Labarai

Matatar Kaduna za ta dawo aiki a Disamba – Darakta

Daga BELLO A. BABAJI Darakta-Manaja na Kamfanin tace Man fetur na Kaduna (KRPC), Dakta Mustapha Sugungun ya sanar da cewa za a kammala aikin gyaran matatar Kaduna zuwa ƙarshen 2024. A baya ne Kamfanin Man fetur na Ƙasa (NNPCL) ya bada kwangilar gyaran matatar ga kamfanin 'Daewoo Engineering and Construction' na ƙasar Koriya ta Kudu akan kuɗi Dala miliyan 741. Kammala aikin zai taimaka wajen samar da ganga 110,000 a kullum daga matatar wanda hakan zai ke wakilci kaso 60 zuwa na nan da watan Disamba, 2024. Mista Sugungun ya ce da zarar an kammala aikin, za a samu damar…
Read More

TUC ta soki jihohin Zamfara da Kuros Ribas bisa koma-bayansu a mafi ƙarancin albashi

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar Kasuwanci, TUC ta yi kira ga jihohin da ba su fara biyan albashi da sabon tsarin mafi ƙarancinsa ba da su gaggauta aiwatarwa ko ma'aikatansu su shiga yajin aiki. Shugaban ƙungiyar, Festus Osifo ya bayyana hakan jim-kaɗan bayan wani zama da Majalisar Zartarwarta ta gudanar a Abuja, a ranar Talata. Ya nuna damuwa kan jinkirin aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi ga da dama daga cikin jihohin Nijeriya wanda hakan ke cigaba da haifar da tsaiko ga harkokin ma'aikata na yau-da-kullum. Osifo ya bayyana cewa yayin da wasu jihohi suka cimma kaso 80 na zartarwar,…
Read More

Majalisar Wakilai na fafutukar a yi amfani da harshen gida a makarantu

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Wakilai ta yi kira ga Ma'aikatar Ilimi da ta samar da shiri da zai bada damar a sanya koyar da yarukan gida a cikin jaddawalin karantarwa a makarantun Nijeriya don amfani da su a matsayin karɓaɓɓu. Haka na zuwa ne bayan da ɗan Majalisa Kalejaiye Adeboye Paul (APC Legas) ya ɗauki nauyin batun a zauren majalisar, ya na mai nuna muhimmancin hakan a makarantun firamare da ƙaramar sekandire. Ya ce Nijeriya ƙasa ce mai arziƙin yaruka daban-daban gami da al'adu masu ƙarfi don akwai buƙatar a faɗaɗa karɓaɓɓun yaruka bayan Turanci. Ya kuma ce turanci…
Read More
Gwamna Uba Sani ya amshi tubabbun ‘yan bindiga

Gwamna Uba Sani ya amshi tubabbun ‘yan bindiga

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi kira ga waɗanda ke shirin haddasa tashin hankali da su zabi hanyar tattaunawa, yana mai jaddada ƙudurin gwamnatinsa na tabbatar da zaman lafiya, adalci da daidaito ga kowa da kowa. Gwamnan ya yi wannan kiran ne a Birnin Gwari ranar Alhamis, yayin da ya karɓi tubabbun ‘yan bindiga da kuma buɗe kasuwar dabbobi da aka rufe tsawon shekara goma saboda matsalar tsaro. Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna, tare da haɗin gwiwar wasu hukumomin tarayya, sun kafa kwamitin tattaunawa da zaman lafiya wanda ke aiki tare da masu ruwa da tsaki. Ya…
Read More

Okonjo-Iweala ta sake zama darakta-janar ta hukumar kasuwanci ta duniya

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO), ta sake naɗa Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin Darakta-Janar a karo na biyu. WTO ta wallafa hakan ne a shafinta na X, a ranar Juma'a inda Majalisar Zartarwarta ta ce naɗin zai fara ne daga ranar 1 ga watan Satumba, 2025. Majalisar ta ce ta amince da naɗa ƴar Nijeriyar ne na wani zangon shekara huɗu sakamakon ƙwarewarta ta fuskar jagoranci da hangenta game da samar da gobe mai kyau ga WTO. Hakan na zuwa ne kasancewar ba a samu wani da ya nemi a ba shi muƙamin ba bayan Okonjo-Iweala wadda…
Read More

