Labarai

Sufeto Janar ya hana jami’an Amotekun da bijilante shiga zaɓen Ondo

Sufeto Janar ya hana jami’an Amotekun da bijilante shiga zaɓen Ondo

Babban Sufeton ‘Yan Sanda na ƙasa, Kayode Egbetokun, ya ba da umarnin haramta wa Ƙungiyar tsaron Yammacin Nijeriya wato Amotekun da kuma bijilante shiga zaɓen gwamna da za a gudanar a ranar 16 ga watan Nuwamba a jihar Ondo. Kwamishinan hulɗa da jama’a na rundunar, Muyiwa Adejobi, ya fitar da wannan sanarwa a ranar Lahadi tare da tabbatar wa da al’umma tsaron zaɓen. Babban Sufeton ya ce an shirya tura jami’ai daga sassa na musamman na ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro a lokacin zaɓen. An kuma tsara yin sintiri ta sama da jiragen helikwafta na ‘yan sanda tare da…
Read More
Ku daina ɓata sunan sashen shari’a – Alƙalin Alƙalan Nijeriya ga kotuna

Ku daina ɓata sunan sashen shari’a – Alƙalin Alƙalan Nijeriya ga kotuna

Daga USMAN KAROFI Babbar Alƙalin Alƙalai ta Nijeriya (CJN), Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta bayyana cewa wasu alƙalai na ɓata sunan ma’aikatar shari’a a ƙasar. Yanke hukunce- hukunce masu jawo cece-kuce daga kotuna masu matsayi ɗaya ya tayar da ƙura a lokuta daban-daban, musamman a Kano da Ribas, inda ake fama da rikici tsakanin manyan ‘yan siyasa. Da take jawabi a wajen wani taron tattaunawa ,Kekere-Ekun ta ce duk da wannan ƙalubale, ma’aikatar shari’a a Nijeriya na da alƙalan da ke da ƙwazo da gaskiya. Ta jaddada cewa Nijeriya na da alƙalai ƙwararru kuma masu aiki tuƙuru, tana jan hankalin…
Read More
Lakurawa: Muƙaddashin hafsan sojojin ƙasan Nijeriya ya isa Sokoto

Lakurawa: Muƙaddashin hafsan sojojin ƙasan Nijeriya ya isa Sokoto

Muƙaddashin babban hafsan sojojin ƙasa na Nijeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya isa jihar Sakkwato domin ziyarar aiki ta farko zuwa yankin da rundunar sojin Nijeriya ta takwas ke da alhakin kula da shi. Rahotanni daga News Point Nijeriya sun nuna cewa a wannan ziyara, Oluyede zai gana da Sarkin Musulmi, Sultan na Sakkwato, tare da wasu masu ruwa da tsaki a cikin yankin da rundunar ta takwas ke aiki. Ziyarar ta kuma bai wa Oluyede damar jawabi ga dakarun rundunar Operation Fasan Yamma da ke yaƙi da ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma. Ziyarar muƙaddashin babban hafsan sojin…
Read More

Noman rani: Gwamnatin Katsina za ta faɗaɗa madatsan ruwa na Ɗanja

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina za ta faɗaɗa madatsan ruwa na ƙaramar hukumar Ɗanja domin faɗadɗa noman rani a yankin. Gwamna Dikko Umar Raɗɗa ya faɗi hakan a garin Ɗanja, lokacin da ya ke ƙaddamar da tallafin Naira miliyan 20 da ɗan Majalisar Dokoki na jihar mai wakiltar Ɗanja, Hon. shamsuddeen Abubakar ya raba. Ya ce gwamnatinsa ta na sane da yanayi mai kyau na ƙasar noma da ke yankin. "wannan shiri kashi ne na biyu zai haɓaka noman rani a yankin, kuma zai bunƙasa tattalin arziƙin ba ma manoma ba kaɗai, har da sauran al'ummar yankin",…
Read More

Har yanzu ƙofar tuba a buɗe ta ke – Sojoji ga ƴan bindigar Katsina

Daga BELLO A. BABAJI Kwamandan Birget na 17 na sojojin Nijeriya a Jihar Katsina, Burgediya Janar Babatunde Omopariola ya sanar da cewa har yanzu ƙofar tuba a buɗe ta ke ga ƴan bindiga da masu haddasa tashin-tashina. Ya shawarci duk waɗanda ke cikin harkar garkuwa da mutane da su ƙaurace wa hakan ko kuma su fuskanci doka. Burgediya Omopariola ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke miƙa wasu mutane tara da aka ceto daga hannun ƴan bindiga ga jami'an gwamnatin Katsina a Birget ɗin. Omopariola, wanda shugaban dakarun Birget ɗin, Kanal Yakubu Nwandiscas ya wakilce shi, ya ce…
Read More

