Labarai

Nijeriya za ta jaddada goyon bayanta kan ƴancin Falasɗinu a taron ƙasashen Musulmi

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron haɗin-gwiwa na ƙasashen Larabawa da Musulunci da za a gudanar a Birnin Riyadh dake Saudiyya don tattauna batutuwan da suka shafi Gabas ta Tsakiya. Shugaba Tinubu zai jadada goyon bayan Nijeriya ne kan ƴancin Falasɗinawa a taron wanda ya samu gayyatarsa daga Yarima, Mohammed Bin Salman daga Saudiyya. Daga cikin ƴan tawagar shugaban ƙasa akwai manyan jami'an gwamnati da suka haɗa da; Ministan Harkokin wajen ƙasar, Ambasada Yusuf Tuggar; Mai ba shugaban ƙasa shawara kan Harkokin Tsaro, Mallam Nuhu Ribaɗu; Ministan yaɗa Labarai da Wayar da kan al'umma, Alhaji…
Read More
Uwargidan Shugaban Ƙasa ta musanta shirin gudanar da addu’a ga ƙasa

Uwargidan Shugaban Ƙasa ta musanta shirin gudanar da addu’a ga ƙasa

Daga USMAN KAROFI Uwargidan Shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu da kuma mai ba Shugaban ƙasa shawara kan tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu a wata sanarwa an ce suna da hannu a wani shirin addu’o’i na kwana bakwai domin neman taimakon Allah a kan halin da ake ciki a ƙasar. Rahoton da aka danganta wa daraktan babban tarayyar addu’a ta Ƙasa, Segun Afolorunikan, ya nuna cewa matar Shugaban ƙasa da Ribadu suna daga cikin waɗanda suka shirya shirin da aka sa wa suna “neman Allah ya shiga al’amuran Nijeriya .” A cewar rahoton, Afolorunikan ya bayyana cewa wannan shiri za a gudanar…
Read More

Canada ta soke biza mai wa’adin shekara 10 ga ƴan Nijeriya da ƴan wasu ƙasashe

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin ƙasar Canada ta sanar da soke katin biza mai wa'adin shekara goma ga ƴaƴan Nijeriya da na wasu ƙasashe. Hukumomin ƙasar sun ce hakan ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin wajen rage adadin shige-da-fice tun bayan aukuwar annobar COVID-19. Bizar, wadda ta ke bada damar shiga da fita ƙasar a lokacin da mutum ya ke so, an soke amfani da ita ne a matsayin karɓaɓɓiyar shaida. Da farko dai, ƙasar ta bada damar amfani da biza iri biyu; wadda ke bada damar shiga ƙasar a kodayaushe da kuma wacce ke sa a shiga bisa wani dalili…
Read More

Babban Hafsan Tsaro ya jinjina wa sojoji kan wanke jami’ansu bisa zargin zubar da ciki a Arewa-maso-Gabas

Daga BELLO A. BABAJI Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa ya yaba wa sakamakon da Tawagar Bincike ta Musamman ga Tauye Haƙƙin Ɗan-adam a ƙoƙarin shafe Ayyukan Ta'addanci a Arewa-maso-Gabas ta fitar, wanda ya wanke jami'an sojoji daga zargin zubar da ciki da adadinsu ya kai 10,000 a yankin. Tawagar, wadda ta ɗauki tsawon shekaru biyu ta na bincike game da lamarin, ta miƙa rahotonta ga Hukumar ƙare ƴancin Ɗan-adam (NHRC) a hedikwatarta da ke Abuja, a ranar Juma'a. Rahoton ya ce, tabbas abin da ake tuhumar sojojin na bin wasu hanyoyi don zubar da ciki da duka da…
Read More

Za mu yi garanbawul ga wasu kwamishinoni – Gwamna Abba

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya ce nan ba da jimawa ba zai cire wasu daga cikin mambobin Majalisar Zartarwa da aka tantance ƙwazonsu a ƙarƙashin ayyukansu . Gwamnan, wanda ya tabbatar da karɓar rahoton kwamitin duba aikin mambobin majalisar, ya bayyana cewa al'umma za su ji matakin da gwamnatinsa za ta ɗauka nan ba da jimawa ba. Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya faɗi hakan a cikin wata sanarwa da ya aika wa kadaura24. Gwamnan ya tunatar da al’umma game da shirin sauya wasu daga cikin mambobin majalisar a wata hira kai-tsaye…
Read More

