miliyan 240 na cinikin fetur duk shekara

Ɗangote da IPMAN sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar lita miliyan 240 na cinikin fetur duk shekara

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Matatar mai ta Ɗangote ta yi tayin samar da lita miliyan 60 na man fetur ga ƙungiyar Dillalan Man Fetur mai zaman kanta ta Nijeriya a duk mako, wanda ke nufin lita miliyan 240 a kowane wata. Wannan jarida ta tattaro daga ƙungiyar cewa matatar ta amince da bai wa ‘yan ƙungiyar IPMAN lita miliyan 60 na fetur a mako-mako, ya danganta da irin tallafin da ake samu. Hakan ya zo ne yayin da aka tattaro cewa matatar mai da ke Lekki ta dala biliyan 20 na da nufin tara biliyoyin daloli don shigo da ɗanyen…
Read More
Nijeriya ta gaza a ƙarƙashin ‘Emilokan’, Obasanjo ya yi wa Tinubu ba’a

Nijeriya ta gaza a ƙarƙashin ‘Emilokan’, Obasanjo ya yi wa Tinubu ba’a

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya ce gazawar gwamnatin Nijeriya a ƙarƙashin mulkin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu “tabbas ce kuma a bayyane ta ke ga kowane mai son gaskiya ya gani.” Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Kehinde Akinyemi ya fitar, inda ta ce Obasanjo ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a taron shugabannin Chinua Achebe da aka gudanar a Jami’ar Yale, New Haɓen, Connecticut, Amurka. "Kamar yadda duniya ke gani, halin da Nijeriya ke ciki ya yi ƙamari," in ji…
Read More
Cibiyar bincike da ƙere-ƙere ta Jami’ar NSUK ta yi taron bajekolin 2024

Cibiyar bincike da ƙere-ƙere ta Jami’ar NSUK ta yi taron bajekolin 2024

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Cibiyar bincike na musamman da ƙere-ƙere da kuma kasuwanci wato Directorate of Research, Innovation and Enterprise COAAPBAS a Turance na babbar jami’ar jihar Nasarawa ta gudanar da babban taron bajekolin kayayyakin bincikenta karo na 8. Babban taron wadda ake gudanar a jami’ar shekara-shekara an gudanar da na bana shekarar 2024 ne a jami’ar dake garin Keffi a makon da ake ciki. Da take jawabi a matsayin ta na babbar mai makokin baki Shugabar Jami’ar Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta bayyana muhimmancin taron wadda ta ce yana bai da damar nuna basirar masu bincike wajen…
Read More
Ku tashi ku nema wa yankinku mafita – Shawarar Tinubu ga jagororin Arewa

Ku tashi ku nema wa yankinku mafita – Shawarar Tinubu ga jagororin Arewa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya buƙaci shugabannin Arewa a ranar Talata da su tashi tsaye wajen nemo hanyoyin da za su warware matsalolin da ke damun yankin. Tinubu wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilta a yayin wani taron tattaunawa kan bunƙasa rayuwar matasan Arewacin Nijeriya wadda gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya, ya ce akwai buƙatar shugabanni su tashi tsaye domin nema wa yankin mafita. Taron dai an yi masa take da: ‘Tallafawa ba baya: dabaru masu ɗorewa wajen bunƙasa rayuwar matasan Arewacin Nijeriya’. Ya ce abubuwan akhairin da…
Read More
Mai jego ta kuɓuta a hannun ɓarayin daji bayan haihuwar tagwaye 

Mai jego ta kuɓuta a hannun ɓarayin daji bayan haihuwar tagwaye 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata mata mai suna Maimuna da ke da zama a garin Lambata na ƙaramar Hukumar Gurara a Jihar Neja ta samu kuɓuta daga hannun wasu da suka yi garkuwa da ita bayan ta haifi tagwaye a hannunsu. Matar kamar yadda Manhaja ta samu labari ta hau mota ne daga garin Lambata a kusa da ƙauyen nasu a ranar Alhamis ta makon jiya zuwa Babban Asibitin garin Suleja don yin awu, bayan ta lura da rashin motsawar cikinta. Ta ce an yi mata awun sannan aka buƙaci ta sake komawa asibitin washegari, ranar Juma’a da…
Read More
Barista Abba Hikima ya maka Wike a kotu kan kamen mabaratan Abuja

