Labarai

Matatar man Ɗangote ta fara safarar mai zuwa ƙasashen Afirka ta Yamma

Matatar man Ɗangote ta fara safarar mai zuwa ƙasashen Afirka ta Yamma

Daga USMAN KAROFI Matatar man fetur ta Ɗangote ta fara fitar da mai da aka tace zuwa ƙasashen yammacin Afirka, abin da ke nuna yiwuwar wannan matata za ta girgiza kasuwar mai a yankin. Rahoton Bloomberg a ranar Talata ya tabbatar da hakan, inda ya ambaci bayanai daga Vortexa, Kpler, Precise Intelligence da kuma dandalin bibiyar jiragen ruwa. Rahoton ya bayyana cewa wata tanka ta ɗauki jirgin man fetur daga matatar Ɗangote ta fitar da shi zuwa gaɓar ruwan Togo. Rahoton ya bayyana cewa CL Jane Austen ya ɗauki ganga fiye da 300,000 daga Ɗangote kuma ya yi tafiya zuwa…
Read More

Sojoji sun casa ma’aurata bisa kere su yayin tuƙi a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Talata ne wata ɗaukar bidiyo ta nuna yadda wasu sojojin Nijeriya waɗanda acikin su har da Manjo-Janar suka riƙa lakaɗawa wani magidanci da matarsa duka a yankin Gwarimpa dake birnin tarayya Abuja. Lamarin ya auku ne a lokacin da ma'auratan masu suna Mista Vershima Mker da Misis Lami Jennifer Iorvihi ke cikin motarsu. An gano cewa an casa mijin ne sakamakon kere motar sojojin da abin hawan na su ya yi a lokacin da su ke tuƙi. A lokacin da su ke bada ba'asi game da batun, ma'auratan sun ce wani mai suna Janar…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta tallafa wa manoman rani a jihar

Gwamnatin Katsina za ta tallafa wa manoman rani a jihar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban hukumar kula da noman rani ta jiha, Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir ya ce gwamnatin Dikko Raɗɗa ta sha alwashin tallafawa manoman rani domin samar da abinci a faɗin jihar. Abdulkadir Andaje ya faɗi haka ne a yayin da ya ke gudanar da taron masu ruwa da tsaki a fanin noman rani,yace taron zai taimaka wajen samun adadin masu noman rani a jihar. "Hukumar ta shirya wannan taro domin ta sami cikakken adadin masu noman rani a jihar "Abdulkarim Nasir ya ce . Hakan zai ba gwamnatin jihar damar tattara bayanan manoman rani da zai…
Read More

Taron G20: Tinubu ya goyi bayan ƙaddamar da taron dangi akan yunwa da talauci

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Tinubu ya jinjina wa tsarin samar da haɗin-gwiwa tsakanin ƙasashe wajen murƙushe yunwa da talauci da Shugaba Luiz Inácio Lula da Silva na ƙasa Brazil ya bijiro da shi. Tinubu ya bayyana hakan a matsayin abu mai muhimmanci ga ƙoƙarin yaƙi da yunwa da talauci a faɗin duniya da ake yi. Ya bayyana hakan ne a yayin taron ƙasashen G20 karo na 19 da ke gudana a Rio de Janeiro na Brazil, ya na mai cewa hakan babban mataki ne na warware wasu daga cikin manyan matsalolin da ake fuskanta a duniya. Ya ce, za…
Read More
Mutum 25 sun mutu sanadiyar kwalara a Sokoto

Mutum 25 sun mutu sanadiyar kwalara a Sokoto

Aƙalla mutane 25 ne suka mutu, yayin da wasu da dama ke kwance a asibiti sakamakon ɓarkewar cutar kwalara a ƙananan hukumomin Sokoto North, Silame da Kware a Jihar Sokoto. Kwamishinar Lafiya ta Jihar, Asabe Balarabe, ta bayyana hakan ga manema labarai a Sokoto, inda ta ce a halin yanzu, jihar tana kula da mutane 15 da aka tabbatar suna ɗauke da cutar a yankunan Sokoto North, Silame da Kware. A cewar Balarabe, an gano waɗannan mutane 15 da ke ɗauke da cutar ne ta hanyar gwaji. Kuma an tabbatar da cewa suna ɗauke da cutar kwalara. Ta kuma bayyana…
Read More
Tarayyar Turai da Birtaniya sun ƙaƙaba sabbin takunkumi ga Iran saboda goyon bayan Rasha