‘Yan bindiga sun kashe mutane 15 a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Aƙalla mutane 15 ne suka rasu a wani ba-takashi tsakanin waɗansu mutane da ake sa ran Lukurawa ne da ke alaƙa da ISWAP da suka fito daga yankin ƙasashen waje kuma su ke da'awar musulunci, da kuma al'ummar garin Mera da ke ƙaramar hukumar Mulki ta Augie. Lamarin ya auku ne a Juma'a da rana bayan da maharan suka kora ilahirin dabbobin mutanen ƙauyen. Wakilinmu ya ruwaito cewa, bayan maharan sun ƙwace dabbobin daga mai kiwon ne shi kuma ya shiga gari ya faɗa wa mutanen garin inda su kuma daga nan sai suka fito…
Read More

Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da wani sahun jami’an community watch corps a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta ƙaddamar da ɗauka da horas da kashi na biyu na jami'an community watch corps domin faɗaɗa ayyukan tsaro a faɗin jihar. A ranar Alhamis da ta gabata ne ƴan ta'adda suka kashe jami'ansu biyar yayin da kuma suka samu raunuka a ƙaramar hukumar Jibiya. Da ya ke jawabi a wajen bikin yaye jami'an, Gwamna Dikko Raɗɗa, ya ce jami'an za su taimaka wa sauran jami'an tsaro wajen yaƙi da ta'adanci a faɗin jihar. Ya ce jami'ai 1,466 gwamnatin jihar ta ɗauka aiki shekarar da ta gabata waɗanda su na cigaba da…
Read More
Gwamna Zulum ya cancanci yabo kan ayyukan cigaban Jihar Borno – NURTW

Gwamna Zulum ya cancanci yabo kan ayyukan cigaban Jihar Borno – NURTW

Daga GAMBO ISAH Shugaban ƙungiyar NURTW reshen ƙaramar Hukumar Bama a Jihar Borno, Alhaji Ba Mai Mustapha, a cikin wata sanarwar manema labarai da ya raba wa jaridun Blueprint a Abuja, ya yaba da ɗimbin nasarorin da Maigirma Gwamnan Jihar Borno ya samu da kuma salon shugabanci a fannin gina hanyoyi, tsarin kiwon lafiya, samar da kayan aiki ga jami'an tsaron soji, 'yan sanda da JTF a dukkan ƙananan hukumomi 27 da ke faɗin jihar, da dai sauransu. Ba Mai ya yaba wa Gwamna Farfesa Baba Gana Zulum bisa jajircewarsa wajen ƙarfafa wa ’yan jihar da kuma mambobin ƙungiyarsa da…
Read More
Sabon Shugaban ƙaramar hukumar Doma ya yaba da zaɓukan bana

Sabon Shugaban ƙaramar hukumar Doma ya yaba da zaɓukan bana

Daga JOHN  D. WADA a Lafiya Bayan da aka kammala zaɓukan duka ƙananan hukumomin jihar Nasarawa, sabon shugaban ƙaramar hukumar Doma a jihar wanda aka zaɓa a inuwar jam'iyyar APC mai ci a jihar  Honorabul Jonathan Addra ya yi alƙawarin yin duka mai yuwa wajen kawo cigaba masu ma'ana a duka matakai a ƙaramar hukumar ta Doma bakiɗaya. Honorabul Jonathan Addra ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu jim kaɗan bayan an rantsar da shi da sauran sabbin shugabannin duka ƙananan hukumomin jihar 13 wanda aka gudanar a gidan gwamnatin jihar dake Lafiya babban birnin jihar…
Read More
Zanga-zanga: Yadda aka bar mu cikin yunwa, inji yaran da aka saki

Zanga-zanga: Yadda aka bar mu cikin yunwa, inji yaran da aka saki

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Bayan da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ba da umarnin sakin su a ranar Litinin, wasu yara ƙanana, masu shekaru tsakanin 14 zuwa 17, da aka kama a lokacin zanga-zangar matsin rayuwa a faɗin ƙasar a watan Agusta, sun bayyana abubuwan da suka fuskanta a yayin da suke tsare. A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai babban sufetan ‘yan sandan ya gurfanar da mutane 76 da suka haɗa da yara ƙanana 32 waɗanda aka kama yayin zanga-zangar, bisa laifuka 10 da suka shafi cin amanar ƙasa, da nufin tada zaune tsaye a Nijeriya da kuma…
Read More