Labarai

Majalisar Dattawa ta sahale wa Tinubu karɓo rancen tiriliyan N1.77

Majalisar Dattawa ta sahale wa Tinubu karɓo rancen tiriliyan N1.77

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Dattawa ta amince Shugaba Bola Tinubu ya ranto naira tiriliyan 1.77 kimanin dala biliyan 2.2 daga ƙetare. Matakin dai ya biyo bayan nazari tare da amincewa da rahoton Kwamitin Majalisar kan basussukan cikin gida da waje, wanda Sanata Aliyu Wamakko da ke wakiltar Sakkwato ta Arewa ya jagoranta. A ranar Talata ce Shugaba Tinubu ya aike wa Majalisar Dokokin Tarayya wasiƙar neman sahalewa ya ranto bashin Naira tiriliyan 1.77 a matsayin sabon tsarin rancen aiwatar da Dokar Kasafin Kuɗin bana. Wasiƙar Shugaban ta ce za a yi amfani da rancen wajen cike giɓin…
Read More

Gwamnan Katsina ya ƙaddamar da makarantun sakandire 75 da AGILE ta gina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Da ya ke jawabi a wajen taron, shugaban Tsarin Ilimin bai ɗaya na jihar Dakta Kabir Magaji, ya bayyana shirin na AGILE a matsayin shiri da ke bada gagarumar gudunmuwa wajen cigaban ilimi a Jihar Katsina. Ya ce cikin makarantun sakandiren guda 75, 45 daga cikin su ƙananan sakandire ne (junior section), sauran kuma manyan sakandire (Senior). A nata jawabin, Kwamishinar Ilimi ta jihar, Hajiya Zainab Musa Musawa, ta bayyana ƙaddamar da buɗe makarantun a matsayin wani abin tarihi a fannin ilimi a Katsina, ta na mai cewa shirin na AGILE ba ƙaramin cigaba ya…
Read More

Gwamnatin Katsina ta jinjina wa sojojin sama kan yaƙi da ta’adanci

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta jinjina wa Rundunar sojojin sama bisa namijin ƙoƙari da suka yi wajen daƙushe ƴan ta'adda a garin Ruwan Godiya da ke ƙaramar hukumar Faskari. Rundunar sojojin da aka fi sani da 'FARAUTAR MUJIYA', sun kai hare-hare ne a maɓoyar ƴan ta'adda a garin inda suka lalata sansanin ƴan ta'addan da kashe wasu da dama daga cikin su. Kwamishinan Cikin gida da Tsaro, Dakta Nasiru Mu'azu Ɗan-Musa ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a inda ya ce ƙoƙarin da jarumta da sojojin suka nuna za su ƙara kwantar wa…
Read More

Majalisar Tattalin Arziƙin Ƙasa ta ɗauki matakan magance matsalolin lantarki a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI A taronta karo na 146, Majalisar Tattalin Arziƙin Ƙasa, NEC ta ƙudiri aniyar haɓaka sabbin dabarun hana faɗuwar turakun wutar lantarki da ake fuskanta a Nijeriya. Majalisar, wadda ke ƙarƙashin jagorancin Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ta fitar da jaddawalin shawarwarin da suka haɗa da samar da wani kwamitin bibiyar gyaran wutar a mataki na ƙasa, ƙarƙashin jagorancin gwamnan Jihar Cross-River, Bassey Otu. Wata takarda da Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin rediyon da yaɗa labarai ta ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Rahama Abdulmajid ta fitar, ta ce sabon kwamitin zai mayar da hankali ne wajen…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: ACF ta dakatar da shugabanta kan tsokaci game da shugabancin 2027

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar Mashawarta ta Arewa, ACF, ta dakatar da shugabanta, Mista Mamman Mike Osuman bisa kalamansa na cewa ƴan Arewa za su zaɓi wanda ya zo daga yankin a madadin Shugaba Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. ACF ta caccaki kalaman shugaban a inda ta ce an fitar da su ne ba tare da yin shawara ba, don haka ba su wakilci matsayar ƙungiyar ba. Acikin wata takarda da shugaban Tawagar Amintattun ƙungiyar, Alhaji Bashir Muhammad Ɗalhatu da Sakatarenta, Alhaji Murtala Aliyu suka sanya wa hannu, sun tabbatar da cewa, Mista Osuman ya faɗi kalaman ne…
Read More
Kotun ICC ta bayar da sammacin kamo Netanyahu da Gallant bisa zargin aikata laifukan yaƙi

