Labarai

Gwamnan Osun ya zargi Ganduje da kitsa fitina a Kudu-maso-Yammacin Nijeriya

Daga BELLO A BABAJI Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana abin da Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ke yi a matsayin barazana ga demokraɗiyya, ya na mai kira ga Shugaba Tinubu da ya ɗauki mataki akansa. Cikin wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun kakakinsa, Olawale Rasheed, Adeleke ya bayyana hakan ne a lokacin da Ganduje ya ce zai ƙwace Osun a zaɓen 2026 bayan nasarar da APC ta samu a zaɓen gwamnan Ondo a kwanan nan. Gwamna Adeleke ya zargin Ganduje da haifar da tsaiko ga zaman lafiya da haɗin kan al'ummar Kudu-maso-Yamma da…
Read More

Chadi ta mayar wa Nijeriya sama da mutane 600 na wasu jihohi

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Chadi ta mayar wa Nijeriya mutane kimanin 600 da ke ayyukan bara a sassa daban-daban na ƙasar. Rahotonni sun bayyana cewa, dubunnan ƴan gudun hijira daga Jihar Borno ne suka watsu zuwa ƙasashen Chadi da Kamaru sakamakon yaƙin Boko Haram tun daga shekarar 2019. Darakta-Janar na Hukumar bada Agajin Gaggawa (SEMA), Muhammed Barkinɗo ya bayyana hakan wa manema labarai a Maiduguri, a lokacin da su ke tantance ƴan gudun hijira inda ya ce ƴan bulaguron, mutane ne daga Jihohin Borno, Kano, Sakkwato da Kaduna waɗanda suka shiga Chadi ba tare da cike ƙa'idodi ba. Barkinɗo…
Read More
Ɗangote ya fi kowa kyautata biyan haraji a Nijeriya – FIRS

Ɗangote ya fi kowa kyautata biyan haraji a Nijeriya – FIRS

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD An karrama rukunin Ɗangote da sauran rassansa da lambar yabo ta FMDƙ mai zinare a matsayin kamfanin da ya fi biyan haraji a Nijeriya. Kamfanin Ɗangote Industries Limited (DIL) da Bluestar Shipping, wani reshensa, an san su ne a matsayin waɗanda suka fi biyan haraji a ƙasar nan gabanin kamfanin sadarwa na MTN, yayin da babban kamfanin ƙera siminti na ƙasar, Dangote a wani lokaci ya samu lambobin yabo uku a na FMDQ. An gudanar da taron miƙa lambar yabon ne a Legas. A yayin bikin ranar musamman ta Hukumar Tara Haraji ta ƙasa, FIRS, a…
Read More
Neja na sa ran girbin tan miliyan ɗaya na masara – Gwamna Bago

Neja na sa ran girbin tan miliyan ɗaya na masara – Gwamna Bago

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamna Mohammed Umaru Bago na Jihar Neja ya kiyasta girbin sama da tan miliyan ɗaya na masara daga gonakin jihar a wannan kakar, inda ya yi alƙawarin yin fallasa masu tara kayan abinci a jihar domin daƙile tashin farashin kayayyaki. Gwamnan ya bayyana haka ne a ƙarshen makon da ya gabata a lokacin da yake ƙaddamar da noman masara a ɗaya daga cikin gonakin Neja, ta hanyar amfani da sabon fasahar girbi. Ya ce, “Yin amfani da fasahar girbin, zai rage asara tsakanin kashi 80 zuwa 90 cikin ɗari. Muna sa ran kusan tan miliyan ɗaya…
Read More

NURTW: Ƙungiyar Arewa Renaissance ta nemi Alƙalin Alƙalai ta hukunta MC Oluomo bisa ƙin biyayya ga hukuncin kotu

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar 'Arewa Renaissance Group' ta hannun shugaban ofishinta na bincike, Haliru Nadabo, ta bayyana zaɓen Musiliu Oluomo a kujerar sabon shugaban ƙungiyar ƴan yuniyon (NURTW), a matsayin karan tsaye ga shari'a. MC Oluomo, wanda yaron Shugaba Tinubu ne a siyaysance, an zaɓe shi ne duk da cewa Kotun Ɗaukaka ƙara ta amince da hukuncin 'Industrial Court of Nigeria' na cewa Frins Ibikunle shi ne halastaccen shugaban ƙungiyar. Saidai, ɓangaren masu biyayya ga MC Oluomo sun je sun yi haramtaccen zaɓe a Abuja a inda suka zaɓe shi a matsayin shugaba. Don haka ne ƙungiyar ke kira…
Read More
Iyalan ɗan siyasar Zamfara da aka kashe sun nemi a yi adalci

