17
Nov
Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Zaɓe, INEC, ta sanar da ɗan takarar jam'iyyar APC, Gwamna Lucky Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Ondo. Babban jami'in zaɓen jihar, Farfesa Olayemi Akinwunmi ya bayyana hakan a hedikwatar hukumar dake Alagbaka a Akure, babban birnin jihar. Farfesan ya ce, Aiyedatiwa ya samu ƙuri'u 366,781 wanda hakan ya ba shi damar doke takwaransa na jam'iyyar PDP, Agboola Ajayi wanda ya samu ƙuri'u 117,845, sai kuma Adeyemi Nejo na jam'iyyar ADP da ya zo na uku da ƙuri'u 4,138. Jaridar Alfijir ta ce 'Daily Trust' ta ruwaito cewa, ɗan takarar APC'n ya…
