Labarai

Yadda Kaduna ta zarce kowace jiha yawan kuɗaɗen shiga a Arewa – NBS

Yadda Kaduna ta zarce kowace jiha yawan kuɗaɗen shiga a Arewa – NBS

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Jihar Kaduna ta ɗauki matsayi na ɗaya a matsayin jihar da ta fi kowacce jiha yawan kuɗaɗen shiga a yankin arewa, inda ta samu zunzurutun kuɗi har Naira Biliyan 62.48 a shekarar 2023. Wannan dai wani gagarumin ƙaruwa ne daga shekarar da ta gabata inda ta samu Naira biliyan 58. Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ce ta fitar da rahoton kwanan nan, inda ya bayyana yadda wasu jihohi ke ƙoƙari wajen samar da kuɗaɗen shiga duk da ƙalubalen tattalin arziki. A nasa jawabin shugaban hukumar tara kuɗaɗen shiga na jihar Kaduna Jerry Adams, ya ce manufofin…
Read More
Matar aure ta tilasta budurwa ta kwanta da mijinta don ta haifa masa ’ya’ya

Matar aure ta tilasta budurwa ta kwanta da mijinta don ta haifa masa ’ya’ya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata jami'iyar 'yan sanda mai bincike (IPO) Sufeto Elizabeth Osikolu, a ranar Litinin, ta shaida wa wata Kotun Laifukan Cin Zarafin Jinsi a Ikeja, yadda wata matar aure, Omolara Alashe, ta tilasta wa wata yarinya ’yar shekara 19 ta kwana da mijinta don ta haifa masa ’ya’ya. Omolara da mijinta, Ramoni Lateef, suna fuskantar tuhume-tuhume guda uku da suka haɗa da haɗa baki, fyaɗe da kuma lalata da ƙaramar yarinya. Sai dai waɗanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin. A yayin da wani shaida yake magana da babban lauyan jihar, Babajide Boye, a gaban kotu, ya…
Read More
Gwamnatin Nijeriya ta cire manyan jami’o’i daga tsarin biyan IPPIS

Gwamnatin Nijeriya ta cire manyan jami’o’i daga tsarin biyan IPPIS

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF) ya tabbatar da cire manyan jami'o'in tarayya (FTI) daga tsarin biyan albashi na IPPIS, wanda ke nuna gagarumin sauyi kan yadda za a tafiyar da biyan albashin waɗannan jami'o'i. Bawa Mokwa, Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na OAGF ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da jaridar The Nation cewa, an dakatar da tsarin IPPIS na FTI biyo bayan umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar. A cewar Mokwa, albashin watan Nuwamba na waɗannan jami'o'i za a riƙa sarrafa su ta hanyar GIFMIS. An umurci cibiyoyi…
Read More
Kwastom a Apapa ta karɓi harajin tiriliyan N1.8 cikin wata 10

Kwastom a Apapa ta karɓi harajin tiriliyan N1.8 cikin wata 10

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Kwastom ta Nijeriya reshen tashar ruwa ta Apapa a Legas ta ce ta tara Naira Tiriliyan 1.8 a matsayin kuɗaɗen shiga tsakanin Janairu zuwa Oktoba 2024. Shugaban Hukumar Kwastom mai kula da yankin Apapa, Babatunde Olomu ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin. Olomu ya ce tara kuɗaɗen shiga na zuwa ne duk da gagarumin koma baya da aka samu a kasuwar. Ya ƙara da cewa, adadin ya nuna ƙaruwar kashi 101 cikin 100 idan aka kwatanta da biliyan N931 da aka tara a daidai wannan lokacin…
Read More
Shugaba Tinubu na iya ƙoƙarinsa wajen yaye wa ‘yan Nijeriya damuwarsu – Idris

Shugaba Tinubu na iya ƙoƙarinsa wajen yaye wa ‘yan Nijeriya damuwarsu – Idris

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan sadarwa da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya ce shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu na cigaba da ƙoƙarin kawo ƙarshen wahalar da ‘yan Nijeriya ke fama da shi. Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a Kaduna a yayin wani shiri na gidan rediyon tarayya na (FRCN) mai suna ‘Hannu Da Yawa’ da ake yi cikin harshen Hausa. Kamfanin dillancin labarai na ƙasa, NAN, ya rawaito ministan na cewa cire tallafin man fetur abu ne da ya zama wajibi saboda wasu ‘yan ƙalilan ne ke cin moriyarsa. Ya ba da tabbacin…
Read More
Malaman addini na yaudarar mabiyansu saboda abin duniya — Sarkin Musulmi 