Tarayyar Turai da Birtaniya sun ƙaƙaba sabbin takunkumi ga Iran saboda goyon bayan Rasha

Daga USMAN KAROFI Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) da Birtaniya (UK) sun ƙara ƙaƙaba wa Iran sabbin takunkumi saboda zargin da ake mata na goyon bayan Rasha a yaƙin da take yi da Ukraine. Sabbin matakan sun shafi manyan tashoshin jiragen ruwa na Iran, kamfanonin jigila da kuma wasu cibiyoyin gwamnati da ake zargi da taimaka wa Rasha wajen samun jiragen yaƙi marasa matuki da makamai masu linzami. Wannan takunkumi ya hana Iran sayarwa ko samar da kayayyakin da ake amfani da su wajen ƙera makamai ga Rasha. Sabbin matakan da EU ta ɗauka sun haɗa da dakatar da duk wani…
Read More

Tinubu ya yi kwaskwarima ga tawagar yaɗa labaransa

Daga BELLO A BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kwaskwarima wa tawagar da ke yaɗa labaran ofishinsa don inganta harkokin ɓangaren a gwamnatinsa. Ya ce daga yanzu, Bayo Onanuga da Sunday Dare da kuma Daniel Bwala za su riƙa aiki tare a matsayin masu magana da yawun gwamnatin. Cikin wata takarda da Onanuga ya fitar a ranar Talata, ya ce Tinubu ya yanke hakan ne don tabbatar da isar da saƙon gwamanti game da tsare-tsare, matakai da sauran aikace-aikace akan lokaci da inganci. Shugaba Tinubu ya yi nuni da muhimmanci yin aiki hannu-da-hannu a lamuran da suka shafi ofishin…
Read More
Shugaban ƙaramar hukuma ya naɗa mataimaka na musamman kan doya, yalo da yaji

Shugaban ƙaramar hukuma ya naɗa mataimaka na musamman kan doya, yalo da yaji

Daga USMAN KAROFI Shugaban ƙaramar hukumar Igbo Etiti da ke Jihar Enugu, Eric Odo, ya amince da naɗin wani mashawarci na musamman kan har harkokin noma, musamman akan yaji da yalo. A cewar naɗin da aka yi, an naɗa Nwodo Everestus Ugonna domin ya kasance mai ba da shawara kan harkar noma, tare da taimakawa a fannin yalo da yaji. Haka kuma, an naɗa Ezeugwu Frederick Ogbonna a matsayin mai ba da shawara kan harkar noma, musamman kan harkokin doya. A cikin takardar naɗin su wacce aka sanya hannu ranar 1 ga Nuwamba, an umurci Nwodo da Ezeugwu su je…
Read More
Gwamna Lawal ya ƙaddamar da gina sabuwar tashar motoci ta zamani a Gusau

Gwamna Lawal ya ƙaddamar da gina sabuwar tashar motoci ta zamani a Gusau

Daga USMAN KAROFI Gwamna Dauda Lawal ya sake tabbatar da ƙudurin gwamnatinsa na samar da ayyukan yi ga al'ummar da ke dogaro da harkokin tasha. A ranar Litinin, gwamnan ya ƙaddamar da gina sabuwqr tashar motoci ta zamani a babban titin Sokoto-Zaria da ke Gusau, babban birnin jihar kamar yadda Mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Bala Idris ya fitar. An ba kamfanin Fieldmark Construction LTD kwangilar aikin, wanda zai ƙunshi wuraren ajiye motoci masu faɗi, wuraren hutawa ga direbobi, tsare-tsaren tsaro na zamani, da tsarin tikiti mai sauƙi domin inganta gudanar da ayyuka. Da yake ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya…
Read More

Hizbullah ta tabbatar da mutuwar kakakinta a harin Beirut

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar Hizbullahi ta tabbatar da mutuwar mai magana da yawunta, Muhammad Afif a wani hari da Isra'ira ta kai a Beirut. Afif wani jigo ne a harkokin jaridar Hizbullahi, wadda ƙungiya ce ta ƙasar Iran, kamar yadda ta wallafa a kafar Telegram. Baya ga kashe jagoran ƙungiyar, Afif shi ne sanannen mutum na biyu da aka kashe wanda kwanan nan ya jagoranci wani taron manema labarai. Haka nan Afif ya kasance na hannun daman tsohon babban sakataren ƙungiyar, Hassan Nasrallah wanda ya rasa ransa a wani hari da Isara'ilan ta kai a ƙarshen watan Satumba. A…
Read More