Iyalan ɗan siyasar Zamfara da aka kashe sun nemi a yi adalci

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Iyalan Marigayi Magaji Lawali wanda ake zargin kwamandan CPG na Zamfara ne ya kashe Kanar Rabi’u 'Yandoto sun yaba wa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Gwamna Dauda Lawal da kuma babban lauyan jihar kuma kwamishinan shari'a bisa jajircewar da suka yi wajen ganin an yi wa mahaifinsu adalci. Alhaji Nura Lawali Magaji Yandoto ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da Blueprint Manhaja jim kaɗan bayan kammala zaman kotun a Gusau ranar Laraba. “Mun tashi da Mummunan lamari a gidanmu a lokacin da aka kashe mana mahaifi, Magaji Lauwali Yandoto, Wanda ya bar ‘ya'ya…
Read More
Dalilinmu na bin diddigin kadarorin masu laifi lokacin bincike – EFCC

Dalilinmu na bin diddigin kadarorin masu laifi lokacin bincike – EFCC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban hukumar yaƙi da masu cin dunduniyar tattalin arziƙin Nijeriya, EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa ƙwace kadara a matsayin wani ginshiƙi na yaƙi da laifukan da suka shafi cin hanci da cin dunduniyar tattalin arziƙi kuma wata dabara ta daban. Olukoyede ya bayyana hakan ne a lokacin da kwamitin majalisar wakilai mai kula da laifukan cin hanci ta ziyarce shi a ranar Taka a Abuja. “Duk wanda ya fahimci cukumurɗan da ke aikin binciken laifukan da suka shafi kuɗi, zai a fahimci bincike Naira biliyan ɗaya ba ƙaramin yaƙi ba ne,” in ji…
Read More
Gwamnatin Zamfara ta gano likitocin bogi 20

Gwamnatin Zamfara ta gano likitocin bogi 20

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce ta gano likitoci ashirin a ɗaya daga cikin asibitin ta a matsayin likitoci kuma ma’aikatan bogi waɗanda ke karɓar albashin sama da Naira miliyan shida duk wata.  Shugaban ma'aikata na jiha kuma shugaban kwamitin gudanarwa na kwamitin tantancewa ma'aikata, Barista Ahmed Liman ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Gusau ranar Laraba.  A cewarsa, gwamnan jihar Dauda Lawal ne ya kafa kwamitin domin tantance ainihin ma’aikatan jihar don aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N70,000.  Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar Zamfara tana da ma’aikata sama da dubu…
Read More
Uwargidan Gwamnan Zamfara ta ƙaddamar da shirin biyan bashi ga mutane 1,000

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta ƙaddamar da shirin biyan bashi ga mutane 1,000

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau  Matar gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal, Hajiya Hurriyya ta ƙaddamar da shirin biyan basussuka ga mutane akalla dubu ɗaya a faɗin masarautun jihar 19. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mataimakiya a fannin yaɗa labarai, ta matar Gwamnan, Hajiya Zara’u Musa da aka raba wa manema labarai a Gusau ranar Laraba. Sanarwar ta ce, an gudanar da wannan sabon tsarin ne a hukumar tattarawa da rabon zakka da waƙafi dake Gusau Babban Birnin jihar. Uwargidan gwamnan ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne da nufin haɗa kan…
Read More
An yi walimar matan aure 10 da suka haddace Alƙur’ani a Argungu

An yi walimar matan aure 10 da suka haddace Alƙur’ani a Argungu

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi An gudanar da walimar bikin walimar matan aure goma da suka haddace Alƙur'ani maigirma a makarantar Kulliyatu Abubakar Majidadi Al-Islamiyya Gidan Tafida da ke garin Argungu. Malam Nasiru Abubakar Mera shi ne shugaban makarantar kuma ya zanta da wakilinmu jim kaɗan bayan kammala walimar ranar Lahadin da ta gabata inda ya bayyana jin daɗinsa da godiyar Allah da ya nuna musu wannan ranar da suka daɗe suna jira. Ya ce mata goma sha ɗaya ne suka haddace Alƙur'ani maigirma sai dai ɗayar mai suna Hauwa'u Ahmed Musa Gulma ta riga ta yi aure kuma…
Read More