Labarai

Raudhatur-Rasul za ta yi bikin cika shekaru 16 da kafuwa da karrama zakarun Gasar Ma’aiki

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ƙungiyar Raudhatur-Rasul za ta yi bikini cika shekara 16 da kafawa, da karrama zakarun gasar musabaƙar yabon Ma'aiki (SAW) gami da karrarama muhimman mutane. Za a gudanar da bikin ne a gidan Mumbayya, a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 10:00 na safe. Bilyaminu Zakariyya da aka fi sani da Abul-waraƙat Ayagi, shi ne shugaban ƙungiyar inda ya ce taron zai zama na musammam domin za a baje-kolin tarihi da ayyukan da ƙungiyar ta yi na shekaru 16, da kuma karɓar shawarwarin inganta ta. "Taro ne na godiya ga Allah, da a cikin huwacewarSa Ya sa…
Read More

Inganta lafiya ne babban burina a Ƙaramar Hukumar Gaya – Mahmud Tajo

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano An bai wa al’ummar ƙaramar hukumar Gaya ta Jihar Kano tabbacin inganta harkar lafiya a yankin yadda ya kamata saboda muhimmancinta ga rayukan al'umma. Zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar, Mahmud Tajo Gaya ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa ta musamman da Sashin Hulɗa da Jama'a na Ma'aikatar Lafiya, karkashin jarorancin Ibrahim Abdullahi, a lokacin da tawagar duba aikin rigakafin shan-inna da aka kammala kwanan nan ta ziyarci yankin, inda aka tattauna a ofishin Shirin Rigakafi na Ƙasa (NPI) reshen yankin. Tajo Gaya ya ce yana da sha'awa game da harkar lafiya kasancewar tun asali shi…
Read More

Hukumar zaɓe za ta fara tantance ƴan takarar ciyamomi da kansiloli a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hukumar zaɓe mai zaman kanta a jihar Katsina, ta ce za ta fara tantance ƴan takarar kujerun ciyamomi da kansiloli na ƙananan hukumomi a mako mai zuwa. A wata takarda da ke ɗauke da sa hannun Alhaji Adamu Salisu Ladan, kwamishinan zaɓe, ya ayyana 20 zuwa 27 na wannan wata a matsayin ranakun da hukumar za ta tantance ƴan takarar. Ya bayyana cewa za a tantance ƴan takarar kujerar ciyaman a ofishin hukumar yayin da na kansiloli kuma za a yi su a sakatariya ta kowacce ƙaramar hukuma da suka fito. Kwamishinan ya shawarci ƴan…
Read More

Majalisar Kula da Alƙalai ta dakatar da alƙalai biyu da sa musu ido

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Kula da Alƙalai ƙarƙashin jagorancin Allƙalin Alƙalan Nijeriya (CJN), Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun, ta hukunta wasu alƙalai biyar bisa laifin rashin kiyaye ƙa'idodin aiki. A yayin zamanta na ranar Alhamis, majalisar ta dakatar da Mai Shari'a G. C. Aguma na Babbar Kotun Tarayya dake Jihar Ribas kan gudanar da ayyukan shari'a na shekara ɗaya ba tare da biya ba sannan da sanya shi a sahun waɗanda za ake sa wa ido na tsawon shekaru biyu. Haka ma an dakatar da Mai Shari'a A. O. Nwabunike na Babbar Kotun Tarayya dake Jihar Anambara bisa irin laifin…
Read More

Lambar yabo ta Oscar: Shettima ya goyi bayan fim ɗin Mai Martaba

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya jaddada goyon bayan Gwamnatin Tarayya kan bikin girmama wa ta Oscar da za a sanya Dala miliyan 618 a shirin Digital da kasuwancin zamani (iDICE), yayin da Nijeriya ta zaɓi fim ɗin Mai Martaba ya lashe lambar yabon. Shettima ya ce musamman waɗanda suka shirya shi za su samu aikin iDICE da zai inganta harkokin Digital da masana'antu masu ƙirƙira. A lokacin da ya ke jawabi a wani zama da tawagar da suka haɗa fim ɗin ƙarƙashin jagorancin Ministar Al'adu, Barista Hannatu Musawa a Fadar shugaban ƙasa, Shettima ya bayyana…
Read More
A binne babban hafsan sojojin ƙasan Nijeriya, Janar Lagbaja a Abuja

