21
Nov
Daga SANUSI MUHAMMAD Gusau Ƙungiyar iyayen ɗaliban da ke karatu a Jami'ar Ƙasa da Ƙasa da ke Ƙasar Cyprus Yan asalin jihar Zamfara, sunyi kira ga gwamnatin jihar Zamfara da ta gaggauta duba halin da ‘ya’yansu 88 ke ciki don ceto su daga halin kuncin rayuwa da suke a ciki a Ƙasar ta Cyprus. Ɗaliban suna karatun kwasa-kwasai daban-daban ne a Ƙasar Cyprus ƙarƙashin Jami'ar Ƙasa da Ƙasa Nicosia waɗanda gwamnatin Jihar ta tura tun gwamnatin da ta gabata ta Ƙaramin ministan tsaro Bello Muhammad Matawalle. Shugaban Ƙungiyar Ambasada, Ibrahim Tudu ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai…