A karo na farko Guardiola ya sha kaye sau huɗu a jere a matsayinsa na koci

Daga BELLO A. BABAJI Pep Guardiola ya sha kaye har sau huɗu a jere a tarihin kasancewar sa koci bayan da ƙungiyar Brighton da doke Manchester City da ci 2 da 1 a ranar Asabar. Ɗan wasan gaba na Manchester City, Erling Haaaland shi ya fara zura ƙwallo a ragar Brighton inda daga baya Jao Pedro ya farke. Ƙasa da mintina 15 kan a tashi ne ɗan wasan Brighton, Matt O'Riley ya zura ƙwallo ta biyu a ɓangaren da Guardiolan ke jagoranta. Guardiola dai ya jagoranci ƙungiyoyin Barcelona da Bayern Munich a baya inda wannan shi ne karo na farko…
Read More
Tinubu ya tafi Saudiyya domin halartar taron haɗin gwiwa na Musulunci da Larabawa

Tinubu ya tafi Saudiyya domin halartar taron haɗin gwiwa na Musulunci da Larabawa

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Nijeriya a ranar Lahadi domin halartar taron ƙoli na haɗin gwiwar ƙasashen Larabawa da Musulunci a Saudiyya. Taron zai gudana ne a Riyadh ranar Litinin, inda zai mayar da hankali kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya. Tinubu zai halarci taron ne bisa gayyatar Sarki Salman da Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Asabar, inda ya ce, “Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga Abuja a ranar Lahadi zuwa Riyadh, Saudiyya, domin halartar taron ƙoli na…
Read More
Tinubu zai lashe zaɓen 2027  – APC

Tinubu zai lashe zaɓen 2027 – APC

Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta gargaɗi jam’iyyun adawa a ƙasar da kada su yi farin ciki da wuce gona da iri game da kayen Kamala Harris, mataimakiyar shugaban ƙasa a Amurka a zaɓen shugaban ƙasa, inda ta ce Shugaba Bola Tinubu zai sake lashe zaɓen a shekarar 2027. An sanar da tsohon shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump a matsayin wanda ya lashe zaɓen a ranar Laraba, inda ya kayar da Harris cikin wata babbar nasara da ta jawo ce-ce-ku-ce a duniya baki ɗaya. Trump mai shekaru 78 ya zama shugaban ƙasa na 47 kuma tsofaffin wanda ya taba…
Read More

Bankin Keystone ya yaba wa gwamnan Zamfara kan inganta ɗan adam a jihar

Daga BELLO A. BABAJI Bankin Keystone ya yaba wa Gwamna Dauda Lawal kan ƙoƙarinsa na inganta rayukan al'umma a Zamfara. Darakta-Manaja na bankin, Hassan Imam ya jagoranci manyan jami'ansu yayin wata ziyara ga gwamnan a Gidan Gwamnatin jihar dake Gusau. Cikin wata takarda da Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce bankin ya na aikin gyaran makarantun Firamare na Sarkin Kudu da Sakandire na Sambo dake Gusau a matsayin sauƙe nauyin da ke kansu ga al'umma. A lokacin da ya ke jawabi, Gwamna Lawal ya yaba wa bankin a ƙoƙarinsa na mayar da Zamfara waje da zai dace…
Read More

Netanyahu ya naɗa sabon Jakada ga Amurka kwanakin kaɗan bayan Trump ya lashe zaɓe

Daga BELLO A. BABAJI Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya naɗa Yechiel Leiter a matsayin Jakadan ƙasar ga Amurka. Leiter, wanda haifaffen Amurka ne, ya kasance shi ne shugaban ma'aikatan Ma'aikatar kuɗi. Ya kuma riƙe muƙaman mataimakin Darakta-Janar na Ma'aikatar Ilimi da kuma shugaban riƙon ƙwarya na Kamfanin Tashoshin Jiragen ruwa na Isra'ila. Hallau, an kashe masa ɗansa a shekarar da ta gabata a yaƙin Gaza da dakarun Hamas, a matsayinsa na sojan Isra'ila. Netanyahu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, ya ce Leiter masani ne a harkar difulomasiyya, ƙwararren kakaki kuma wanda ya san siyaysa da al'adun…
Read More