Barista Abba Hikima ya maka Wike a kotu kan kamen mabaratan Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Fitaccen lauya a Kano, Barista Abba Hikima, ya maka Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike a kotu, kan kamen mabarata da nakasassu da masu talla a kan titunan Abuja. Abba Hikima ya shigar da ƙarar ne a ranar Laraba, kimanin mako biyu bayan hukumar Birnin Tarayya ta yi kame tare da tsare mabarata da nakasassu da masu talla a kan titunan Birnin Abuja. Abba Hikima wanda ɗan gwagwarmayar ƙare haƙƙin ɗan Adam ne, yana zargin Ministan Abuja da jami’ansa da cin zarafi da ƙuntatawa da kuma tauye haƙƙoƙi da cin zalin mabaratan da nakasassun…
Read More
Matatar Ɗangote ta koma sayen ɗanyen mai Amurka

Matatar Ɗangote ta koma sayen ɗanyen mai Amurka

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Matatar man Ɗangote ta ɗora daga inda ta tsaya wajen sayen ɗanyen mai daga ƙasar Amurka a ci gaba da ƙoƙarin da ta ke yi na samar da wadataccen mai da kuma inganta aikin tace manta. Lamarin ya zo ne bayan dakatar da sayen ɗanyen mai daga ƙasashen ƙetare na tsawon watanni uku, inda aka mayar da hankali wajen sayen na cikin gida Nijeriya. Wani rahoto da Bloomberg ta fitar a ranar Larabar da ta gabata ya ce, za a kai gangar ɗanyen mai ta WTI Midland miliyan biyu daga Cheɓron Corp zuwa matatar Dangote a…
Read More
Tinubu na shirin naɗa sabbin jakadun Nijeriya

Tinubu na shirin naɗa sabbin jakadun Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta fara shirin tura jami’an ofishin jakadanci zuwa ofisoshin diflomasiyya a duniya kafin a naɗa sabbin jakadu. Shekara guda da wata ɗaya kenan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dawo da jakadun Nijeriya gida. Tun bayan dawo da su ranar 2 ga Satumba, 2023, ofisoshin jakadancin Nijeriya 109 a ƙasashen waje sun kasance babu cikakken wakilci na jakadanci.  Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya ce jakadun sun yi aiki ne bisa umarnin shugaban ƙasa a cikin ƙasashen da suka karɓi baƙuncinsu kuma "ikon shugaban ƙasa ne ya aika ko kiran su daga kowace…
Read More
Ta’addanci: An kama jagoran IPOB a Finland

Ta’addanci: An kama jagoran IPOB a Finland

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jagoran haramtacciyar ƙungiyar IPOB ta Kudu maso Kudancin Nijeriya, Simon Ekpa ya shiga hannu a ƙasar Finland bisa zarginsa da aikata laifukan ta'addanci. Kafofin watsa labarai na ƙasar Finladn sun ruwaito cewa wata kotu a yankin Päijät-Häme ta tura Ekpa gidan yari bisa zarginsa da ingiza mutane su aikata laifuka. Kotun ta ce Simon Ekpa yana yaɗa farfagandar a ware a kafofin sadarwa. Bayan Ekpa kuma, kotun ta ce a kamo mata wasu mutum huɗu bisa zarginsu da laifukan ta'addancin. Ekpa, wanda ɗan Nijeriya ne, wanda yake da izinin zama ɗan ƙasar Finland, an…
Read More
Majalisar Wakilai ta watsar da ƙudirin wa’adin shekara shida ga Shugaban ƙasa da gwamnoni

Majalisar Wakilai ta watsar da ƙudirin wa’adin shekara shida ga Shugaban ƙasa da gwamnoni

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Wakilai ta ƙasa ta ƙi amincewa da karatu na biyu na ƙudirin da ke neman samar da wa’adin shugabancin shekaru shida kacal ga Shugaban ƙasa da gwamnoni. Majalisar ta yi watsi da ƙudirin ne yayin zamanta na ranar Alhamis. ƙudirin dai an gabatar da shi ne ƙarƙashin jagorancin ɗan majalisa Ikenga Imo Ugochinyere tare da sauran mambobi 33. An gabatar da ƙudirin domin karatu na biyu ne daga babbar mai ɗaukar nauyinsa, Ugochinyere, sannan aka goyi bayan hakan. Sai dai, yayin da Kakakin Majalisar, Abbas Tajuddeen, ya miƙa ƙudirin don kaɗa ƙuri’a ta…
Read More