Kotun ICC ta bayar da sammacin kamo Netanyahu da Gallant bisa zargin aikata laifukan yaƙi

Daga USMAN KAROFI A ranar 21 ga Nuwamba, 2024, kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) ta fitar da sammacin kama Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da tsohon Ministan Tsaro, Yoav Gallant bisa zargin aikata laifukan yaƙi a Gaza. ICC ta bayyana cewa akwai hujjoji masu ƙarfi da ke nuna Netanyahu da Gallant sun aikata laifukan yaƙi. Kotun ta ce ba lallai ne Isra'ila ta amince da ikon kotun ba kafin gudanar da bincike. A yayin haka, Amurka ta sake amfani da karfin ikon ta karo na huɗu wajen daƙile ƙudirin kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke neman kawo…
Read More
Yadda yara suka jagoranci zaman Majalisar Dokokin Kano

Yadda yara suka jagoranci zaman Majalisar Dokokin Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Majalisar ɗinkin duniya ta ware ranar 20 ga watan Nuwanba na kowace shekara a matsayin ranar yara ta duniya. Yaran da suka fito daga makarantu dadan-daban na Jihar Kano sun jagoranci zaman majalisar dokokin Kano wanda asusun kula da ƙananan yara na majalisar ɗinkin duniya UNICEF reshen jihar Kano ya ɗauki nauyi, taken ranar ta bana shi ne "Kowane yaro yana da yanci" A yayin zaman majalisar, a ranar Laraba, an gabatar da ƙudirorin da dama waɗanda suka shafi ƙananan yaran da ya shafi ilimi, lafiya, aikin gona da dai sauransu. Wani yaro mai suna…
Read More

Tsohon Babban Daraktan Tashar Ruwan Nijeriya, Zubairu Ɗambatta ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon Babban Daraktan Hukumar Tashar Jiragen ruwa ta Nijeriya (NPA), Alhaji Zubairu AbdulHamid Ɗambatta ya rasu. Marigayin kuma shi ne mai bada shawara na musamman kan harkar man fetur ga tsohon shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo. Ɗaya daga cikin iyalan gidan marigayin ya shaida wa 'News Point Nigeria' cewa, Ɗambatta ya rasu ne a Kano ya na da shekaru 75, bayan fama da wani gajeren rashin lafiya. Ya kuma bar mata ɗaya da ƴaƴa dajikoki. An yi jana'izar mamacin ne a masallacin Usman Bin Affan dake ƙofar Gadon ƙaya, da misalin ƙarfe 1 na rana. Da…
Read More
Ƙaramar Hukumar Jahun ta kashe miliyan N60 don dawo da lantarki

Ƙaramar Hukumar Jahun ta kashe miliyan N60 don dawo da lantarki

Daga UMAR AKILU MAJERI Dutse Bayan shafe shekaru takwas cikin duhu da ƙaramar hukumar Jahun tayi na rashin hasken wutar lantarki sakamakon sace kayan wutar lantarki da ɓarayi sukayi a yankin, sabon shugaban ƙaramar hukumar ta Jahun Hon. Jamilu Muhammed Ɗan malam ya kashe kimanin naira miliyan 60 domin ceto al,ummar ƙaramar hukumar daga kwana cikin duhu babu wutar lantarki. Shugaban ƙaramar hukumar ya faɗi hakane a wata ganawa da ya yi da wakilinmu na Jihar jigawa a ofishinsa da ke Jahun ,ya kuma nuna damuwarsa a kan yadda yanzu wasu unguwanni suke kwana a cikin duhu a garin na…
Read More
Maraɗin Katsina kuma Hakimin Kurfi, Alhaji Ahmadu Kurfi ya rasu

Maraɗin Katsina kuma Hakimin Kurfi, Alhaji Ahmadu Kurfi ya rasu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Tsohon sakataren hukumar zaɓe na kasa maraɗin Katsina kuma Hakimin kurfi ya rasu. Ya rasu a babban asibitin gwamnatin tarayya da ke Katsina yana da shekara 90. Marigayi Ahmadu kurfi ya taba riƙe sakataren hukumar zaɓe na ƙasa(FEDECO) a shekarar 1999. Kafin nan marigayin ya fara aiki a mulkin Sardauna Ahmadu Bello a 1958 . Ya kuma riƙe muƙamin babban sakatare a ma'aikatun gwamnatin tarayya guda uku kafin ya ajiye aiki a shekarar 1986. Daga nan ne ya sami sarauta maraɗin Katsina Hakimin kurfi.
Read More