A binne babban hafsan sojojin ƙasan Nijeriya, Janar Lagbaja a Abuja

Hawaye sun bayyana sosai a ranar Juma’a yayin da aka yi jana'izar marigayi Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja a Abuja, inda aka kawo ƙarshen Kyawawan ayyukansa na soja wanda ya shafe shekaru masu yawa a ciki. An yi jana'izar ne a maƙabartar Ƙasa dake babban birnin tarayya, inda aka kammala kwanaki biyu na jerin abubuwan girmamawa da aka fara a Legas a farkon mako. An binne shi daidai ƙarfe 4:41 na yamma bayan taron ya dauki tsawon sa’o’i biyu da rabi. Makarar gawar Lagbaja mai launin tutar Najeriya, kore da fari, ta iso maƙabarta da misalin ƙarfe…
Read More
Fashewar Gas ya yi sanadiyar jikkata mutane da dama da lalata dukiyoyi a Katsina

Fashewar Gas ya yi sanadiyar jikkata mutane da dama da lalata dukiyoyi a Katsina

Wata mota ɗauke da gas ta fashe a unguwar Magama, ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina a ranar Juma’a, inda mutane da dama suka samu raunuka, haka kuma aka samu lalacewar motoci da gidaje kamar yadda News Point Nigeria ta tabbatar. Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a wata tashar mai mai suna 'Walidan', inda ake zargin an ɓoye wasu kayayyakin da ake zaton an shigo da su cikin ƙasa daga Jamhuriyar Nijar. Wani mazaunin Magama, Aliyu Muhammad, ya ce, "Lamarin ya faru ne lokacin da aka ajiye wata mota ɗauke da gas a tashar mai tsawon kwanaki.…
Read More

Matawalle: Ƙungiyar manema labarai ta Arewa ta nemi a hana cin mutuncin ƴan jarida

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar manema labarai ta Arewa ta nuna damuwa kan yadda wata Babbar Kotun Tarayya dake ƙaramar hukumar Bichi a Jihar Kano ta ci mutuncin wasu ƴan jarida. Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya shigar da ƙara kan wasu shahararrun ƴan jarida biyu, Shua'ibu Mungadi na gidan rediyon Vision da Ahmed Tijjani Ramalan na gidan rediyon da telebijin na Freedom wanda hakan ya ci karo da sashi na 22 na kundin dokokin ƙasa da ya bai wa ƴan jarida damar bibiyar ayyukan masu muƙaman gwamnati da kuma sashi 39 da ya bada damar yin jawabi. A cikin…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya bayar da umarnin ɗaukar matashin da ke tallen ruwa aiki duk da kammala digiri da sakamako mafi daraja

Gwamna Raɗɗa ya bayar da umarnin ɗaukar matashin da ke tallen ruwa aiki duk da kammala digiri da sakamako mafi daraja

Daga UMAR GARBA a Katsina A cikin wani faifan bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta an ga wani ɗalibi, Sham'una na tallar ruwan leda 'Satchet Water' a babban birnin tarayya Abuja duk da cewa ɗalibin ya kammala karatunsa na jami'a da sakamako mafi daraja wato 'First Class'. a jami'ar Umaru Musa 'Yar'adua dake Katsina. Lamarin ya haifar da cece kuce musamman a shafukan sada zumunta game da matasa dake kammala karatu ba tare da samun aikin yi ba a ƙasar nan. To sai dai gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Raɗɗa, ya ce ya ga bidiyon ɗalibin don haka ne…
Read More

Tirela ɗauke da gas ta kama da wuta a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Wata motar tirela ɗauke da man gas ta kama da wuta a daidai gidan man Tamal dake yankin Magama a hanyar ƙaramar hukumar Jibiya a ranar Alhamis. Wannan al'amari ya jefa al'ummar garin Magama da Jibiya cikin fargaba da tashin hankali. Motoci 6 ne suka ƙone ƙurmus a inda kuma ba a rasa rai ko ɗaya ba. Jami'an tsaro na ƴan sanda da sojoji suka kai ɗauki na gaggawa har inda suka samu nasarar kashe wutar. Jami'in yaɗa labarai na rundunar ƴan sandan Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya bayyana…
Read More