Malaman addini na yaudarar mabiyansu saboda abin duniya — Sarkin Musulmi 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya zargi malaman addini yaudarar mabiyansu domin samun abin duniya. Sarkin Musulmi, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA), ya gargaɗe su a kan hakan sannan ya umarce su da su tuba, su riƙa gudunar da wa’azi ta hanyar ingantacciyar koyarwar Musulunci don gina al’umma ta gari. Ya bayyana haka ne a wajen taron yankin kan rikicin da ke haifar da sauyin yanayi a Arewacin Nijeriya, wanda aka gudanar ranar Litinin a Kaduna. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito…
Read More
Mulkin shekara takwas Tinubu zai yi — Doyin Okupe

Mulkin shekara takwas Tinubu zai yi — Doyin Okupe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Darakta-Janar na Kwamitin Yain Neman Zaɓen Obi/Datti, Mista Doyin Okupe ya ce an ƙulla alƙawari cewa yankin Arewa zai mulki Nijeriya tsawon shekara takwas sannan yankin Kudu ya karɓa na tsawon shekara takwas. Doyin Okupe ya bayyana cewa tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari daga yankin Arewa ya yi shekara takwas a bisa mulki, don haka Tinubu da ke kan mulki zai yi shekara takwas idan yana so. Okupe wanda tsohon kakakin tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ne, ya ce Tinubu na iya cin zaɓen Shugaban ƙasa a 2027 idan ya iya shawo kan…
Read More
Gwamnatin Abba za ta gina tsangayoyin almajirai 44 a Kano – Gwani Falaki

Gwamnatin Abba za ta gina tsangayoyin almajirai 44 a Kano – Gwani Falaki

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano An bayyana cewa a ƙoƙarinsa da yake yi wajen cika alƙawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe ta fuskar bunƙasa ilimi da taimakon addini ga ɗaukacin al'ummar Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi alƙawarin cewa zai bunƙasa ilimi da kuma inganta rayuwar al'umma ta kowace fuska, yanzu haka wannan ya yi nisa wajen cika alƙawari kamar yadda ko wanne mutumin kirki ya yi alƙawari ya ga ya cika ba yaudara ba, to ba shaka kowa shaida ne a Kano Gwamna Abba, na cika alƙawarin Kanawa, har ma wanda bai alƙawarin yi ba…
Read More
Da ni ke mulki a Nijeriya da ba ta shiga tasku ba — Atiku

Da ni ke mulki a Nijeriya da ba ta shiga tasku ba — Atiku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce manufofin da Shugaba Tinubu ke bijiro da su, ba su da kan gado.  Ya ce Gwamnatin Tarayya na bijiro da manufofin tattalin arziƙi waɗanda ba su da ma’ana kuma na ƙara jefa ’yan Nijeriya cikin wahala. “Yin sauye-sauye don daidaita farashin canjin kuɗi, kuɗin wutar lantarki, da farashin man fetur lokaci guda, wannan matakai sun yi tsauri a lokaci guda,” in ji shi. Atiku, ya bayyana cewa da shi ne shugaban ƙasa, zai bi abubuwa a hankali don rage raɗaɗin da sauye-sauye za su haifar. Atiku…
Read More
An yi wa ’yar shekara biyu fyaɗe har lahira a Bauchi

An yi wa ’yar shekara biyu fyaɗe har lahira a Bauchi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar ’yan sanda  ta bayyana cewa an yi wa wata yarinya ’yar shekara biyu fyaɗe har lahira a ƙaramar Hukumar Ningi ta Jihar Bauchi. Kakakin ’yan sanda a jihar Bauchi, Ahmed Mohammed Wakil, a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata, 5 ga Nuwamba, 2024. Ya ce an kai rahoton aikata laifin ne a hedikwatar ’yan sanda da ke Ningi bayan “an gano gawar wata ’yar shekara biyu a gefen wani masallaci da ke kan titin Deneɓa, a ƙaramar Hukumar Ningi, da alamun fyaɗe.…
Read More