16
Nov
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun cinnawa gonakin mutane da dama wuta inda suka ƙona dukkan amfanin gona, a ƙaramar Hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna a yankin Arewa maso yammacin Nijeriya. Hakan na zuwa ne bayan da aka yi wani zaman sulhu tsakanin 'yan bindigar da al’ummar yankin na Birnin Gwari da zummar kawo ƙarshen ɓarnar da suke yi. Maharan sun cinnawa gonakin masara da wake wuta ne a tsakar dare, inda suka ƙona gonaki da dama, abinda kuma ya haifar da hasara mai ɗimbin yawa. Wasu daga cikin manoman…
