Labarai

’Yan kwangila ne dalilin ɗauke wutar lantarki —EFCC

’Yan kwangila ne dalilin ɗauke wutar lantarki —EFCC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziƙi ta Nijeriya (EFCC) ta ɗora laifin yawan lalacewar babbar cibiyar wutar lantarki ta ƙasa a kan ’yan kwangila masu sayo kaya masara inganci. EFCC ta ce jabun na’urorin samar da lantarki da ake amfani da su ne babban musabbabin ɗauke wutar da ta munana a baya-bayan nan. Ta ƙara da cewa a shekaru 20 da suka wuce, manyan ayyukan da aika aikatawar a fannin samar da wutar a Najeriya bai fi kashi ɗaya bisa biyar na abin da aka tsara ba. Shugaban Hukumar, Ila Olukoyede, ne ya…
Read More
An gargaɗi Kiristoci dangane da rayuwar handama

An gargaɗi Kiristoci dangane da rayuwar handama

Daga JOHN D. WADA a Lafiya  Wani malamin addinin Kirista mai suna Rabaran Moses Sunday mai ritaya ne ya yi kiran a wa’azinsa a wajen sujadar Lahadi na Cocin ECWA 3 dake Tudun-gwandara a Lafiya babbar birnin jihar Nasarawa. Ya ce ba shakka kiran ya zama wajibi idan aka yi la’akari da yadda rayuwar handama ya zama ruwan dare a rayuwar al’umma yanzu ciki har da mabiya Kiristoci. Rabaran Moses Sunday ya bayyana cewa a yanzu da zarar mutum ya mutu sai a riƙa tunanin handame dukiyoyin sa ba tare da tausaya wa ‘ya’ya da matan da ya bari a…
Read More
Motar Ɗangote ta murƙushe mutane a kasuwar Legas

Motar Ɗangote ta murƙushe mutane a kasuwar Legas

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Mutane uku ne suka mutu a wani mummunan hatsari da ya rutsa da wata motar siminti ta Dangote. Hakazalika, haɗarin ya yi sanadinjikkatar wasu da dama a mahaɗar Ayetoro da ke kan hanyar Lekki zuwa Epe a Jihar Legas. Lamarin ya faru ne a ranar 11 ga Nuwamba, 2024. Rahotanni sun bayyana cewa motar tana saukowa ne daga gadar Ita-Opo a lokacin da motar ta kwace daga hannun direban, kuma ta yi karo da wata mota ƙirar Toyota Camry da ke fake a gefen titi a kasuwar. Masu ba da agajin gaggawa sun isa wurin don…
Read More
Tilasta zubar da ciki a Arewa maso Gabas: An tuhumi ƙungiyar Medecins Sans Frontieres

Tilasta zubar da ciki a Arewa maso Gabas: An tuhumi ƙungiyar Medecins Sans Frontieres

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kare Haƙƙin bil’adama ta ƙasa (NHRC) a ranar Larabar da ta gabata ta shawarci Gwamnatin jihar Borno da ta tantance ayyuka da shirye-shiryen ƙungiyar Medecins Sans Frontieres a jihar. An rawaito cewa hukumar ta bayar da wannan shawarar ne a cikin wani rahoto da ta gabatar wa jihar, wanda ya wanke sojojin Nijeriya daga hannu a rahoton tilasta mata 10,000 zubar ciki a yankin Arewa maso Gabas. A ranar 7 ga Disamba, 2022, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa wani rahoto da ke cewa tun daga shekarar 2013, sojojin Nijeriya sun gudanar da wani…
Read More
SERAP ta buƙaci Tinubu ya hana Wike da gwamnoni bai wa alƙalai motoci da gidaje

SERAP ta buƙaci Tinubu ya hana Wike da gwamnoni bai wa alƙalai motoci da gidaje

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiya mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Nijeriya, SERAP, ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya hana ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike da gwamnonin ƙasar 36, daga karɓe iko da aikin hukumar kula da harkokin shari'a ta Nijeriya, (NJC), da shugabannin kotuna ta hanyar bai wa alƙalai motoci da gidaje.  SERAP ta ce, waɗannan abubuwa ƙarara sun saɓa wa tanade-tanaden manufofi da ke ƙunshe a kundin tsarin mulki na rabon iko tsakanin ɓangarorin gwamnati da kuma tsarin bin doka, kuma hakan zai sa a riƙa kallon ɓangaren shari'a a matsayin kamar wanda…
Read More
Sarki Sanusi da Farfesa Ajayi sun yi tir da taɓarɓarewar ɓangaren shari’a