Gwamnatin Katsina ta tallafa wa mutane 10,000 da ambaliya ta shafa

Mataimakin gwamnan Katsina, Farouk Lawal Joɓe Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kayayyakin sun haɗa da buhunan hatsi guda 7,000 da aka raba wa ƴan gudun hijira da marasa galihu da ambaliyar ruwan sama ya shafa. Mataimakin gwamnan Jihar Katsina, Malam Farouk Lawal Joɓe ya sanar da haka a lokacin da ya ke bayyana wa manema labarai nasarorin da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta samu tun lokacin hawan hawansa mulki. Ya ce wannan ƙari ne akan kuɗi Naira miliyan 451 da aka raba wa wasu ƙarin mutane dubu ɗaya. Bugu da ƙari kuma malam Joɓe ya ce an raba wasu kayan agaji…
Read More
Gwamnatin Tarayya na shirin tilasta wa  ma’aikatu da hukumomi amsar masu yi wa ƙasa hidima

Gwamnatin Tarayya na shirin tilasta wa ma’aikatu da hukumomi amsar masu yi wa ƙasa hidima

Gwamnatin Tarayya na shirin tilastawa ma'iakatu da hukumomin gwamnati da cewa wajibi ne su amshi masu hidimar ƙasa da aka turo ma'aikatun su. Ministan ci gaban matasa na ƙasa, Ayodele Olawande ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja. Ministan ya yi wannan martani a dalilin yawan ƙorafe-ƙorafe da suke samu yadda ma'aikatun gwamnati ke ƙin amsar masu yi wa ƙasa hidima, ya na mai tabbatar da cewa za su rubuta takarda su aika wa shugaban ƙasa. Idan ba a mance ba, a cikin watan Nuwamba gwamnati ta dakatar da dokar da ke hana masu yi wa ƙasa…
Read More

Har yanzu ana cigaba da azabtar da mutane a Gaza – Ofishin Jakadancin Palestine

Daga BELLO A. BABAJI Kimanin kwanaki 419 kenan da mayaƙan haɗin-gwiwa na ƙasashen Amurka da Isra'ila, wato USA-Israeli suke kisan kiyashi tare da ɗaiɗaita dubunnan al'umma a Gaza, kamar yadda ofishin Jakadancin Palestine a Nijeriya ya bayyana. A cikin wata takarda da Jakadan Palestine a Nijeriya, Abu Shawesh Abdullah ya fitar, ya ce zuwa ranar 27 ga Nuwamba, mutane 44,249 ne aka yi wa kisan gilla yayin da aka raunata 104,746 a Gaza waɗanda mafi yawancin su yara ne da mata, sannan kuma da dama suna tsaka-mai-wuya a buraguzan gine-ginen da aka tarwatsa. A tare da wasu laifukan yaƙi da…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta ƙi amincewa da buƙatar EFCC ta sake gurfanar da Yahaya Bello

Daga BELLO A. BABAJI Yayin da ba a ga lauyoyinsa ba, Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, ta ƙi amincewa da buƙatar hukumar EFCC ta sake gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello. An shirya sauron ƙarar ne da aka shigar a gaban Alƙali Emeka Nwite kan tuhumce-tuhumce guda 19 da aciki akwai zarginsa da badaƙalar Naira biliyan 80.2. A lokacin da aka kira sauraron hukunci game da ƙarar tsohon gwamnan, babu ɗaya daga cikin lauyoyinsa da suke wajen inda daga nan ne wakilin ɓangaren EFCC, Mista Kemi Pinheiro ya nemi kotun ta bar hukumar ta gurfanar da Bello.…
Read More
Za a tsame talakawa daga biyan haraji a sabon ƙudirin dokar ta 2024 – Fadar Shugaban ƙasa

Za a tsame talakawa daga biyan haraji a sabon ƙudirin dokar ta 2024 – Fadar Shugaban ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban kwamitin kuɗin da gyaran haraji na Fadar Shugaban ƙasa, Taiwo Oyedele, ya yi ƙarin haske kan daftarin dokar gyaran haraji wanda Shugaba Tinubu ya gabatar wa majalisa, inda ya ce an tsara daftarin ne ta yadda za a rage wa ma’aikata kaso 90 na harajin da suke biya. Ya kuma ce daftarin dokar an yi shi ne domin sake daba fasalin harajin ɓAT domin daidaita abin da kowacce jiha ya kamata ta samu ta la’akari da abin da ake samarwa a jihar. Mista Oyedele ya yi wannan ƙarin haske ne a ranar Laraba…
Read More