Labarai

Farashin fetur na iya raguwa sakamakon yarjejeniyar Dangote da ’yan kasuwa

Farashin fetur na iya raguwa sakamakon yarjejeniyar Dangote da ’yan kasuwa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Nijeriya, IPMAN, ta yi ƙarin bayanin dagane da matsayar da suka cimma da matatar mai ta Dangote kan farashin da za su ringa siyen man fetur daga wajensa.  Kungiyar ta ce, kamfanin Dangoten ya amince da sayar musu da man fetur ɗin kan Naira 990, yayin da kuma masu deport, su kuma zai riƙa sayar musu da shi kan naira 940.  Kungiyar IPMAN ta ƙulla yarjejeniya da matatar man Dangote domin ɗauke man fetur kai tsaye. Shugaban ƙungiyar IPMAN na ƙasa, Abubakar Garima, ne ya sanar da hakan a wani taron…
Read More
An zargi hukumomin tsaron Nijeriya da gaza kare layukan lantarki

An zargi hukumomin tsaron Nijeriya da gaza kare layukan lantarki

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumomin tsaro a Nijeriya na cigaba da fuskantar suka kan gazawarsu wajen kare layukan lantarkin ƙasa daga ɓarayi, lamarin da ke janyo katsewar wutar lantarki da kuma taɓarɓarewar tattalin arziki. Duk da hukumomi da yawa da abin ya shafa, manyan layukan lanataki sun yi rauni saboda rashin isasshen kariya. Yawaitar hukumomin leƙen asiri da tsaro a ƙasar wani lamari ne mai matuƙar muhimmanci, amma duk da haka ba a samun abin da ya dace. Yayin da ake da hukumomi da yawa da abin ya shada, akwai ƙalubale wajen tantance wanda ke da alhakin kare layukan lantarki.…
Read More
An koka da rashin cibiyar kula da cutar kansa a Jihar Neja

An koka da rashin cibiyar kula da cutar kansa a Jihar Neja

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani matashi mai fafutuka a jihar Neja, Yahaya Mohammed-Usman, wanda aka fi sani da Sai Baba, ya yi kira ga gwamna Umaru Bago da ya gaggauta ɗaukar likitocin kula da cutar daji tare da kafa cibiyar kula da cutar daji a jihar domin daƙile ƙaruwar mace-macen masu kamuwa da cutar. A cikin wani faifan bidiyo da ya yi wa gwamnan a ranar Litinin,  Usman ya koka da yadda cutar ke ƙaruwa a faɗin jihar. Mai fafutukar ya ce, abin takaici ne yadda ba za a iya samun wani ƙwararren masani a ɓangaren cutar kansa guda ɗaya…
Read More
Sama da mutum 243,000 sun yi watsi da DStv da GOtv

Sama da mutum 243,000 sun yi watsi da DStv da GOtv

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kamfanin talbijin na Multichoice, mai kula da gidan talbijin na Pay-Tv na Afirka ta Kudu, ya bayyana cewa sashinta na Nijeriya, ya yi rasa kwastamomi masu biya kuɗi don si kallo sama da 243,000 a DSTV da GOtv a cikin watanni shida na Afrilu zuwa Satumba na wannan shekara. Kamfanin ya bayyana hakan ne a cikin Sakamako na Kuɗi na wucin gadi na watanni shida da suka ƙare a ranar 30 ga Satumba, 2024, wanda aka fitar ranar Talata. A cewar kamfanin, hauhawar farashin kayayyaki a Nujeriya sama da kashi 30 cikin 100 sakamakon tsadar kayan…
Read More
Dujiman Katsina ya yi ta’aziyar rasuwar Jakada Zakari Ibrahim

Dujiman Katsina ya yi ta’aziyar rasuwar Jakada Zakari Ibrahim

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Dujiman Katsina kuma shugaban kwamitin harkokin cikin gida na majalisar wakilai Hon Aliyu Abdullahi ya bayyana rasuwar Talban Katsina a matsayin babban rashi ba wai al'ummar jihar Katsina ba har da ƙasa baki ɗaya. A wata takardar sanarwar ɗauke da sa hannun mataimaki na musamman a kan yaɗa labarai Mr Francis Sardauna ya ce ɗan majalisar ya ɗimauta ƙwarai da samun labarin rasuwar Jakada Zakari Ibrahim. Ya bayyana marigayi Talban Katsina a matsayin ɗaya daga cikin manyan jami'in tsaro a ƙasan da ya ɗaukaka darajar jihar Katsina a idon duniya. Dujiman Katsina ya ƙara da…
Read More
Dikko Raɗɗa da Sarkin Katsina sun halarci jana’izar Talban Katsina, Jakada Zakari Ibrahim

