Labarai

Mu ƙara ƙoƙari wajen gyaran maƙabartu don kyautata goben mu – Sarkin Amowu Odofin

Mu ƙara ƙoƙari wajen gyaran maƙabartu don kyautata goben mu – Sarkin Amowu Odofin

Daga DAUDA USMAN a Legas An shawarci al'ummar Musulmin Arewa mazauna jihohin Kudu da yammacin Nijeriya da su ƙara ƙoƙari a wajen gyaran maƙabartunsu, gidajensu  na gaskiya a ranar gobe kiyama. Mai martaba Sarkin al'ummar Hausawan ƙaramar Hukumar Amuwo Odofin dake cikin garin Legas Alhaji Adamu Aliyu ɗan asalin jihar Jigawa da mai martaba Sarkin Hausawan Festac Alhaji Mustapha Musa ɗan asalin jihar Katsina sune suka nemi hakan a lokacin da sarakunan guda biyu suka jagoranci waɗansu daga cikin sarakunan ƙabilun Musulman arewacin Nijeriya da matasa mazauna jihar Legas a wajen aikin gaiyya na noman maƙabarta tare da gyaranta gaba…
Read More
Za mu gudanar da ayyuka da za su kawo cigaba da bunƙasa Jam’iyyar PDP a Kano – Kabiru Ɗandago

Za mu gudanar da ayyuka da za su kawo cigaba da bunƙasa Jam’iyyar PDP a Kano – Kabiru Ɗandago

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Sabon Mataimakin Shugaban Jam'iyyar PDP na shiyyar Kano ta Tsakiya, Alhaji Kabiru Bello Ɗandago ya ce zai gabatar da ayyukan da za su zama na samun cigaba ga jam'iyyar a jihar Kano. Ya  bayyana hakan ne a yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a shiryar Kano ta Tsakiya  ya ce zaɓen fitar da shugabannin jam'iyyar da aka gudanar sun san ya yi wa wasu daɗi wasu kuma akasin haka, amma su a matsayinsu na sabbin shugabanni aikinsu na farko shine su yi rarrashi da bayar da haƙuri da saka cigaban jam'iyyar a gaba.…
Read More
Yadda sojoji suka yi wa ‘yan bindigar da suka lalata babban layin lantarkin Arewa luguden wuta 

Yadda sojoji suka yi wa ‘yan bindigar da suka lalata babban layin lantarkin Arewa luguden wuta 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani hoton tauraron ɗan’Adam ya nuna yadda aka yi rugu-rugu da wani yanki da ke zagaye da tashar wutar lantarki da ke Shiroro inda a kwanakin baya aka samu matsalar lalacewar baban layin wutar rarraba lantarki a wurin mai ƙarfin 330Kɓ ta Shiroro-Mando. A ranar Litinin ne Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta harba bamabamai ga ‘yan ta’addan da suka hana gyaran wutar lantarkin layin wuta na Shiroro-Kaduna da ake zargin ‘yan bindiga da lalatawa. Lalacewar wannan layin wutar lantarki dai ya jefa al’ummar yankin Arewa cikin matsanancin duhu duk da cewa an dawo da…
Read More
Sabon Ministan Ilimi ya soke ƙudurin cika shekaru 18 kafin shiga manyan makarantu a Nijeriya

Sabon Ministan Ilimi ya soke ƙudurin cika shekaru 18 kafin shiga manyan makarantu a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sabon Ministan Ilimi, Olatunji Alausa, ya soke dokar da ta buƙaci sai ɗalibi ya kai shekaru 18 kafin shiga jami’a wanda tsohon Ministan Ilimi, Tahir Mamman, ya kawo. Minista Alausa ne ya bayyana wannan mataki a yayin da jawabi bayan shiga ofishinsa a matsayin sabon Ministan Ilimi a ranar Talata. Shugaban ƙasa Bola Tinubu ne ya naɗa shi bayan cire tsohon ministan ilimi Tahir Mamman sakamakon sake fasalin ministocinsa. Sannan Shugaba Tinubu ya sauya wa ƙaramin ministan ilimi, Yusuf Sununu, ma’aikata zuwa ma’aikatar hukumar jinƙai da yaƙi da talauci. A makon da ya gabata…
Read More
Ba za a dawo da tallafin man fetur ba — Minista

Ba za a dawo da tallafin man fetur ba — Minista

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Kuɗi, Wale Edun, ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta soke sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ya kawo a ɓangaren canjin Dala da kuma ɓangaren man fetur ba. Edun, ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi sabuwar ƙaramar Ministar Kuɗi, Doris Uzoka Anite, a hedikwatar ma’aikatar a ranar Litinin. Ya ce, “Yanzu Nijeriya tana da farashin dala wanda yake tafiya daidai a kasuwa, da kuma kasuwar mai wacce aka sauya mata fasali. “Waɗannan sauye-sauye ne da ya kamata a yi shekaru da dama da suka gabata, amma Shugaba Tinubu ne ya fara…
Read More
Hafsoshin sojin ƙasan Nijeriya da suka mutu a bakin aiki