Sarki Sanusi da Farfesa Ajayi sun yi tir da taɓarɓarewar ɓangaren shari’a

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, da limamin cocin Emmanuel Chapel Methodist, Farfesa Konyinsola Ajayi, sun bayyana takaicin su kan taɓarɓarewar harkokin shari’a a Nijeriya, tare da bayyana hakan a matsayin abu na biyu mafi muni na cin hanci da rashawa a ƙasar. Sanusi ya koka da cewa duk da cewa aikin alƙalanci a Nijeriya na da sarƙaƙiya saboda taɓarɓarewar harkokin siyasa, amma a wasu lokutan alƙalan na yanke munanan hukunce-hukunce. A nasa ɓangaren Ajayi ya ce duk da cewa ya kamata ɓangaren shari'a ta zama tana tabbaci a Nijeriya, amma ita ce babbar hanya mara tabbas.…
Read More
Babu wata barazana da za ta hana ni rusau a Abuja – Wike

Babu wata barazana da za ta hana ni rusau a Abuja – Wike

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya ce gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba sakamakon zagon ƙasa daga wasu ƙungiyoyin farar hula da masu fafutuka a neman a dakatar da rusau a Abuja. Ministan ya bayyana hakan ne biyo bayan ziyarar da ya kai unguwar Ruga da aka ruguje tare da shugabannin hukumomin tsaro a babban birnin tarayya Abuja, bayan wani taron majalisar tsaro da aka yi a yammacin Lahadi. An rawaito cewa wasu daga cikin mutanen da aka rusa wuraren su tare da lauyan kare haƙƙin ɗan Adam, Deji Adeyanju, da kuma…
Read More
Ɗaliban Zamfara: Yadda matsayar Jami’ar Cyprus ta bambanta da Sudan da Indiya – Gwamna Dauda

Ɗaliban Zamfara: Yadda matsayar Jami’ar Cyprus ta bambanta da Sudan da Indiya – Gwamna Dauda

Daga AISHA ASAS A ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2023 ne Gwamna Dauda Lawal ya karɓi ragamar gwamnati daga hannun gwamnatin da ta gaza biyan hukumomin jarrabawar har tsawon shekaru uku, hakan kuwa ya kawo ci baya tare da dakushe ɗaliban babbar sakandare na faɗin jihar ta Zamfara daga rubuta jarrabawar ƙare sakandare, wato WASSCE DA NECO. A cikin wata sanarwa da ta fito daga hannun kakakin gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ta bayyana cewa, "daga cikin matsalolin da gwamnatinmu ta gada akwai batun rashin biyan kuɗin tallafin karatu ga ’yan asalin Jihar Zamfara da aka tura karatu…
Read More
Rashin fahimtar ƙudurin gyaran haraji ne ya firgita ‘yan Arewa – Jibrin Kofa

Rashin fahimtar ƙudurin gyaran haraji ne ya firgita ‘yan Arewa – Jibrin Kofa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Dan majalisar wakilai daga jihar Kano, Abdulmummin Jibrin, ya roƙi mutanen Arewa su mara wa ƙudurin dokar sake fasalin haraji baya da Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya kawo. Dan majalisar ya bayyana hakan ne a yayin da yake magana a ranar Lahadi a cikin shirin talabijin na Channels. Dan majalisar wanda ɗan jami’iyyar NNPP ne, ya ce ƙudurin na ƙunshe da abubuwa da dama da yankin Arewa za ta amfani da su. “ƙudurin ya ƙunshi wasu matakan ba wa jihohin Arewa kariya kowanne irin abun da ka iya cutar da su. “Waɗannan matakai…
Read More
Lakurawa na amfani da jirgi mara matuƙi, sun karɓe iko a ƙauyukan Kebbi —Bukarti

Lakurawa na amfani da jirgi mara matuƙi, sun karɓe iko a ƙauyukan Kebbi —Bukarti

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Lauya mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam, Abdu Bulama Bukarti, ya bayyana cewa Mayaƙan Lakurawa suna kafa manyan sansanoni a yankunan da suka kwace iko a Jihar Kebbi. Bulama Bukarti wanda ya ce mayakan kasar wajen sun ƙwace aikin sarakunan gargajiya ya bayyana cewa sun kai shekaru shida a Nijeriya kuma suna da haɗari domin aƙidarsu ɗaya da ta Boko Haram, da ISWAP. Ya ce, “Suna gina manyan sansanoni kuma da mukkan makamai kuma har da jirage marasa matuƙi da suke amfani da su wajen yin sintiri a kan ƙauyuka da sansanonin sojin gwamnati.…
Read More