Dikko Raɗɗa da Sarkin Katsina sun halarci jana’izar Talban Katsina, Jakada Zakari Ibrahim

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Raɗɗa da mai martaba sarkin Katsina Alhaji Abdulmummuni Kabir Usman na daga cikin waɗanda suka halarci jana'izar Talban Katsina. Sauran waɗanda suka halarci jana'izar sun haɗa da tsohon ministan sufuri sanata Hadi Sirika da shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Katsina Alhaji Jabiru Salisu Tsauri. An gudanar da jana'izar ne a fadan mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmummuni Kabir Usman. Da kammala jana'izar sai gwamnan da sarkin Katsina tare da sauran mutane su ka taka zuwa maƙabartan ɗan takun inda aka binnne marigayi Talban Katsina.
Read More

Ribaɗu ya jagoranci manyan jami’an gwamnati a ganawa da shugaban Chadi

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Idriss Débu Itno ya karɓi baƙoncin babbar tawaga daga Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Mai bai wa shugaban ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu. Lamarin ya auku ne a ranar Lahadi inda tawagar ta isar da saƙon Shugaba Bola Tinubu ga Shugaba Déby na jajenta masa game da harin da ƴan ta'adda suka kai a yankin Barkaram Island wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji da dama. Shugaba Tinubu ya kuma jaddada goyon bayansa ga shugaban ƙasar. Daga cikin mambobin tawagar akwai; Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa; Shugaban Sashin…
Read More

Harin sojojin sama ya hallaka fitattun ƴan bindiga, Ɗan-Isuhu da Dogo Sule a Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar sojin sama ta Nijeriya (NAF), ta ce ta yi luguden wuta wa ƴan bindiga inda ta kashe da da yawa daga cikinsu har da shahararru biyu, wato Ɗan-Isuhu da Dogo Sule. Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, Kwamado Olusola Akinboyewa ya bayyana hakan cikin wata takarda a ranar Lahadi inda ya ce hakan wani ƙoƙari ne na tawagar atisayen 'Fansar Yamma' wanda jami'an suka gudanar a ranar Juma'a, 15 ga watan Nuwamba. Lamarin ya auku ne a yankin ƙauyen Babban Ƙauye dake ƙaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara. Jami'in ya ce, wani bayani na sirri…
Read More

Tinubu ya tafi Brazil don halartar taron shugabannin ƙasashen G20

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tafi birnin Rio de Janeiro na ƙasar Brazil don halartar taron shugabannin ƙasashen G20 da za a yi karo na 19. An shirya gudanar da taron ne a ranakun 18 da 19 na watan Nuwamba inda za a tattauna muhimman batutuwa na ƙasa-da-ƙasa. A cikin sanarwar da Mai taimaka wa Shugaba Tinubu kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce Shugaban ƙasar Brazil Inácio Lula da Silva ne ya aiko da saƙon gayyata ga shugaban na Nijeriya zuwa taron. Taron zai haɗe shugabannin ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi daga Nahiyoyin…
Read More
Gwamna Lawal ya rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi a Zamfara

Gwamna Lawal ya rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi a Zamfara

Daga USMAN KAROFI Gwamna Dauda Lawal ya rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi guda 14 a jihar Zamfara tare da jan hankali kan muhimmancin adalci da daidaito wajen ayyukan ci gaba. A yayin bikin rantsarwar da aka gudanar a ɗakin taro na tsohon majalisar gwamnatin jihar, Gwamna Lawal ya yi kira ga sabbin shugabannin da su fifita jin daɗin al’umma tare da tabbatar da kowa ya ci gajiyar ayyukan ci gaba a yankunansu. Gwamnan ya yabawa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Zamfara (ZASIEC) saboda shirya zaɓe mai inganci da gaskiya wanda ya bai wa ’yan takarar jam’iyyar PDP…
Read More