Hafsoshin sojin ƙasan Nijeriya da suka mutu a bakin aiki

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Har yanzu ana cigaba da alhinin rasuwar Babban Hafsan Sojin ƙasan Nijeriya, Taoreed Abiodun Lagbaja, wanda tuni shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayar da umarni a rage ɗagawar da ake wa tutocin Nijeriya a ƙasar. Janar Lagbaja ne dai mutum na uku da ya rasu a lokacin da yake riƙe da muƙamin babban hafsan sojin ƙasa na Nijeriya. Lagbaja ne babban hafsan sojin ƙasan Nijeriya 23, kuma ya riƙe muƙamin ne tsakanin Yunin 2023 zuwa Nuwamban 2024, inda ya rasu yana da shekara 56 a duniya bayan fama da jinya. Baya ga Janar Lagbaja ga wasu…
Read More
AA Rano, Matrix da AYM Shafa sun maka Ɗangote a kotu

AA Rano, Matrix da AYM Shafa sun maka Ɗangote a kotu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wasu ’yan kasuwar man fetur uku, AYM Shafa, A. AA Rano, da Matrix sun buƙaci babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta yi watsi da ƙarar da matatar man dangote ta shigar. A cikin takardar shaidar haɗin gwiwa mai alamar: FHC/ABJ/CS/1324/2024, da kwanan wata Nuwamba 5, manyan ’yan kasuwa uku a Nijeriya sun buƙaci kotu da dakatar da Dangote daga mamaye ɓangaren mai a ƙasar. Kamfanonin sun ɗauki matakin ne bayan Dangote ya yi ƙorafi a kwace lasisinsu na shigo da mai daga ƙetare. Hakan ya biyo bayan zargin da Dangote ke yi musu kan…
Read More

Babban koma-baya ga PDP: Tsohon ɗan majalisa a Zamfara, Kabiru Classic ya koma APC

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Kabiru Yahaya Classic ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Classic ya bayyana sauya shekar tasa ne a ranar Alhamis, bayan ganawa da shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Tukur Ɗanfulani da Tsohon shugaban APC na jihar, Alhaji Lawal M. Liman da sauran masu-ruwa-da-tsaki na jami'iyyar. Yahaya Classic ya wakilci mazaɓar Anka/Talata Mafara tsakanin 2019 zuwa 2023 a karkashin PDP a mataki na Majalisar Wakilai. Tsohon ɗan majalisar ya ce, ya fice daga PDP ne saboda babu adalci a jam’iyyar reshen jihar shi ya sa ya yanke shawarar ficewa daga…
Read More
’Yan ta’adda sun sace mutum 50 sun ƙaƙaba harajin miliyan N150 a ƙauyukan Zamfara

’Yan ta’adda sun sace mutum 50 sun ƙaƙaba harajin miliyan N150 a ƙauyukan Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan ta’adda sun yi garkuwa da mutane sama da 50 a ƙauyukan Jihar Zamfara, a yayin da mutanen suke aikin gona. ’Yan ta’addan sun kuma sanya wa mazauna ƙauyukan jihar harajin Naira miliyan 50 a kan ƙauye guda, da wa’adin mako biyu kacal. Kazalika sun sanya tatar sama da Naira miliyan 100 a kan wasu ƙauyuka da ke ƙaramar Hukumar Tsafe, inda kowanne aka ayyana abin da mazaunansa za su biya, tskannain miliyan bakwai zuwa miliyan 20. Hakan na zuwa ne bayan ’yan bindiga sun kashe manoma 10, suka sare kawunan shida daga cikinsu…
Read More
Zaɓe: Al’umma sun buƙaci Gwamnan Zamfara, PDP, ZASIEC da su canza masu ɗan takara

Zaɓe: Al’umma sun buƙaci Gwamnan Zamfara, PDP, ZASIEC da su canza masu ɗan takara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau  Kungiyar masu kishin ƙasa ta ƙaramar Hukumar Bunguɗu a jihar Zamfara sun yi kira ga Gwamna Dauda Lawal da Jam'iyyar PDP reshen jihar da kuma Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta jihar ZASIEC da su gaggauta sauya ɗan takararsu na Shugaban ƙaramar Hukumar ta Bunguɗu, Nura Umar Abdullahi a zaɓen ƙananan hukumomi dake tafe nan da kwana tara masu zuwa.  Shugaban ƙungiyar, Kwamared Sulaiman Kwatarkwashi ya yi wannan roƙo a wata hira da manema labarai a Gusau ranar Alhamis. A cewarsa, tuni aka rubuta takardar koke ga ofishin shugaban jam’iyyar na jihar da kuma hukumar…
Read More